Yana daga cikin abubuwan da mutane sukeyi kullum ba tare da tunani ba haɗa free WiFi a café, airport, hotel, ko shopping mall. Yana da sauƙi. Yana kama da babu matsala. Amma ga cybercriminals, wannan yana daga cikin hanyoyi mafi sauƙi na satar bayananka, passwords ɗinka, da shiga accounts ɗinka.
Yadda Harin Ke Aiki
Mafi shahararren hari akan public WiFi ana kiransa a turance Man-in-the-Middle attack. Criminal wato mai laifi yana sa wata device tsakanin waya ko laptop ɗinka da internet connection na gaskiya. Duk wani data da kake turawa ko karɓa yana fara wucewa ta wajen criminal ɗin. Login credentials, banking sessions, personal messages duk suna iya zama a bayyane kuma ana iya sace su.
Akwai ma mafi sauƙi daga haka: criminals suna ƙirƙirar fake WiFi hotspots masu suna kamar na gaskiya. “Airport_Free_WiFi.” “CafeGuest.” “Hotel_Lobby.” Sai ka haɗa kana tunanin official network ne, alhali kai tsaye kana haɗe da equipment na criminal. Duk abin da kake yi online ana iya sa ido akai.
Me Ke Cikin Haɗari?
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Idan ka shiga email ɗinka, social media, ko bank account ta public WiFi ba tare da kariya ba, bayananka na iya shiga hannun hackers. Idan ka shiga crypto exchange, session ɗinka na iya zama hijacked. Ko browsing habits da personal information ɗinkama ana iya tattarawa domin a yi amfani da su wajen future attacks.
Sauƙaƙan Hanyoyin Kariyar Kai
VPN — wato Virtual Private Network — yana encrypting duk data da ke fita daga device ɗinka, yana sa ya zama unreadable ga duk wanda yake ƙoƙarin interception a public network. Reliable VPN services kamar ProtonVPN ko NordVPN suna ɗaukar ƴan kuɗi kaɗan a wata kuma ya kamata duk wanda yake aiki ko yin transactions online ya ɗauke su da muhimmanci.
Bayan VPN kuma: kada ka shiga banking ko crypto accounts a public WiFi ba tare da VPN ba. Kashe automatic WiFi connection a device ɗinka. Kullum ka tabbatar da exact network name tare da staff kafin ka haɗa. Kuma idan kana cikin shakka — ka yi amfani da mobile data ɗinka maimakon public WiFi.