Gabatarwa
Pump.fun wani dandamali ne da aka gina a kan Solana (kuma yanzu har da Ethereum da Base), wanda ya sauya yadda ake kirkirar memecoins a Web3.
A baya, kirkirar coin yana bukatar:
- Ilimin coding
- Ko kuma babban liquidity
Amma yanzu, Pump.fun ya sauΖaΖa komai kowa zai iya kirkirar coin da kusan $2 kacal.
Yadda Pump.fun Yake Aiki
Babban manufar dandamalin ita ce βFair Launchβ wato kowa yana farawa daga mataki daya.
Ga yadda tsarin yake:
- Coin yana farawa da Ζananan market cap (~$5,000)
- Idan mutane suka ci gaba da siya, darajar tana tashi
- Da zarar ta kai kusan $69,000, ana kai liquidity zuwa Raydium
- Sannan a burn liquidity domin Ζara tsaro
π Wannan tsarin yana rage damfara na farko, amma ba ya kawar da haΙari gaba Ιaya.
Abubuwan Da Ya Kamata Ka Duba Kafin Saka Kudi
1. Branding (Hoto da Suna)
Coin mai kyau yawanci yana da:
- Hoto mai inganci
- Suna mai jan hankali ko trending
π Idan ka ga hoto mara kyau ko suna mara maβana yi hattara.
2. Social Links (Community)
Duba ko coin yana da:
- Telegram
- X (Twitter)
π Shiga ka gani:
- Shin mutane na gaske ne?
- Ko bots ne kawai?
3. Dev Holdings
Duba βHoldersβ:
- Idan Dev yana da fiye da 10%, akwai haΙarin dump
- Coin mai kyau yana da rabon mallaka mai kyau
4. Comment Section
Karanta raβayoyin mutane:
- Shin ana zargin Dev da damfara?
- Shin akwai gargadi daga wasu users?
π Wannan na iya ceton ka daga asara.
Yadda Ake Gane Rug Pull (Damfara)
Step 1: Dev Sell
Idan Dev yana sayarwa tun da wuri: π Alamar rashin tabbas ko shirin guduwa.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Step 2: Bundled Launch
Masu damfara na amfani da bots:
- Wallets da yawa (20β50)
- Suna siya a lokaci guda
π Wannan alama ce ta fake demand.
Step 3: Tarihin Dev
Wasu Devs suna da suna:
- Sun taba kai coins zuwa Raydium
- Ko kuma suna da tarihin scam
π Yin bincike yana da matuΖar muhimmanci.
Me Yasa Pump.fun Yake Jan Hankali?
Babban dalili: Multipliers
π Zaka iya:
- Saka $10
- Ya koma $1,000 cikin mintuna
Wannan saurin riba ne ke jan hankalin mutane da yawa.
Amma:
β Kamar yadda ake saurin samun kudi, haka ake saurin rasa su.
Gaskiyar Kasuwa
Pump.fun ba wasa bane.
- Yana bukatar saurin yanke shawara
- Yana bukatar ilimi da bincike
- Yana da hadari mai yawa
π Kada ka taba saka kudin da ba zaka iya jure rashinsa ba.
Kammalawa
Pump.fun ya bude Ζofa ga kowa a Web3 amma tare da wannan dama, akwai haΙari.
Nasara a wannan dandali tana bukatar:
- Fahimta
- Bincike
- Da kuma discipline
A darasi na gaba, zamu duba yadda ake amfani da tools kamar DEX Screener da Birdeye domin gano coins masu tasowa da kuma yadda ake tsara buy/sell strategy.
Rubuta Presido