Kimanin asarar $500M cikin sa'o'i ya haifar da zaman ɗar-ɗar ga ƴan kasuwar.

Cikin kankanin lokaci rahotannin tattalin arzikin duniya sun sauya salo zuwa ba zata. 

Ƙarin yawaitar basussuka duka a lokaci guda.

Farashin bitcoin ya faɗi zuwa $83,000.

A daidai lokacin da farashin ɗanyen mai ya haura zuwa $100.

Hau-hawar kuɗin lamuni (treasury bills) tareda jiran rahoton FED na yau. 


ME DUKA WANNAN KE NUFI?

Idan baku manta ba, a rahoton mu na jiya mun tattauna akan alaƙar crypto da tsarin tattalin arzikin duniya.

Batutuwa uku da suka haifar da matsin lamba ga kasuwar a crypto a lokaci guda:

Tashin Farashin Danyen Mai: Danyen mai na Brent ya haura dala 101 a kowace ganga sakamakon rikice-rikicen siyasa na duniya.

Kasuwar ɗanyen mai na sake rura wutar fargabar hauhawar farashi, wanda ke barazanar lalata tsare-tsaren manyan bankunan ƙasashe.

Tashin Ribar Takardun Lamuni: Ribar takardar lamuni ta Treasury mai tsawon shekaru 10 ta haura kashi 5.3%. Sa'ad da takardun lamuni masu ƙarancin risk ke bayar da fiye da kashi 5%.

Wannan dalilin yana sanya investors cire kuɗaɗen su daga kasuwa irin crypto zuwa cash ko bonds.

Farfadowar Dalar Amurka: Babban ma'aunin dake nuna ƙarfin Dalar Amurka (DXY) ya sake komawa matakin sama da 102. 

Ƙarfin dalar Amurka na taka birki kai tsaye ga kaddarorin da ake cinikinsu da dala, wanda hakan ke ƙara matsin lamba ga crypto.


ZIRAREWAR KIMANIN $500M CIKIN KASA DA 24 HOURS 

Faduwar farashin bitcoin zuwa $83,000 kai tsaye ana alaƙan tashi ne da mummunar dakan sakwara da masu leverage suka sha. Hakan yayi sanadiyyar awon gaba da mafiya yawan longs position a kasuwar.

Kimanin $487 million long traders sukayi asara sanadin haka. 

Masana na ganin hakan a matsayin wata sharar fage domin mikewar kasuwa.


ABUN LURA.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Rahoton Taron Fed: Abin da 'Yan Kasuwa Ke Jira a Yau Babban Bankin Amurka (Fed) yana fitar da takaitaccen rahoton taronsa na manufofin watan Satumba a yau. 

Kasuwanni suna son sanin ko menene matsayar central banks zuwa ga hauhawar farashin (inflation) da sauran kayan masarufi.

Wannan zai sa mu kalli batutuwa 3:

Tsananta Manufofi (Hawkish): Idan rahoton ya nuna karuwar damuwa kan hauhawar farashi, ana sauran ribar lamuni "treasury" ta ci gaba da ƙaruwa. 

Wannan zai iya lalata matakin bitcoin zuwa $80,000 kai tsaye.

Yanayin Sauki (Dovish/Neutral): Idan Fed ya jaddada raguwar harkokin tattalin arziki ko kasadar kwanciyar hankali ta kudi, ribar lamuni za ta iya samun sauki. 

Wannan zai ba Bitcoin sararin gudanar da gagarumin sake shawagi komawa zuwa $85,000+.

Idan Ba'a Samu Sauyi Ba: Idan rahoton bai bayyana wani sabon abu ba, hankalin kasuwa zai koma kan farashin energy da kuma shigar kudi zuwa lalitar hanyar ETF.

Daga ƙarshe yana da kyau mu ƴan kasuwa mu takaita dogaro da tsarin bashin leverage domin neman riba a kasuwa.

Zaman dakon rahoton FED yana da matukar muhimmanci domin fahimtar alkiblar kasuwa ta gaba.

Ku faɗa mana ra'ayoyin ku akan tsarin "leverage"