Najeriya na daga cikin manyan kasuwannin crypto a duniya. Yayin da naira ke fuskantar matsin lamba kuma matasa da dama ke neman hanyoyin bunkasa kudinsu, cryptocurrency ya zama babban zabin saka jari ga miliyoyin mutane. Amma tare da wannan hanzari, akwai manyan kura-kurai β kura-kurai dake sa mutane su rasa kudinsu a kowace rana.
Ko kaji labarin crypto daga aboki, ko kaga wani yana nuna ribarsa a Twitter, ko kuma ka gaji da yadda hauhawar farashi ke cin kudinka β wannan rubutu naka ne. Zamu bayyana manyan kura-kurai 3 mafi hadari da sabbin masu amfani da crypto a Najeriya keyi yanzu, kuma mafi muhimmanci, yadda za ka kauce musu.
Wadannan ba kirkirarren labari bane. Yan Najeriya na gaske suna rasa kudinsu na gaske saboda wadannan kura-kurai guda uku β a yanzu.
Kuskure na 1: Fadawa tarkon βTabbatacciyar Ribaβ
Mu fara da babba. Kowane mako a Najeriya, sabbin kungiyoyin saka jari suna bayyana a WhatsApp, Telegram, da Instagram suna maka alkawarin riba 50%, 100%, har ma 300% cikin βyan kwanaki. βKa turo BTC ko USDT kawai, za mu ninka maka kudinka.β Ka taba ji ko?
Wannan shine Ponzi scheme. Kowane lokaci. Babu wani halal din saka jari na crypto da ke bada tabbacin riba. Idan wani yayi maka alkawarin riba tabbatacciya, yana maka karya kai tsaye.
Wadannan tsare-tsare suna amfani da tsohuwar dabara β suna biyan wadanda suka fara da kudin sabbin masu shiga, suna gina hayaniya, sannan su bace idan kudin ya kare. Dubban βyan Najeriya sun rasa ajiyarsu, kudin makaranta, har ma kudin da suka aro saboda wadannan masu damfara.
Abu mafi muni? Wadanda ke yada wadannan tsare-tsare sau da yawa abokanka ne, βyan uwa, ko mutanen da kake girmamawa β wadanda aka biya su da wuri kuma suna ganin yana aiki. Su ma victims ne. Amma basu sani ba tukuna.
Magani: Kayi amfani da exchanges masu sahihanci kamar Binance, Gate.io, koCoinbase. Ka sayi crypto na gaske ka rike shi da kanka. Babu wanda zai βyi trading a madadinkaβ ya baka riba tabbatacciya β koda kuwa kwararre ne.
Kuskure na 2: Rashin Tsaron Wallet β Sannan a rasa komai
Ga abin da ke faruwa kullum a Najeriya: mutum ya sayi crypto karo na farko, ya ajiye shi a exchange, amma bai taba kokarin fahimtar wallet, seed phrase, ko private keys ba. Sai daya daga cikin wadannan abubuwa ya faru:
1. Anyi hakin exchange din ko an rufe shi
2. Ya danna link na phishing, aka kwashe masa komai
3. Ya manta password dinsa, ya rasa access gaba daya
βBa naka key ba, ba naka coin ba.β Wannan yana daga cikin dokoki mafi muhimmanci a crypto β amma mafi yawan mutane suna watsi da shi.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Masu damfara a Najeriya sun kara wayo sosai. Wasu suna fake customer care a social media suna cewa suna taimaka maka kayi βverifyβ account. Wasu apps suna kama da Binance ko Trust Wallet amma na karya ne β suna satar seed phrase dinka da zarar ka shigar. Kuskure daya kawai na iya shafe watanni na ajiyar ka.
Seed phrase dinka β kalmomi 12 ko 24 β shi ne mabuΙin wallet dinka gaba daya. Ka rubuta shi a takarda. Kakuma ajiye shi a wuri mai tsaro. Kada ka taba saka shi a wani website ko app. Babu wani kamfani na gaske da zai taba tambayarka shi.
Magani: Yi amfani da hardware wallet (kamar Ledger) idan kudinka sun yi yawa. Rubuta seed phrase a takarda β kada ka dauki screenshot. ka kunna 2FA a dukkan accounts dinka. Idan wani ya tambaye ka seed phrase dinka, to damfara ce β babu gardama.
Kuskure na 3: Saka kudin da ba zaka iya rasa rasawa ba
Wannan yana da zafi saboda yana fitowa daga wahala ta gaske. Saboda tsadar rayuwa da faduwar naira, mutane da yawa suna shiga crypto ba a matsayin saka jari ba β amma a matsayin mafita ta karshe. Wannan ne inda matsalar ke farawa.
Mutane suna karbar bashi su sayi Bitcoin. Suna sayar da dabbobi ko fili su saka a altcoins da suka ji a intanet. Suna saka kudin makarantar βyaβyansu saboda βsignal ya nuna zai tashi.β Idan kasuwa ta fadi su rasa kudin β kuma a crypto kasuwa tana faduwa sosai β wadannan mutane suna shiga matsanancin hali.
Bitcoin ya taba faduwa sama da kashi 70% daga kololuwar farashinsa a 2022. Altcoins ma sun fadi fiye da haka β wasu har sun koma sifili. Wannan alβada ce a crypto. Idan ba za ka iya jure irin wannan asara ba, bai kamata ka saka wannan kudin ba.
Kasuwar crypto tana daga cikin kasuwanni mafi saurin canzawa a duniya. Harma kwararru suna rasa kudi. Idan kana saka kudin haya, abinci, ko gaggawa β wannan ba saka jari ba ne, caca ce da rayuwarka.
Tunanin da ya dace shi ne: crypto ya zama kudin daka ware bayan ka riga ka kula da bukatunka, emergency fund, da sauran ajiyar ka. Fara da kadan. Kanemi ilimi da farko. Kabar riba ta zo daga baya.
Magani: Kada ka taba saka fiye da kashi 5β10% na ajiyarka a crypto idan kana farawa. Gina emergency fund da farko. Yi dollar-cost averaging β ka rika saye kadan-kadan a hankali maimakon saka komai lokaci guda. Hakuri ya fi gaggawa.
Kalmar Karshe
Damar dake cikin crypto gaskiya ce β amma ga wadanda suka kusance ta da ilimi, hakuri, da taka tsantsan. Ka tura wannan rubutu da wanda kake ganin yana bukatar karantawa a yau.
Wannan rubutu don ilimi ne kawai, ba shawarar saka jari ba. Ka yi bincike da kanka kafin ka saka jari.