Ba'a samar da irin kuɗin da kuke amfani dashi domin su baku aminci ba!

Eh, dakai nake mai karanta wannan rubutun, ka sani; shi tsarin kuɗin fiat na gargajiya ya dogara ne da dillalai (bankuna), gwamnatoci da sauran wasu tsirarun mutane domin samarwa, tura wa, adana ko kuma duk wasu harkokin gudanarwa na kuɗi.

Wannan shi ake cewa massive centralisation "ta yadda kaima dan kallo ne akan dukiyar ka".

Za'a sa maka a rai kaji cewa kai ne ka mallaki dukiyar ka, amma fa a zahiri wasu ne daban suke da iko da ita.

Kudin cypto kai tsaye sai suka zama kishiyar irin wannan tsarin da aka ɗora ku a kai, tsarin bautarwa, kama karya da wayo. Tsarin da ake miƙo maka Naira goma a hannun dama sai kuma a amshi ₦100 daga hagun ka.

Idan har yanzu baka gane ba, crypto ya zo domin ya fitar da kai daga tsohon tsarin gurguzu, tsarin kashin dankali ya sanya maka rigar ƴanci da walwala.


ME YASA ZAKA RUNGUMI CRYPTO DA KYAU?

A tsohon tsarin kuɗin gargajiya, kaine da dukiya amma wasu ne ke cin gajiyar ta. 

Misali, 

Kaine kayi aiki na wahala ka samu kuɗi sai ka kai banki ajiya don kana tunanin nan zaka samu salama.

To bari kaji abunda ba zasu taɓa gaya maka ba, kuma ba zasu so ka sani ba. 

Su bankin dai zasu ajiye maka 10% na kuɗin da ka kai ajiya sauran 90% kuwa su bayar dashi rance. Ba tareda ka sani ba.

Ana kiran tsarin "Bankin Fractional Reserve System".

Hallau dai sai kayi dace zaka samu wani ɗan kaso na ribar da suka farauto daga dukiyar da ka kai musu ajiya. 

Yayinda kake jin daɗin ganin lambobi a wayar ka, wasu kuma na jin daɗin more gumin naka. 

Kuma hakan ba zaisa suƙi:

Kulle maka asusu a koda yaushe ba.

Takaita maka wasu mu'amaloli.

Sauya manufofin kuɗi da ka iya tauye wahalhalun da kayi a baya.

Kayyade yadda zaka kashe kuɗaɗen ka. 

Sanya ido akan yawan kuɗin da ke iya mallaka.


SABON TSARIN CRYPTO. 

Jama'a sune hukuma.

Abunda suka amince akai shine doka.

Kwamfuta ke zartar da duk wata mu'amala. Cikin tsari, tsafta cewa. 

Babu son rai.

A crypto kaine bankin kanka.

Kai dai zakaci gajiyar dukiyar ka sai kuma wanda ka so.


CRYPTO BA KIRIPTOL BA. 

Ba kowane kuɗin cryptocurrency ce yake da cikakken decentralization ba.

Anan si kunyi duban tsanaki. 

Saboda karku rungumi Kura da fatar Akuya.

Wani blockchain na iya samun ikon da ya fi karkata ga wasu tsirarun mutane ko ƙungiyoyi ta fuskar:

Mallakar token

Ikon validators

Ikon mining

Ci gaban software

Kayan aikin blockchain

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Liquidity a exchanges

Saboda haka, kasancewar wani abu yana kan blockchain kaɗai bai isa ba.

Tambayar da zaka yiwa kanka itace:

Wa ke da iko a kan wannan network?

Saboda karka gudu daga rana kuma ka faɗa cikin wuta.


BANBANCIN TSOHON TSARI DA SABON TSARI.

Kudin gargajiya: hukuma ke baka dama a kai

Kuɗin crypto: dokokin kwamfuta (Code) ke zartarwa 

Kuɗin gargajiya: kai ma ɗan kallo ne 

Kuɗin crypto: kai ke da cikakken iko akai

Kuɗin gargajiya: karyewar daraja (inflation)

Kuɗin crypto: ribata tsohon lokaci 

Manufar Crypto:

Babbar hujjar cryptocurrency ba wai bankuna ko gwamnatoci ba su da kyau ba ne.

Abunda crypto yazo dashi shi ne:

Ya kamata mutane su samu damar amfani da tsarin kuɗi wanda za su iya bincika dokokinsa da kansu, maimakon dogaro gaba ɗaya da hukuma guda.

Wannan shi ne ginshikin ƴanci.

Kafin ka amince wa kuɗin crypto, tambayi kanka:

Wa ke sarrafa samar da token?

Wa ke tabbatar da mu'amaloli?

Yaya tsarin yake da decentralization?

Wa zai iya sauya dokokinsa?

Shin mai amfani zai iya sarrafa kadarar

sa da kansa?

Me zai faru idan babban intermediary ya daina aiki?

Crypto ko Fiat? Ku fada mana ra'ayoyin ku.