Lokacin da aka kirkiro Bitcoin a shekarar 2009, mutane da yawa sun dauka cewa anonymous ne. Amma ba haka ba ne. Duk transaction da kayi a public blockchain ana iya gani daga ko’ina a duniya har abada. Wallet address dinka, adadin crypto dinka, inda ka tura shi, da inda ya fito duk ana rubuta su a permanent public ledger. A baya wannan bai damu mutane sosai ba. Crypto karami ne a lokacin. Babu wanda ya damu sosai da shi.

Yanzu komai ya canza gaba daya.

Yanzu Duniya Tana Kallo

Gwamnatoci, hukumomin haraji, blockchain analytics companies, harma da masu laifi yanzu suna sa ido sosai akan crypto transactions. Companies kamar Chainalysis da Elliptic ana biyansu miliyoyin daloli domin bibiyar motsin crypto a madadin hukumomi da jami’an tsaro. Abin da kayi da crypto naka yau za a iya tracking, analysis, sannan wata rana a yi amfani da shi akanka.

Wannan ba conspiracy theory ba ne. Wannan shi ne gaskiyar duniyar crypto yanzu.

Wallet Address Naka Kamar Bank Statement Ne β€” A Bude Ga Kowa

Kayi tunani idan duk abin dake shiga da fita daga account dinka yana bayyane ga kowa a internet. Wannan kusan shi ne abin da ke faruwa idan kana amfani da public blockchain ba tare da privacy ba.

Da zarar wani ya san wallet address naka ta hanyar transaction, donation, ko ma public post zai iya ganin tarihin kudinka gaba daya da ke hade da wannan address din. Adadin crypto dinka. Inda ya fito. Inda ka tura shi. Idan wannan bayanin ya shiga hannun da bai dace ba, yana da hadari sosai.

Privacy Ba Domin Boye Laifi Ba Ne

Wannan shi ne hujjar da gwamnatoci suka fi amfani da ita cewa duk wanda yake son financial privacy yana da abin da yake boyewa. Amma idan haka ne, ai banki ma ya kamata ya rika wallafa albashinka da duk yadda kake kashe kudi a fili.

Privacy hakki ne na dan Adam. β€˜Yan kasuwa suna bukatarsa domin kare bayanan kasuwancinsu. Activists a wasu kasashe suna bukatarsa domin rayuwarsu. Talakawa kuma suna bukatarsa domin kare kansu daga scammers, barayi, da kuma wuce gona da iri wajen sa ido. Hare-haren wrench a Faransa da muka tattauna a baya? Wadancan masu laifi sun gano targets dinsu ne ta hanyar public on-chain data da social media. Privacy zai iya kare su.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Abin Da Zaka Iya Yi Domin Kare Privacy Naka

Yi amfani da privacy-focused tools. Wallets kamar Wasabi Wallet suna da CoinJoin wata hanya dake hada transaction dinka da na wasu domin tracking ya yi wahala. Monero kuma cryptocurrency ne da aka gina gaba daya akan privacy, inda transactions suke boye automatically.

Kada ka rika sake amfani da wallet address daya. Duk lokacin da zaka karbi crypto, yi amfani da sabon address. Yawancin modern wallets suna yin haka automatically. Sake amfani da address yana sa tracking ya zama mai sauki sosai.

Ka kula da KYC exchanges. Lokacin da kayi verification a exchange, wannan exchange din ya hada ainihin identity naka da crypto activity naka har abada. Yi amfani da KYC exchanges idan ya zama dole kawai, kuma ka fahimci abin da kake rasawa ta bangaren privacy.

Kada ka cika posting a social media. Kamar yadda muka fada a article din tsaro nuna holdings dinka, profits, ko transactions a fili yana daya daga cikin hanyoyi mafi sauri na mayar da kai target.

Karshe

Crypto ya baiwa duniya financial freedom. Amma freedom ba tare da privacy ba bai cika ba. Blockchain yana da karfi amma kuma yana da transparency da yawancin users basu gane sosai ba lokacin da suka fara amfani da shi. Ka dauki privacy dinka da muhimmanci. Ba saboda kana da abin boyewa ba amma saboda rayuwar kudinka taka ce, ba ruwan kowa ba ne.


Wannan rubutu don ilimi ne kawai, ba shawarar saka jari ba.