Hakika abubuwan bazata, farin ciki, da tsoro sun faru a cikin wannan makon, a matsayin ka na ɗan kiripto bai kamata ka bari a baka labarin irin wainar da ake toyawa ba. Wasu daga cikin kanun: Bitcoin ya fuskanci matsin lamba, Ethereum yana nunawa kasuwar crypto tirjiya, yayin da manyan kamfanonin kuɗi ke ƙara zurma ƙafa zuwa duniyar blockchain.
BTC a matakin $80k
Matsin lamba ta tilastawa bitcoin sake komawa yankin $77k maimakon tsallen baɗaken da yayi a baya zuwa farashin $80k
Daga cikin manyan abubuwan da suka matsa kasuwar sun haɗa da hauhawar farashin mai, damuwar inflation da mutane suka shiga bisa tsammanin yiwuwar Fed zata ƙara interest rate.
Makomar Ethereum
Ethereum ya kasance ɗaya daga cikin mafi ƙarfi daga cikin manyan assets, bayan gagarumin tashi da yayi a farkon wannan wata.
Masu nazarin taswirar motsin farashi (chart) nada ra'ayin ETH din ka iya sake wani sabon motsi idan ya samu damar karya manyan resistance levels na yanzu.
Hankali Yana Sake Karkata Kan Bitcoin ETFs
Duk da faduwar farashin BTC, Bitcoin ETFs sun samu sama da $1B na inflows cikin kwanaki uku na trading.
Wannan na nuna cewa wasu institutional investors har yanzu suna amfani da dips wajen ƙara exposure zuwa Bitcoin.
Abinda Ya Faru Da Liquid Network
Ɗaya daga cikin manyan labaran tsaro na makon shi ne harin da aka kai wa Liquid Network, inda aka cire kusan 4,000 BTC, wanda darajarsa ta kai kusan $320M a lokacin.
Harin ya sake tunatar da kasuwa cewa ko da blockchain na da ƙarfi, infrastructure da ke kewaye da shi na iya zama babban wurin haɗari.
Nasdaq Tana Shinshinar Crypto
Wani babban labari: Nasdaq ta sanar da zuba jarin $100M a kamfanin da ke bayan Kraken.
Manufar ita ce ƙara bunƙasa tokenized equities—wato amfani da blockchain wajen wakiltar da kasuwanci da wasu traditional financial assets.
Wannan na iya zama wani muhimmin mataki wajen haɗa Wall Street da blockchain.
Ƙoƙarin Tsaftace Kasuwancin Crypto
A Amurka, CLARITY Act ya ci gaba da jan hankali yayin da 'yan siyasa da masana'antar crypto ke fafutukar ganin yadda za a tsara dokokin kasuwar.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Ana sa ran wani muhimmin mataki kan dokar a Senate a ranar 15 Satumba.
Kasuwar Stablecoins
Stablecoins sun ci gaba da faɗaɗa zuwa ƙarin blockchain networks, yayin da prediction markets kamar Polymarket da Kalshi suka ci gaba da samun gagarumin trading volume.
Wannan na nuna cewa crypto ecosystem yana ƙara faɗaɗa fiye da Bitcoin da trading kawai.
Alkiblar Kasuwar Crypto Bisa Rahoton Wannan Satin:
Institutional adoption ↑
Tokenization ↑
Stablecoins ↑
Regulation ↑
Security risks ↑
Macro pressure ↑
A takaice, wannan yana nuna mana cewa yanzu kasuwancin crypto ya wuce matakin speculation da muka sani. Manyan kamfanonin kuɗi suna ƙara amfani da blockchain wajen gina sabon tsarin financial infrastructure.
Amma akwai gargadi:
Yayin da adoption ke ƙaruwa, haɗarin tsaro, regulation da tasirin tattalin arzikin duniya ma suna ƙaruwa.
Tambayoyin Da Zamu Biɗi Amsoshin Su Mako Mai Kamawa.
Bitcoin zai dawo sama da $80K?
Ethereum zai ci gaba da ƙarfinsa?
Me zai faru da CLARITY Act?
Shin tokenization zai zama babban crypto narrative na gaba?
Kuma... shin wannan pullback dama ce ko farkon wani babban correction?
Wacce tambaya zaku iya yi mana kintacen amsarta tun yanzu?