A cikin β€˜yan kwanakin nan, TON ya fara nuna alamun dawowa kasuwa bayan faduwar da ya yi daga kusan $8 zuwa $1.2.


Yanzu haka, farashin TON ya fara tashi kuma ya kai kusan $2 β€” abin da ya jawo hankalin traders da investors musamman a Najeriya da Afrika.



Menene Ya Faru?



Rahotanni daga masana crypto ciki har da Engr Adam Muhammad Muhtar sun nuna cewa:


  • Telegram sun fara daukar TON da muhimmanci sosai
  • An rage kudin transaction (fees) har sau 6
  • Telegram sun zama manyan validators a network
  • An kara staking na TON da yawa



Wannan duk yana nuna cewa akwai babban shiri na farfado da TON.



Tasirin Farashi (Price Impact πŸ“Š)



A cikin kwanaki kadan:


  • TON ya tashi da kusan 50%
  • Daga ~$1.2 β†’ ~$2
  • Sabbin tokens kamar MTONGA sun tashi daga $100K β†’ $4.2M market cap



Wannan yana nuna cewa market na fara samun confidence a TON ecosystem.



Dalilin Tashin TON




1. Rage Fees



Saukin amfani da network yana jawo users da developers.



2. Telegram Involvement



Telegram yanzu suna taka rawar gani a matsayin validator β€” wannan yana kara trust.



3. Community Hype (MTONGA)



Kalmar β€œMake TON Great Again” ta fara jawo hankali sosai.



4. Movement na Ecosystem Coins



Projects kamar:


  • Notcoin
  • Dogs
  • Fish



duk sun fara motsi kadan β€” alamar liquidity na dawowa.



TON vs Solana β€” Sabuwar Gasa?



A halin yanzu, TON na kallon Solana a matsayin babban competitor.


Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Domin TON ya yi nasara:


  • Dole ya jawo degens (high-risk traders)
  • Dole ya samar da tokens masu anfani
  • Dole ya bawa investors riba



πŸ‘‰ Wannan shine hanyar da Solana ta bi kafin ta yi nasara.



Shawara Ga Masu Zuba Jari ⚠️



Masana suna cewa:


  • Kada ka shiga market bayan pump ya kare
  • Jira retracement (retest) idan zai faru
  • Ka guji zama β€œexit liquidity”



πŸ‘‰ Wannan yana da matukar muhimmanci musamman ga beginners.



Tasiri Ga Najeriya da Afrika 🌍



Yawancin matasa a Najeriya suna cikin TON ecosystem (Notcoin, Telegram bots, da sauransu).


Idan TON ya tashi:


  • Za a samu karin masu anfani
  • Za a samu sabbin earning opportunities
  • Afrika na iya zama babban user base




Ra’ayi / Analysis



Gaskiya ita ce:


TON yana da babban advantage β€” Telegram.


Idan Telegram suka yi amfani da:


  • User base nasu
  • Tech improvements
  • Marketing



πŸ‘‰ TON na iya zama daya daga cikin top blockchains a duniya.


Amma har yanzu akwai risk, saboda:


  • Competition da Solana
  • Market volatility
  • Overhype




Mu Tattauna



Kai fa:


Shin TON zai iya komawa sama sosai kamar da? Ko wannan temporary pump ne kawai?



Karshe



A yanzu, duk idanu suna kan TON.


Idan Telegram da Pavel Durov suka cika alkawari, akwai yiwuwar TON ya zama babban competitor a crypto space.


Ku ci gaba da bibiyar Fuchaweb3 domin samun sabbin crypto updates, signals da airdrops cikin harshen Hausa.