Central Bank of Nigeria (CBN) ta Ι—aga matakin tsaro a harkokin kuΙ—i. Daga ranar 1 ga watan Mayu, 2026, sabbin dokoki na BVN zasu fara aiki, kuma zasu canza yadda muke amfani da manhajojin banki.

Ko da yake dokokin na iya zama masu tsauri, an tsara sune da buri guda Ι—aya: a hana masu damfara damar kwashe kuΙ—in mutane cikin sauΖ™i.

Ga cikakken bayani da yadda za ka shirya.

1. App Ι—aya, waya Ι—aya

Yanzu baza ka iya amfani da banking app Ι—inka a wayoyi da yawa ba. Sabuwar doka ta tanadi cewa app Ι—in bankinka zai yi aiki a waya Ι—aya kacal a lokaci guda. Idan ka shiga account Ι—inka daga wata sabuwar waya, za a fitar da kai daga tsohuwar. Wannan mataki yana taimakawa wajen hana hackers samun damar shiga asusunka daga wani wuri ba tare da saninka ba.

2. Sauya lambar waya sau Ι—aya kacal a rayuwa

Wannan shine daya daga cikin manyan canje-canje. Yanzu za a baka damar sauya lambar wayar dake da alaΖ™a da BVN Ι—inka sau Ι—aya kacal a rayuwarka. Dalilin wannan doka shine rage damfara da ake yi ta hanyar sauya SIM.

Idan karasa layinka kuma ka riga kayi amfani da damar sauyawa sau Ι—aya, dole ne kaje banki domin yin cikakken tantancewa ta hanyar biometric domin tabbatar da kai ne.

3. Lokacin jira na awa 24 (β€œCooling Off”) a turance

Duk lokacin daka kunna banking app Ι—inka a sabuwar waya, za a takaita ayyukan da zaka iya yi na Ι—an lokaci. A cikin awa 24 na farko, ba za ka iya tura fiye da ₦20,000 ba. Wannan lokaci zai baka damar tuntubar banki idan aka samu matsala kamar satar waya ko wani yunΖ™urin satar kuΙ—i.

4. Tantance fuska da β€œLiveness Check”

Password da PIN kaΙ—ai ba su isa ba yanzu. Sabbin dokokin sun tanadi amfani da tantance fuska tare da β€œliveness check". Wannan yana nufin app Ι—inka zai iya buΖ™atar ka Ι—auki hoto kai tsaye yayin da kake motsa kai ko kifta ido, domin tabbatar da cewa kai mutum ne na gaske, ba hoto ko deepfake ba.

Za a haΙ—a wannan da bayananka na NIN da BVN domin tabbatar da ingancin bayanai.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

5. Iyakar shekaru da β€œFraud Watchlist”

Iyakar shekaru:

Dole ne mutum ya kai shekaru 18 kafin ya mallaki BVN na kansa. Accounts na yara zasu kasance a Ζ™arΖ™ashin kulawar wani babban mutum.

Fraud Watchlist:

Idan aka gano BVN Ι—inka yana da alaΖ™a da wani abu da ake zargi da damfara, ana iya daskare duk asusun dake da alaΖ™a da shi a duk bankunan Najeriya nan take har sai an kammala bincike.

Me ya kamata kayi yanzu?

1. Ka tabbatar lambar wayar da ke haΙ—e da BVN Ι—inka ita ce wadda kake sonci gaba da amfani da ita.

2. Idan kana son yin canji, kayi kafin 1 ga watan Mayu, 2026 domin kauce wa matsaloli.

3. Ka tabbatar sunanka da ranar haihuwa sun yi dai-dai tsakanin NIN da BVN.

Kammalawa

Zamanin damfara mai sauΖ™i yana Ζ™arewa. Duk da cewa waΙ—annan dokoki zasu iya Ζ™ara Ι—an wahala wajen amfani da banking apps, tsaron kuΙ—inka ya fi komai muhimmanci. Ƙarin matakan tsaro kaΙ—an a yau na iya ceton ajiyarka gaba Ι—aya a nan gaba.