Kasuwar crypto ta sake shiga wani sabon lale!
Abunda ake yi masa kallon yayi da zai yi tashe ya wuce, ko kuma wani dandalin canki-canki, salon kasuwanci mai hatsari da bai kai a mayarda hankali a kansa ba.
Yau mun wayi gari crypto ya zama kadara.
Manyan kamfanoni cinikayya na duniya, hada-hadar kuΙi da Ιai-Ιaikun investors suna sanya kuΙaΙen su domin kwadayin irin romon da suke hange.
Da kai nake mai karanta wannan rubutun, shin har yanzu kana jiran sai ance maka ka fara ribatar kasuwancin crypto?
ABU MAI MUHIMMANCI
Abun burgewa da kuΙaΙen crypto shine tsarin Ζ΄anci, takaita inflation.
Yayin da suke samun karΙuwa kuma supply dinsu baya karuwa.
Hakan na haifar da demand, demand kuma yana Ζara musu daraja.
Shigowar manyan hukumomi ya sake Ζarawa abun citta.
Yancin mallakar dukiyar ka, kyawawan dokoki domin kariya, irin kuΙin da yake tururuwa da kuma sauΖin mallaka ba tare da ciwon kai ba ya sake baiwa investors Ζwarin gwiwar amincewa kuΙaΙen crypto.
CRYPTO YA SHIGA JERIN MANYAN KADARORIN DUNIYA
Idan ka duba da kyau zaka ga cewa yanzu crypto yana tasirantuwa da:
Global liquidity
Interest rates
U.S. dollar strength
Institutional flows
Market leverage
Investor sentiment
Yanzu price action bai kai dalilin yanke makomar crypto ba.
MANYAN ABUBUWAN DUBAWA
Jin waΙannan jawaban bazai sa kai kuma ka saki jiki ba.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Hallau dai kasuwar crypto tana buΖatar taka tsantsan saboda hatsarin volatility.
Musamman kai trader. Dole ne ka sanya idanu hakan waΙannan:
Open Interest: Zai taimaka maka ka fahimci yawan leverage da yake shiga kasuwa.
Funding Rates: Yawan positions da aka buΙe. Long ko Short shima yana taimakawa wajen fahimtar alkiblar kasuwa.
Liquidity: Cewar sauye sauyen shirin hukumomi yana shafar kasuwar kai tsaye.
Price Structure: Abunda ya shafi support, resistance ko trend yana da matukar muhimmanci.
CRYPTO A BABBAN MADUBI
Tairsin crypto a yanzu ya wuce ka tsaya sauraron ko tambayar matakin farashi.
Alaji yanzu ana maganar matakin crypto ne a kasuwar kuΙaΙe ta duniya.
Kasuwancin crypto a yanzu yana sake samun karΙuwa a gurin jama'a. Kuma bisa ga alkaluma farin jinin sa zai cigaba da yaΙuwa.
Abun ya wuce jiran tsammanin sabon coin na yayi. Da sannu crypto na samun matsuguni a cikin global financial market.
Koma dai menene shirin ka, to kayi nazari fiye da kallon taswirar candle sticks.
Ku faΙa mana irin hangen da kuke yiwa kasuwar crypto nan gaba.