Idan kana bibiyar wannan kasuwar da kyau, tabbas ka saba da ganin yadda ake fito da guguwa iri-iri. Yau zaka samu ana maganar AI coins, gobe a tsallake kan RWA, jibi kuma a dawo kan memecoins. Wadannan labarai da ke yawo a kasuwa, su muke kira narratives. Ko shakka babu suna da dadi a kunne, amma ga wata gaskiya guda daya: yawancinsu tarkon kwashe wa yanbaiwa kuΙi ne.
Idan kana son ka dore a harkar nan kuma ka daina asara, dole ne ka bar bin hayaniyar dandalin X, Facebook ko Telegram, ka dawo ga asalin abin da ke juya kasuwar, wato Market Structure (alkibla da gaskiyar motsin farashi).
Yadda Ake Yaudararku Da Labaran Karya
Wadannan labaran da ke tashe a kowane lokaci, makami ne da manyan βyan kasuwa (whales) ke amfani da su wajen rura wutar tsoron kada a bar mutum a baya (FOMO). Tsarin shi ne, za a ru-ruta labarin gaba daya sai duniyar crypto ta dauka. Hakan zai sanyawa mutane azamar fara rugawa suna sayen abu babu lissafi.
Matsalar ita ce, labarai suna da saurin tsufa. Abin da kowa ke rububi a kai a wannan makon, zai iya zama tsohon yayi a mako mai zuwa. Kuma a mafi yawan lokuta, kafin labarin ya zo kunnenka har kayi tunanin investing, manyan mutane sun riga sun gama saye tun yana kasa, suna jiran shigowarka ne kawai su zuba maka kaya a ka, su fita da ribarsu.
Gaskiya Guda Ζaya
Kasuwa ba ta tashi ko sauka don kawai an fadi magana mai dadi ba. Tana tafiya ne a kan fafatawa ta gaskiya (Demand and Supply) tsakanin masu saye da masu sayarwa. Wannan fafatawar ita ce ke zana ainihin hoton da muke gani a jikin allon chart.
WaΙanda suka fahimci kasuwar basayin hanzari ga kowane labari, suna kallon inda ainihin activities na gaskiya ke gudana ne ta wadannan hanyoyin:
Support & Resistance: Wadannan sune matakan farashi na gaskiya inda masu saye ko masu yarwa suke dako. Idan ba'a samu shigar kuΙi na gaske ba (Volume), tofa babu wani labarin da zai sanya farashin wannan assets ya tashi komai dadinsa har takai yayi breaking wadannan matakan kariyar
Trend: Idan kasuwa gaba dayanta tana cikin yanayin faduwa (bear market), ko da za a fito da labarin al'ajabi, farashi ba zai iya yin wani dogon tashi ba. Saboda alkiblar kasuwar ya saba da abinda yake faruwa.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Sell The News
Akwai wata shahrarriyar magana da tsofaffin harkar nan suka sani: "Buy The Rumour Sell The News". Koda yake labari yanada muhimmanci a kasuwar crypto amma shi kaΙai bazai zama abun dogaro koda yaushe ba. Idan ka iya karanta motsin farashi, za ka ga cewa kasuwar ta riga ta kammala shirin yin sama ko kasa tun kafin ma tashoshin labarai su wallafa abin da ke faruwa.
Labari kamar mai ne kawai da ake zuba wa mota; ba shi ne ke tuka motar ba, alkiblar kasuwa ce ke tuka ta. Idan kasuwa ta shirya tashi, labari mai kyau zai sa ta hanzari da sauri. Haza zalika idan kuma ta nuna faduwa, kyawun labari ba zai hana yiwuwar hakanba.
Yadda Zaka Daina Bin RuΙani
Idan kana son ka daina zama abincin tsofaffin kuraye a wannan kasuwar, ga abunda zakayi:
Koyi karanta motsin farashi da kanka: Kar ka zama mai jiran abin da wani zai ce maka. Yana da kyau ka karanci yadda ake gano lokacin da kasuwa ta sauya taku.
Kiyaye jarinka: Idan ka fahimci inda kasuwa ta dosa, za ka san daidai inda ya kamata ka tsayar da asararka idan abubuwa suka tabarbare.
Labarai suna da dadi kuma suna sa kasuwa ta yi dumi, amma alkiblar kasuwa ita ce taswirar da ke nuna gaskiyar abinda yake faruwa. Duk wanda ya gina dabarunsa a kan bin guguwar labarai kawai, to kuwa yayi kama da mai gina gida ne a kan yashi.
Idan ka san yadda kake karanta kasuwa da kanka, za ka daina firgita lokacin da aka baza labaran tsoratarwa (FUD), kuma za ka daina rawar jiki wajen sayen kaya da tsada lokacin da kowa ke murna. Mayar da hankali ga abin da farashi yake yi, ka rage sauraron abin da mutane ke fada.