Kasuwar crypto ta sake shiga wani sabon lale!

Abunda ake yi masa kallon yayi da zai yi tashe ya wuce, ko kuma wani dandalin canki-canki, salon kasuwanci mai hatsari da bai kai a mayarda hankali a kansa ba. 

Yau mun wayi gari crypto ya zama kadara.

Manyan kamfanoni cinikayya na duniya, hada-hadar kuɗi da ɗai-ɗaikun investors suna sanya kuɗaɗen su domin kwadayin irin romon da suke hange.

Da kai nake mai karanta wannan rubutun, shin har yanzu kana jiran sai ance maka ka fara ribatar kasuwancin crypto?


ABU MAI MUHIMMANCI 

Abun burgewa da kuɗaɗen crypto shine tsarin ƴanci, takaita inflation.

Yayin da suke samun karɓuwa kuma supply dinsu baya karuwa.

Hakan na haifar da demand, demand kuma yana ƙara musu daraja.

Shigowar manyan hukumomi ya sake ƙarawa abun citta.

Yancin mallakar dukiyar ka, kyawawan dokoki domin kariya, irin kuɗin da yake tururuwa da kuma sauƙin mallaka ba tare da ciwon kai ba ya sake baiwa investors ƙwarin gwiwar amincewa kuɗaɗen crypto.


CRYPTO YA SHIGA JERIN MANYAN KADARORIN DUNIYA 

Idan ka duba da kyau zaka ga cewa yanzu crypto yana tasirantuwa da:

Global liquidity

Interest rates

U.S. dollar strength

Institutional flows

Market leverage

Investor sentiment

Yanzu price action bai kai dalilin yanke makomar crypto ba.


MANYAN ABUBUWAN DUBAWA 

Jin waɗannan jawaban bazai sa kai kuma ka saki jiki ba. 

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Hallau dai kasuwar crypto tana buƙatar taka tsantsan saboda hatsarin volatility. 

Musamman kai trader. Dole ne ka sanya idanu hakan waɗannan:

Open Interest: Zai taimaka maka ka fahimci yawan leverage da yake shiga kasuwa.

Funding Rates: Yawan positions da aka buɗe. Long ko Short shima yana taimakawa wajen fahimtar alkiblar kasuwa. 

Liquidity: Cewar sauye sauyen shirin hukumomi yana shafar kasuwar kai tsaye.

Price Structure: Abunda ya shafi support, resistance ko trend yana da matukar muhimmanci.


CRYPTO A BABBAN MADUBI 

Tairsin crypto a yanzu ya wuce ka tsaya sauraron ko tambayar matakin farashi.

Alaji yanzu ana maganar matakin crypto ne a kasuwar kuɗaɗe ta duniya.

Kasuwancin crypto a yanzu yana sake samun karɓuwa a gurin jama'a. Kuma bisa ga alkaluma farin jinin sa zai cigaba da yaɗuwa.

Abun ya wuce jiran tsammanin sabon coin na yayi. Da sannu crypto na samun matsuguni a cikin global financial market. 

Koma dai menene shirin ka, to kayi nazari fiye da kallon taswirar candle sticks.

Ku faɗa mana irin hangen da kuke yiwa kasuwar crypto nan gaba.