Daga $50k FDV zuwa $1M cikin ƙasa da 24 Hours!
Idan baka ji labarin $SUNUSI ba acikin kwanakin nan, to tabbas baka shiga shafin X (Twitter) ko Facebook ba! Ko ta ina ka duba, maganar sabon meme token din nan ake yi mai taken "The African Bull" 🐂. Ƙura ta tashi, kuma matasan crypto a fadin nahiyar nan sun fara rishin dadi.
Amma tambayar dake bakin kowa ita ce: Shin wannan tafiyar tafi-da-gidanka ce ta gaskiya, ko kuwa dukan ruwa ne a bakin ƙofar gari? ku biyo mu domin jin ƙwa-ƙwaf!
Me Yasa $SUNUSI Ke Ta Trend Kamar Wutar Daji?
A harkar meme coins, muddin labari ya bada ma'ana, to babu abun mamaki idan anga ambaliyar ruwan kudade cikin ƙiftawa. $SUNUSI ya sosa zuciyar kowa:
Alamar Jajircewa (The African Bull): Ba kamar sauran memes da ko team dinsu ba'a sani ba, Sunusi sanannrn haziqin matashi ne kuma mai kamanta gaskiya (al'ummar crypto tayi masa wannan shaida). $SUNUSI ya zo da tambarin positive na kasuwa (Bull) tareda karkafar Afirka — wadda ke nuna juriya da neman na kai. Wannan ya sa matasanmu suka ji jikinsu ya karba.
Son Barka (FOMO is Real): Kamfen din da ake yi a Facebook da X ba na wasa ba ne. Masu fada a ji (KOLs) da manyan shafukan crypto suna ta tura labarin, wanda hakan ke sa kowa tsoron kada a bar shi a baya.
Matakin da Team ɗin Ya Ɗauka Ya Jawo Hankali
Daya daga cikin abubuwan da suka sa mutane suka ci gaba da magana kan wannan aikin shi ne sanarwar da team ɗin ya fitar.
Sun bayyana cewa sun karɓi kusan $4,000 a matsayin Creator Rewards, kuma sun ce za su karkatar da wannan kuɗi gaba ɗaya zuwa ayyukan talla da bunƙasa al'ummar aikin (marketing).
Ko da yake wannan ba tabbaci ba ne na nasara, irin wannan mataki na iya nuna cewa masu haɓaka project din suna ƙoƙarin mayar da kuɗin da suka samu wajen faɗaɗa shirin maimakon riƙe shi domin amfanin kansu.
An Kuma Yi Maganar Airdrop
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Ba a daɗe ba kuma aka sanar da cewa ana shirin gudanar da airdrop ga masu riƙe da token ɗin ($SUNUSI holders).
A tarihi, irin wannan tsari kan kasance wata hanya ta ƙarfafa mutane su ci gaba da riƙe token, tare da gina al'umma mai ƙarfi. Duk da haka, yana da kyau masu saka jari su jira cikakkun ƙa'idoji da sharuddan airdrop kafin su yanke hukunci.
Idan Wannan Project Ya Yi Nasara, Wane Alheri Zai Iya Kawowa?
Idan har $SUNUSI ya samu gagarumar nasara a nan gaba, akwai wasu fa'idodi da za su iya bayyana.
Na farko, zai iya nuna cewa Afirka na da ikon gina meme projects da za su iya jan hankalin duniya, ba wai jiran ayyuka daga wasu nahiyoyi kawai ba.
Na biyu, hakan na iya ƙarfafa matasa masu shirye-shirye, masu zanen hoto, masu talla da masu gina al'ummomi a nahiyar su fara ƙirƙirar nasu ayyukan blockchain.
Na uku, idan aka gina al'umma mai ƙarfi, hakan na iya jawo sababbin masu amfani da crypto daga sassa daban-daban na Afirka, wanda zai taimaka wajen faɗaɗa ilimin blockchain da tattalin arzikin dijital.
Sannan idan project ɗin ya ci gaba da haɓaka cikin gaskiya da tsari, zai iya zama wata hanya ta nuna cewa ba lallai sai manyan kamfanoni ko manyan masu saka jari ba ne kawai ke iya haifar da babban tasiri a kasuwar crypto.
Daga Ƙarshe
Duk da irin wannan ci gaba mai ban sha'awa, yana da muhimmanci a tuna cewa meme tokens suna cikin kadarorin da suka fi haɗarin saka jari.
Farashin da ya iya hawa da sauri, haka ma yana iya sauka cikin gaggawa.
Saboda haka, kafin kowa ya saya ko ya riƙe kowanne token, ya kamata ya yi cikakken bincikensa (DYOR – Do Your Own Research), ya fahimci haɗarin da ke tattare da shi, kuma kada ya saka kuɗin da ba zai iya jure rasa su ba.