Kasuwar cryptocurrency ta shiga wani sabon yanayi a shekarar 2026. Bayan October crash da aka gani shekarar 2025, yanzu hankalin masu zuba jari ya koma rubu'i na ƙarshe (Q4) wannan shekarar, wanda a tarihi yake ɗaya daga cikin lokutan da Bitcoin kan yi manyan motsi.
Sai dai tambayar ita ce: me zai faru a Q4 na wannan shekara?
Masana sun yi imanin cewa akwai wasu manyan alamomi guda biyar da za su iya ba da haske kan inda Bitcoin zai dosa a watannin Oktoba zuwa Disamba.
1. Manufofin Babban Bankin Amurka (Federal Reserve)
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke tasiri kan Bitcoin ba fasahar blockchain ba ce, illa tattalin arzikin duniya.
Idan Federal Reserve ya rage kuɗin ruwa (Interest Rates), hakan kan sa masu saka jari su koma kadarori masu haɗarin gaske kamar Bitcoin. Amma idan aka ci gaba da tsaurara manufofin kuɗi, hakan kan rage yawan kuɗin da ke shiga kasuwar crypto.
Saboda haka, duk wani jawabi daga Fed a cikin watanni masu zuwa zai iya janyo gagarumin motsi a kasuwa.
2. Shigowar Kuɗin Manyan Hukumomi Ta Bitcoin ETFs
A cikin shekarun baya, Bitcoin ETF ya zama wata muhimmiyar hanya da manyan kamfanoni da cibiyoyin kuɗi ke amfani da ita wajen saka jari.
Lokacin da aka samu yawan kuɗin da ke shiga ETFs (ETF inflows), hakan kan nuna cewa manyan masu zuba jari suna sake tara Bitcoin. Idan kuma kuɗi na fita daga ETFs, hakan na iya nuna cewa ana rage haɗari. A kwanakin baya an fara ganin dawowar kuɗi cikin ETFs, abin da ya ƙara ƙarfafa fata a kasuwa.
3. Muhimman Matakan Farashi
Masu nazarin fasaha (Technical Analysts) na kallon wasu matakan farashi a matsayin matakai masu muhimmanci.
A halin yanzu:
Yankin kusan $60,000 na ci gaba da zama babban matakin kariya (support).
Yankin $67,000 zuwa $68,000 kuma ya zama babban matakin da masu sayarwa ke karewa (resistance).
Idan Bitcoin ya karya wannan yankin da ƙarfi, akwai yiwuwar kasuwa ta shiga sabon yanayin tashin farashi. Amma idan ya kasa, ana iya sake komawa ƙasa.
4. Makomar 4 Year Circle
Bisa al'ada duk bayan halving na Bitcoin, akwai wani tsarin cycles (zagayen shekaru 4 da kasuwar crypto ke tafiya akai).
Sai dai bayan abubuwan da suka faru a 2025 da 2026, wasu masana suna ganin cewa shigowar manyan hukumomi da ETFs ya fara sauya wannan tsarin. Wasu kuma suna ganin har yanzu Q4 na 2026 na iya zama lokacin da kasuwa za tayi zarafi ƙwarai kafin shiga sabon bullrun na gaba.
Saboda haka, wannan shekara ana iya ganin sabon tsarin kasuwar Bitcoin.
5. Yanayin Tattalin Arzikin Duniya
Ba Bitcoin kaɗai ke motsawa ba.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Abubuwa kamar:
hauhawar farashi (Inflation),
rikice-rikicen siyasa,
ƙarfin dalar Amurka,
da yanayin kasuwannin hannayen jari, duk suna da tasiri ga yadda kuɗi ke shiga ko fita daga kasuwar crypto. Idan yanayin tattalin arziki ya inganta, hakan na iya ƙarfafa masu saka jari su sake komawa kasuwa.
Me Tarihi Ke Nunawa Game da Q4?
A tarihi, rubu'i na ƙarshe na shekara yana daga cikin lokutan da Bitcoin kan yi kyakkyawan aiki. Amma masana sun yi gargaɗi cewa tarihin kasuwa ba tabbacin abin da zai faru ba ne.
Kasuwar 2026 ta bambanta da ta shekarun baya saboda:
ƙaruwar tasirin ETFs,
shigowar manyan kamfanoni,
sabbin dokokin gwamnati,
da kuma sauye-sauyen tattalin arzikin duniya.
Abin da Ya Kamata Masu Zuba Jari Su Yi
Maimakon ƙoƙarin bin Yarima domin shan kiɗa ko kuma shaci faɗi marasa kan gado a kafafen sada zumunta, yana da muhimmanci a ci gaba da lura da:
Manufofin Federal Reserve.
Shigowa ko ficewar kuɗi daga Bitcoin ETFs.
Muhimman matakan farashin Bitcoin.
Bayanai kan tattalin arzikin duniya.
Da kuma yanayin masu saka jari gaba ɗaya.
Wadannan su ne abubuwan da za su fi ba da haske kan inda kasuwar Bitcoin za ta dosa.
Q4 na shekarar 2026 na iya zama ɗaya daga cikin lokutan da za su fi muhimmanci ga kasuwar Bitcoin. Duk da cewa akwai alamun da ke nuna yiwuwar farfaɗowa, har yanzu akwai ƙalubale da dama da ka iya sauya alkiblar kasuwa cikin sauri.
Ga masu zuba jari, abin da ya fi dacewa shi ne bin bayanai na gaskiya, yin nazari kafin yanke hukunci, da kuma guje wa ɗaukar mataki bisa jita-jita kawai.