Central Bank of Nigeria (CBN) ta ɗaga matakin tsaro a harkokin kuɗi. Daga ranar 1 ga watan Mayu, 2026, sabbin dokoki na BVN zasu fara aiki, kuma zasu canza yadda muke amfani da manhajojin banki.
Ko da yake dokokin na iya zama masu tsauri, an tsara sune da buri guda ɗaya: a hana masu damfara damar kwashe kuɗin mutane cikin sauƙi.
Ga cikakken bayani da yadda za ka shirya.
1. App ɗaya, waya ɗaya
Yanzu baza ka iya amfani da banking app ɗinka a wayoyi da yawa ba. Sabuwar doka ta tanadi cewa app ɗin bankinka zai yi aiki a waya ɗaya kacal a lokaci guda. Idan ka shiga account ɗinka daga wata sabuwar waya, za a fitar da kai daga tsohuwar. Wannan mataki yana taimakawa wajen hana hackers samun damar shiga asusunka daga wani wuri ba tare da saninka ba.
2. Sauya lambar waya sau ɗaya kacal a rayuwa
Wannan shine daya daga cikin manyan canje-canje. Yanzu za a baka damar sauya lambar wayar dake da alaƙa da BVN ɗinka sau ɗaya kacal a rayuwarka. Dalilin wannan doka shine rage damfara da ake yi ta hanyar sauya SIM.
Idan karasa layinka kuma ka riga kayi amfani da damar sauyawa sau ɗaya, dole ne kaje banki domin yin cikakken tantancewa ta hanyar biometric domin tabbatar da kai ne.
3. Lokacin jira na awa 24 (“Cooling Off”) a turance
Duk lokacin daka kunna banking app ɗinka a sabuwar waya, za a takaita ayyukan da zaka iya yi na ɗan lokaci. A cikin awa 24 na farko, ba za ka iya tura fiye da ₦20,000 ba. Wannan lokaci zai baka damar tuntubar banki idan aka samu matsala kamar satar waya ko wani yunƙurin satar kuɗi.
4. Tantance fuska da “Liveness Check”
Password da PIN kaɗai ba su isa ba yanzu. Sabbin dokokin sun tanadi amfani da tantance fuska tare da “liveness check". Wannan yana nufin app ɗinka zai iya buƙatar ka ɗauki hoto kai tsaye yayin da kake motsa kai ko kifta ido, domin tabbatar da cewa kai mutum ne na gaske, ba hoto ko deepfake ba.
Za a haɗa wannan da bayananka na NIN da BVN domin tabbatar da ingancin bayanai.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
5. Iyakar shekaru da “Fraud Watchlist”
Iyakar shekaru:
Dole ne mutum ya kai shekaru 18 kafin ya mallaki BVN na kansa. Accounts na yara zasu kasance a ƙarƙashin kulawar wani babban mutum.
Fraud Watchlist:
Idan aka gano BVN ɗinka yana da alaƙa da wani abu da ake zargi da damfara, ana iya daskare duk asusun dake da alaƙa da shi a duk bankunan Najeriya nan take har sai an kammala bincike.
Me ya kamata kayi yanzu?
1. Ka tabbatar lambar wayar da ke haɗe da BVN ɗinka ita ce wadda kake sonci gaba da amfani da ita.
2. Idan kana son yin canji, kayi kafin 1 ga watan Mayu, 2026 domin kauce wa matsaloli.
3. Ka tabbatar sunanka da ranar haihuwa sun yi dai-dai tsakanin NIN da BVN.
Kammalawa
Zamanin damfara mai sauƙi yana ƙarewa. Duk da cewa waɗannan dokoki zasu iya ƙara ɗan wahala wajen amfani da banking apps, tsaron kuɗinka ya fi komai muhimmanci. Ƙarin matakan tsaro kaɗan a yau na iya ceton ajiyarka gaba ɗaya a nan gaba.