Mu leƙa kasuwar crypto.
Matsin lamba, rashin tabbaci, fargaba da kuma abinda ya shafi tsaro.
Motsin farashin Bitcoin, matsalolin dokokin Amurka, fitar kuɗi daga Bitcoin ETFs, matsalar tsaro a Liquid Network da tasirin tattalin arzikin duniya ga kasuwar crypto.
Dama wasu kanun.
Ku biyo mu a cikin wannan rahoton.
Wannan satin kasuwar crypto cike take da chakwakiya tun da kan ƙalubale da rashin tabbas akan dokokin Amurka, damuwar hauhawar farashi (inflation) da kuma tashin farashin ɗanyen mai.
Hallau dai zirga-zirgar kuɗaɗen manyan kamfanoni ya sake tada zaune tsaye ga ra'ayin ƴan kasuwar.
Wannan satin ya nuna mana manyan darussa guda biyu:
Yadda shigar manyan kamfanonin hada-hada ke tasiri akan ƴan kasuwa da kuma yadda matsalar tsaro kan taka rawar gani wajen rusa ƙwarin gwiwar ƴan kasuwa duba da yadda har manyan kamfanonin Blockchain ma basu tsira ba.
Bitcoin.
Wannan makon bai zowa bitcoin da sauƙi ba.
Kasuwar bitcoin ta faɗi har zuwa ƙasa da $80k. Hakan ya sanya investors sake tuntun-tuni akan yanayin kasuwar.
Wasu na ganin faduwar bai tsaya ga taswirar farashi kaɗai ba.
Tuni ƴan kasuwar suka alaƙanta wannan yanayin da treasury yields, hauhawar farashi da kuma abinda zai iya biyo bayan tsare-tsaren dokokin Amurka.
Dalilin da yasa muka cika kallon motsin bitcoin kafin komai: shi bitcoin jagora ne kuma sarki ne.
Abinda yake faruwa a kasuwar bitcoin kai tsaye yana shafar sauran coins ta fuskoki da dama.
Faduwar farashin bitcoin ba yana nufin din-din-din ɗin faduwar kasuwa bane. Domin sanin alkiblar kasuwa akwai buƙatar ku sanya idanun ku anan da kyau:
price structure, trading volume, open interest, funding rates da kuma yanayin zirga-zirgar kuɗaɗe a lalitar ETFs.
Waɗannan sune zasu haska maku kasuwa a babban allo fiye da hawa da saukar farashi.
U.S cCarity Act
Tsarin zartar da gudanarwar kuɗaɗen crypto (Clarity Act) ya samu cikas daga zauren senate a cikin wannan satin.
Hakan kamar mayarda hannun agogo baya ne.
Yanzu dole sai majalisar ta sake nazari kan yadda zata ɓullowa batun domin dokar ta samu sahalewa.
Babu jayayya kan irin yadda kasuwar zata tasirantu da tsarin dokokin na clarity act. Irin wannan cikas ba ƙaramin koma baya zai kawo a kasuwar ba.
Kasuwar crypto tana buƙatar tsarin dokokin na Clarity Act domin sauƙin gudanarwa tare da aminci.
Rashin samuwar hakan zai jefa kasuwar cikin halin tsoro da rashin tabbas ƙwarai da gaske.
ETFs.
An samu gagarumin zirarewar kuɗaɗe daga lalitar bitcoin ETFs.
Bincike ya tabbatar da kimanin $462.7 million investors suka cire daga kasuwar a tsakanin kwanaki biyu.
Janye kuɗaɗe da investors keyi kai tsaye yana tilasta wa masu kula da hannun jarin sayar da bitcoin domin daidaita tsarin investment din a bisa doka.
Hakan kuma na ƙara zama barazana tare da raunana kasuwar ta crypto.
Har yanzu dai yana da kyau ƴan kasuwar su iya bambance tsakanin:
Short-term outflows.
Persistent outflows.
Da renewed outflows.
Matsalolin Tsaro.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Tsautsayi da ya afkawa Liquid Network.
Liquid network salon fasaha ce data ginu akan tsarin bitcoin (bitcoin sidecahin).
Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu nasarar dawo da kimanin 3,400 btc da aka kwamushe cikin 4k bitcoin.
Wannan yanayi ya tilasta tsayar da gudanarwar network ɗin a lokacin da incidence din ya faru.
Sai dai faruwar lamarin ya jefa ƴan kasuwar cikin tan-tama kan yadda zasu cigaba da rarraba kuɗaɗen su a kasuwar.
Hakan ya tilasta wa investors yin dogon nazari da bincike mai zurfi don kaucewa hatsari.
Macroeconomics
A matsayin ka na ɗan kiripto ya kamata kasan cewa kasuwancin nan yana dogaro ne da wasu manyan alkaluman tattalin arziki.
Tashin farashin ɗanyen mai, treasury bills, inflation ko interest rate suna taka muhimmiyar rawar gani wajen fayyace goben kasuwar ta crypto.
Kasuwar Altcoins
Abubuwan da suka faru cikin wannan satin sun sake daidaita tsayuwar farashin sauran alts.
Da yawa daga cikin alts sun samu faduwar darajar kudi.
Koda yake wasu alts basu ji jiki kamar sauran ba. Saurin faduwar darajar alts ɗin yana da alaƙa kai tsaye da ƙarancin marketcap dinsu.
Muhimman abubuwan dubawa sune:
Project-specific developments.
Token supply and distribution.
Network usage and adoption.
Liquidity across exchanges.
Leverage in derivatives markets.
Muhimman Darussa.
Cikin wannan satin mun fahimci yadda kasuwar crypto ta dogara kai tsaye bisa wasu alkaluma daga wajen kasuwar.
Daga ciki:
Tasirin tsare-tsaren gwamnatoci.
Ruwa da tsakin manyan kamfanoni.
Muhimmancin tsaro.
Mako mai kamawa.
Tilas mu sanya idanuwanmu akan:
Bitcoin support and resistance levels.
ETFs flows.
Regulatory developments.
Macroeconomics data.
Security updates.
Derivatives market.
Menene yafi daukar hankalin ku cikin wannan satin? ku faɗa mana ra'ayoyin ku.