Babban Bankin Najeriya, wato CBN, ya fitar da wasu sabbin dokoki guda 10 da suka shafi tsarin Bank Verification Number (BVN), wadanda za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu.
An ce an dauki wannan mataki ne domin rage damfarar yanar gizo, kare asusun banki, da kuma kara tsaro a harkokin bankin dijital da ake yi ta wayoyi da intanet.
Muhimman Sauye-Sauyen Da Za Su Fara Aiki
1. Manhajar Banki Zata Yi Aiki A Na’ura Daya Kacal
Daga yanzu, za ka iya amfani da banking app a waya daya kawai a lokaci guda.
2. Sabuwar Na’ura Zata Fitar Da Tsohuwar
Idan ka shiga manhajar banki a sabuwar waya, tsohuwar wayar za ta fita kai tsaye.
3. Sauya Waya Sai An Kara Tantance Kai
Idan kana son amfani da sabuwar waya, za a sake yin karin bincike ko tantancewa kafin a baka damar shiga.
4. BVN Mai Zargi Zai Shiga Kulawar Awanni 24
Idan an ga wata alama ta zargi a BVN dinka, za a sanya shi a jerin sa ido na tsawon awanni 24.
5. Ana Iya Kulle Asusun Da Aka Gano Matsala
Bankuna na iya dakatar da asusu ko rufe shi na dan lokaci idan an danganta shi da BVN mai matsala.
6. Lambar Wayar Da Aka Hada Da BVN Sau Daya Kawai Za A Canza
Masu amfani za su samu damar canza lambar waya da ke hade da BVN sau daya kacal.
7. An Yi Dokar Don Hana Damfarar SIM Swap
Wannan doka na kokarin dakile masu canza SIM ba tare da izini ba domin shiga asusun mutane.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
8. Shekara 18 Zuwa Sama Kawai Za Su Yi BVN
Mutanen da shekarunsu suka kai 18 ne kawai za su iya yin rijistar BVN da kansu.
9. Yara Sai Ta Hannun Uba Ko Mai Kula
Duk wanda bai kai shekaru 18 ba dole sai ya bude asusu karkashin kulawar iyaye ko guardian.
10. Sabuwar Waya Za Ta Iya Tura ₦20,000 Kawai A Rana Ta Farko
Idan ka kunna banking app a sabuwar waya, a cikin awanni 24 na farko ba za ka iya yin ciniki sama da ₦20,000 ba.
Me Wannan Ke Nufi Ga Jama’a?
Wadannan sabbin dokoki na nufin cewa CBN na kokarin kare kudaden jama’a da hana yawaitar satar bayanai da damfara ta yanar gizo.
Masu amfani da banki su tabbata sun sabunta bayanansu, sun kiyaye wayoyinsu, kuma sun guji bai wa kowa bayanan sirri.
Karshe
Idan kana amfani da mobile banking, ya kamata ka san wadannan dokoki tun yanzu kafin ranar 1 ga watan Mayu. Tsaro ya fi komai muhimmanci a zamanin bankin dijital.
Ku ci gaba da bibiyar Fuchaweb3 domin samun sabbin labarai da bayanai masu anfani cikin harshen Hausa.
Tushen Labari: https://x.com/BashirAhmaad/status/2046186497989021820