A yau idan ka duba kafofin sada zumunta, zaka ji ana ta surutu cewa crypto ya mutu, kasuwa ta lallace, kuma kowa ya kwashe kudinsa ya gudu. To amma tambayar a nan ita ce: shin da gaske crypto din ne ya mutu, ko kuwa tsohon salon bariki na cuwa-cuwa da neman kudin dare daya ne ya zo karshe?
Gaskiyar magana ita ce, tsohon tsarin ne ya mace, amma sabon juyin juya hali yanzu aka fara shi. Don haka, bismillah, bari kuji asalin abunda yake faruwa.
1. Zamanin "Cuwa-Cuwa" Ya Kare
Dole mu fuskanci gaskiya; lokacin da kowa yake shigowa crypto da burin yin arziki na dare daya ya wuce. Wancan zamanin shi ne ya mutu, kuma hakan ya faru ne saboda wadannan dalilan:
Karshen Zamanin Shitcoins: Lokacin da zaka sayi wani memes kanka tsaye, kana samun 10,000% a rana guda ba tare da wani amfani na gaske ba, gaskiya ya zama tarihi. Yanzu kasuwa ta daina daukar garari.
Shigowar Gwamnatoci: Da can ana zancen "babu ruwanmu da gwamnati," amma yanzu kowa ya san dokoki sun matsa. Idan project ba zai kiyaye regulations ba, to tafiyarsa ba zata yi nisa ba.
Mazambata Sunyi Ζaranci: Ruftewar manyan tsare-tsare na boge da asarar kudade sun gyara wa mutane zama. An tace kasuwa, ba kamar lokutan baya ba.
A takaice: Wannan ba mutuwa ba ce, sai dai mu kirashi sabuwar shimfida domin dai-daita zama
2. Gagarumin Sauyin Dake Tafe
Maganar da ake ciki yanzu ita ce crypto ya balaga. Bayan kura ta lafa, abubuwan da suka rage a kasa sune ainihin kashin bayan tafiyar. Yanzu muna a lokacin da manyan 'yan wasa na gaske suka karbe ragamar kasuwa:
Real-World Assets (RWA) Su Ne A Gaba
Yanzu an daina zancen hotunan birai na NFT wadanda ba su da amfani. Manyan kamfanoni yanzu suna dawo da abubuwan gaskiya kamar gidaje, zinari, da hannun jarin kamfanoni zuwa kan Blockchain. Wannan shi ne asalin juyin juya halin.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Shigowar Masu Manyan Hannun Jari (Institutions)
Yanzu ba maganar tsoro ba ne; manyan kamfanonin gudanar da dukiya irinsu BlackRock da Fidelity ne ke gaba-gaba yanzu wajen tura motar crypto ta hanyar Bitcoin da Ethereum ETFs. Wannan ya nuna cewa crypto ya zama halastaccen tsarin kudi na duniya.
Layer-2 Sun Kawo Sauki
Idan ka tuna lokacin da tura kudi ta Ethereum yake da tsada da jinkiri, yanzu abin ya canza. Fasahohin Layer-2 (kamar su Arbitrum, Optimism, da Base) sun sa hada-hada ta zama cikin sauri kuma a kan farashi kalilan.
3. To, Me Wannan Ke Nufi Ga Sauran Yan Kasuwa?
Idan kai mai trading ne ko mai rike da kudi na dogon lokaci (HODLer), dabarunka na baya dole su sauya idan kana son cin gajiyar wannan sabon juyin juya halin.
Yi Karatun Ta Nutsu: Ka daina siyan coins kawai saboda kowa yana surutu a kai a TikTok ko Telegram.
Tambayi kanka: wace matsala wannan project din yake magancewa? Yi Fundamental Analysis na gaske.
Tsohon tsarin crypto ya mutu saboda ya ginu ne akan hayaniya, fargaba, da son neman kudi ta barauniyar hanya. Amma sabon salon da aka fito da shi yanzu ya fi karfi, ya fi tsari, kuma ya dogara ne akan amfani na gaske na fasahar Blockchain.
Kada ka bari labaran firgici na FUD su fitar da kai daga kasuwa. Crypto bai mutu ba; kawai ya canza salo ne ya dawo na kwararru. Tambayar ita ce: Shin kana shirye ka canza takunka ka bi sahun sabon juyin juya halin, ko zaka tsaya kana kallo?