A cikin 'yan kwanakin nan, da yawa daga cikin masu fadi-tashi a fannin crypto sun tsinci kansu cikin tsaka-mai-wuyar da ba su gane mata madafa ba. Kana zaune kana kallon taswirar kasuwa (charts), sai kawai ka ga farashi ya rikiceβko dai ya lula samaniya ko kuma yayi mummunar faduwaβalhali babu wani labari na a-zo-a-gani da ya faru a duniya. Sai dai yan kasuwar ta crypto suna yiwa kansu wannan tambayar: shin menene wanda ba dai-dai ba a kasuwar nan?
Amsar ba ta da dadi, amma ita ce gaskiyar lamari: Kasuwa ba tafiya take yi da kanta ba. Akwai wadanda ke juya akalarta.
Idan kai gama garin dan kasuwa ne (Retail Trader), yana da sauki ka fada tarkon tunanin cewa farashin Bitcoin ko sauran crypto yana tashi ne ko faduwa saboda saye da sayarwa na gaba daya (demand supply based). Sam abin ba haka yake ba. A bayan fage, akwai wasu shafaffu da mai da ke juya akalar kasuwar yadda suka ga dama.
Su Waye Mala'un Kasuwar?
A harkar crypto, ana kiran wadannan mutane ko kungiyoyi da suna Whales (Kuraye) ko kuma Market Makers (Masu Siffanta Kasuwa). Wadannan sun hada da:
Manyan Kamfanonin Zuba Jari: Kungiyoyin da ke rike da biliyoyin daloli a asusunsu.
Kasuwannin Crypto (Exchanges): Wadanda ke ganin duk wani sirri na inda talakawa suka sanya asararsu (Stop Losses) da inda suke fatan samun riba (Take Profit).
Masu Manyan Na'urorin Hakar Crypto: Wadanda ke rike da tarin kuΙaΙen na crypto tun fil azal.
Hanyoyin Wayo da Whales Ke Amfani Dashi
Idan ka taba ganin kasuwa ta ruguje kasa lokaci guda, sannan da zaran ka sayar saboda tsoron kada kudin ya kare, sai ka ga farashin ya sake daka tsalle sama da gudu, to ka sani cewa an yi maka dabarar "Liquidation Hunt" ne
Abunda Yake Faruwa:
Wadannan whales suna amfani da dabarun algorithms na na'ura mai kwakwalwa don karyar da farashi da gangan. Burinsu guda daya ne: su tsorata kananan 'yan kasuwa su jefar da kayansu da araha (Panic Selling). Da zaran kowa ya sayar saboda tsoro, sai su kuma su kwashe kayan da arha, daga nan kuma kasuwa ta harba sama.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
A takaice, ba wai kasuwar ce ke zirga-zirga da kanta ba; an riga an tsara motsin ne don a kwashe abin da ke aljihunka.
Hanyoyi 3 Da Za Ka Kare Kanka
Tun da mun san cewa an riga an tsara wasan ne, ta yaya kai kuma za ka tsira? Ga manyan hanyoyin da kwararru ke amfani da su:
Kada Ka Bi Rudun Tsoro (FOMO & FUD): Idan ka ga farashi yana faduwa da sauri ba tare da wani mummunan labari na gaske ba, kada kayi gaggawar sayarwa. Yawancin lokuta kora ce ake muku don a kwashe muku kaya.
Koyi Karatun Chart na Gaske (Volume and Order Flow): Kada ka dubi layukan farashi kawai. Dubi adadin kudin da ke shiga kasuwa (Volume). Shi ne kadai ba ya karya, domin Whales ba za su iya boye girman kudadensu ba idan sun shiga kasuwa.
Yi Amfani Da "Dollar-Cost Averaging" (DCA): Maimakon ka zuba kudadenka gaba daya lokaci guda, kasasu gida-gida kana saye kadan-kadan. Wannan yana rage maka tasirin duk wani juyi na bogi da za a yi wa kasuwar.
Kasuwar crypto ba fagen raba kyauta ba ne; fili ne na gwada kwakwalwa da juriya. Ranar da ka daina kallon chart a matsayin lambobi kawai, ka fara kallonsa a matsayin fagen fama tsakanin manyan kadoji da kananan kifi, a nan ne za ka fara gane inda kalar ribarka take.
Kasuwa ba ta motsi da kanta, juyata ake yi. Amma idan ka san hanyar da manyan whales suka nufa, sai ka ninkaya tare da su maimakon su hadiye ka.
Me kuke tunani game da wannan boyayyen shiri na juyar da kasuwa? Ko kun taba fadawa wann
an tarkon? Ku sanya mana ra'ayoyin ku