Kasuwar Crypto ta sake motsawa. Bitcoin ya dawo da ƙarfi, Ethereum da wasu manyan altcoins sun fara tashi, kuma yanayin kasuwa ya sauya daga tsoro zuwa fata. Sai dai hausawa sukan ce "ba girin-girin ba, tai mai": Shin da gaske bull season ɗin ko kuwa wata maƙarƙashiya?
Kasuwar crypto tanada wata ƙa'ida; yawanci farin ciki yana saurin faruwa kafin tabbaci.
A matsayin ka na ɗan crypto, yau zaka iya wayar gari cikeda fargaba, tsoro tareda yanke ƙauna, gobe kuma ka cika da murna tareda babban fata. Take zaka fara tunanin babu wata matsala kuma.
Sai dai kasuwar crypto bata bin abunda zuciyarka ke marari.
A halin yanzu, abin da muke gani ya fi kama da babban sauyin yanayi da ke bukatar ƙarin tabbaci kafin a kira shi cikakken sabon Bull Market.
Tashin Bitcoin, Shin Akwai Dalili?
Tsakanin jiya da yau kaɗai, Bitcoin yayi babban pump har zuwa sama da $77,000, bayan dogon suma daga kusan $60,000 da aka gani a baya. Rahotanni sun nuna cewa Bitcoin ya samu kusan kashi 21% a cikin mako guda—ɗaya daga cikin mafi ƙarfi da aka gani cikin shekaru biyu.
Wannan ba ƙaramin motsi ba ne.
A wannan makon, Bitcoin Spot ETFs a Amurka sun samu kusan dala biliyan 1.6 na net inflows daga Litinin zuwa Alhamis, yayin da ranar Alhamis kaɗai aka samu kusan dala miliyan 606. Wannan shi ne mafi ƙarfin weekly inflow da aka gani a shekarar 2026.
Wasu na ganin ba iya zarafin kuɗin ETF ba ne. Akwai:
Yanayin kasuwar Treasury da liquidity.
Raɗe-raɗin tabbatuwar bayyananniyar dokar crypto a Amurka ya ƙara ƙarfafa confidence.
Ma'aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da ƙara sayen dogayen Treasury bonds, lamarin da ya taimaka wajen rage matsin lamba daga hauhawar yields. Wannan ya taimaka wajen farfaɗo da wasu risk assets, ciki har da Bitcoin.
A gefe guda kuma, ana ci gaba da samun motsi wajen samar da tsarin dokokin crypto a Amurka, musamman batun Clarity Act, wanda zai iya ƙara fayyace matsayin digital assets.
Wannan haɗin gwiwar abubuwa uku yana da muhimmanci.
Domin Bull Market mai ɗorewa yawanci baya farawa da chart kawai.
Yana farawa ne lokacin da kuɗi, liquidity, confidence da demand suka fara tafiya a hanya ɗaya.
To, Shin Wannan Bull Season Ne?
Amsar gaskiya ita ce: ko Satoshi ba zai iya baka wannan tabbacin ba.
Amma akwai alamun da suka fi kyau fiye da na makonnin baya.
Wani babban abin lura shi ne cewa Bitcoin ba shi kaɗai yake motsawa ba. Ethereum ma ya samu babban farfaɗowa, yayin da wasu manyan altcoins suka fara samun ƙarfi. Wannan na iya zama farkon abin da ake kira market breadth—wato motsin kasuwa ya fara yaɗuwa daga Bitcoin zuwa sauran manyan assets.
Amma har yanzu akwai bambanci tsakanin rally da Bull Market.
Rally na iya ɗaukar kwanaki ko makonni.
Bull Market kuwa yana buƙatar lokaci.
Yana buƙatar kasuwa ta kafa higher highs da higher lows, volume ya tabbatar da motsin, liquidity ya ƙaru, kuma manyan kudade su ci gaba da shigowa.
Saboda haka, abin da muke gani yanzu ya fi dacewa a kira shi:
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
“Bullish recovery mai ƙarfi da ke buƙatar confirmation.”
Tukuna, wannan bai zama hujjar ƙarshe cewa sabon Bull Run ya fara ba.
Babban Abinda Zai Iya Mayarda Wannan Zuwa Tarko
A nan ne ya kamata kai mai bibiyar kasuwa kayi hankali.
Saboda lokacin da Bitcoin ya tashi da sauri, mutane kan fara shiga kasuwa saboda tsoron rasa damar samun riba—FOMO.
Misali:
Mutane sun ga Bitcoin yana tashi → Nan kowa zai fara tururuwa → leverage zai ƙaru → hakan zai sake cilla farashin ya ƙara hawa → kowa ya fara tunanin Bull Run ya dawo → anan kuma manyan investors zafu fara zame jikin su → sai kasuwa ta juya.
Wannan shi ne irin yanayin da zai iya mayar da rally zuwa bull trap.
Abokin kasuwa ya kamata ka fahimci wannan: Bitcoin ya samu gagarumar tashin farashi cikin ɗan lokaci, yayin da wasu rahotanni suka nuna cewa short positions da dama anyi liquidating din su yayin wannan motsi. Wannan yana nufin wani ɓangare na tashin ya samu ƙarfi daga short squeeze, ba wai asalin demand ba.
Short squeeze na iya taimakawa farashi ya tashi sosai cikin sauri.
Amma ba shi kaɗai ne yake tabbatar da Bull Market ba.
Da Sauran Tsalle?
Kafin muyi hanzarin shiga kasuwa, yana da kyau mu kalli waɗannan alkaluma:
1. Cigaba da ɗorewar ETF inflows.
2. Ya zamana Bitcoin yayi maintaining manyan support levels.
3. Fara murmurewar alts coins.
4. Abin da ke faruwa da dollar, Treasury yields, interest-rate expectations da liquidity na duniya na iya canza yanayin kasuwa cikin sauri.
5. Volume. Farashi yana iya tashi saboda ƙarancin liquidity. Amma Bull Market na gaske yana buƙatar volume mai ɗorewa.
Idan farashi yana hawa amma volume da participation ba sa bin sa, wannan na iya zama gargadi.
Daga ƙarshe: ka iya allon kafin ka wanke