Gabatarwa

Pump.fun wani dandamali ne da aka gina a kan Solana (kuma yanzu har da Ethereum da Base), wanda ya sauya yadda ake kirkirar memecoins a Web3.

A baya, kirkirar coin yana bukatar:

  • Ilimin coding
  • Ko kuma babban liquidity

Amma yanzu, Pump.fun ya sauΖ™aΖ™a komai kowa zai iya kirkirar coin da kusan $2 kacal.

Yadda Pump.fun Yake Aiki

Babban manufar dandamalin ita ce β€œFair Launch”  wato kowa yana farawa daga mataki daya.

Ga yadda tsarin yake:

  • Coin yana farawa da Ζ™ananan market cap (~$5,000)
  • Idan mutane suka ci gaba da siya, darajar tana tashi
  • Da zarar ta kai kusan $69,000, ana kai liquidity zuwa Raydium
  • Sannan a burn liquidity domin Ζ™ara tsaro

πŸ‘‰ Wannan tsarin yana rage damfara na farko, amma ba ya kawar da haΙ—ari gaba Ι—aya.

Abubuwan Da Ya Kamata Ka Duba Kafin Saka Kudi

1. Branding (Hoto da Suna)

Coin mai kyau yawanci yana da:

  • Hoto mai inganci
  • Suna mai jan hankali ko trending

πŸ‘‰ Idan ka ga hoto mara kyau ko suna mara ma’ana yi hattara.

2. Social Links (Community)

Duba ko coin yana da:

  • Telegram
  • X (Twitter)

πŸ‘‰ Shiga ka gani:

  • Shin mutane na gaske ne?
  • Ko bots ne kawai?

3. Dev Holdings

Duba β€œHolders”:

  • Idan Dev yana da fiye da 10%, akwai haΙ—arin dump
  • Coin mai kyau yana da rabon mallaka mai kyau

4. Comment Section

Karanta ra’ayoyin mutane:

  • Shin ana zargin Dev da damfara?
  • Shin akwai gargadi daga wasu users?

πŸ‘‰ Wannan na iya ceton ka daga asara.

Yadda Ake Gane Rug Pull (Damfara)

Step 1: Dev Sell

Idan Dev yana sayarwa tun da wuri: πŸ‘‰ Alamar rashin tabbas ko shirin guduwa.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Step 2: Bundled Launch

Masu damfara na amfani da bots:

  • Wallets da yawa (20–50)
  • Suna siya a lokaci guda

πŸ‘‰ Wannan alama ce ta fake demand.

Step 3: Tarihin Dev

Wasu Devs suna da suna:

  • Sun taba kai coins zuwa Raydium
  • Ko kuma suna da tarihin scam

πŸ‘‰ Yin bincike yana da matuΖ™ar muhimmanci.

Me Yasa Pump.fun Yake Jan Hankali?

Babban dalili: Multipliers

πŸ‘‰ Zaka iya:

  • Saka $10
  • Ya koma $1,000 cikin mintuna

Wannan saurin riba ne ke jan hankalin mutane da yawa.

Amma:

⚠ Kamar yadda ake saurin samun kudi, haka ake saurin rasa su.

Gaskiyar Kasuwa

Pump.fun ba wasa bane.

  • Yana bukatar saurin yanke shawara
  • Yana bukatar ilimi da bincike
  • Yana da hadari mai yawa

πŸ‘‰ Kada ka taba saka kudin da ba zaka iya jure rashinsa ba.

Kammalawa

Pump.fun ya bude Ζ™ofa ga kowa a Web3 amma tare da wannan dama, akwai haΙ—ari.

Nasara a wannan dandali tana bukatar:

  • Fahimta
  • Bincike
  • Da kuma discipline

A darasi na gaba, zamu duba yadda ake amfani da tools kamar DEX Screener da Birdeye domin gano coins masu tasowa da kuma yadda ake tsara buy/sell strategy.


Rubuta  Presido