A ranar 1 ga Satumba, 2026, manyan cibiyoyin kuɗi 21 daga sassa daban-daban na duniya sun sanar da wani shiri mai girma: ƙirƙirar kuɗin crypto domin sauƙaƙa mu'amalar kasuwanci, wanda ake sa ran fara amfani da shi a shekarar 2027.

A cikin waɗannan bankuna akwai Bank of America, Citi, Goldman Sachs, Wells Fargo, UBS, Deutsche Bank, Santander, BBVA, MUFG da Standard Bank, tare da Fidelity Investments da WisdomTree.

Idan ma baka fahimta ba to bari kaji, wannan ba labarin bankuna sun sayi Bitcoin ba ne. Abin da ke faruwa ya fi haka zurfi: ana maganar bankunan duniya sun ga uwar bari babu shiri yanzu sun tsunduma cikin harkar crypto. Tunda kake ka taɓa tunanin za'a zo lokacin da bankuna zasu dinga ƙirƙirar coins na nasu na kansu? to yanzu dai live abun yake faruwa 😅


Kofar Da Bankunan Ke Shirin Budewa:

- stablecoins;

- tokenized deposits;

- blockchain settlement;

- programmable payments;

- da digital custody.

Kai daganin wannan kasan ba irin crypton muce nida kai ba. Manufar ita ce a sauƙaƙa biyan kuɗi tsakanin ƙasashe, rage jinkiri da kuma ba da damar yin settlement 24/7—ba tare da jiran lokutan aiki na bankuna ba.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Stablecoin zai iya zama kuɗin dijital da ake amfani da shi a fili, yayin da tokenized deposit yake wakiltar kuɗin banki a kan blockchain. Dukansu na iya aiki tare, suna buɗe sabuwar kofa ga kasuwancin crypto da tsarin kuɗin duniya.

Wannan ba yana nufin USDT ko USDC za su ɓace ba. Maimakon haka, za a iya samun gasa mai ƙarfi tsakanin bankuna da kamfanonin crypto wajen gina sabuwar financial infrastructure. Wannan gasa na iya haifar da ƙarin sabbin abubuwa, saurin mu’amala da kuma damar saka hannun jari a fannin crypto.

Shigar bankuna cikin blockchain ba lallai ya zama crypto adoption kai tsaye ba. Amma yana nuna wani abu mai girma: blockchain technology na shiga cikin tsarin harkokin kuɗi na duniya.

Saboda haka, ku ƴan uwana ƴan kiripto ya kamata ku kula da wannan sauyi. Karku tsayar da tunanin ku iya kan farashin portfolio dinku, idan ma baku saniba to abun ya wuce haka; wannan ainihin juyin juya hali ne dake faruwa a bayan fage, inda harkar kuɗaɗen gargajiya ke kaura zuwa kasuwancin crypto.

Babban sauyi ba lallai ya zo da hayaniya ba. Wani lokaci abun yana zuwa ne cikin sanarwar banki, cikin sabon tsarin biyan kuɗi ko kuma cikin wata fasahar da ke aiki a bayan fage.

Kamar yadda wannan karon, bankuna 21 suka busa ƙahon su.