Yan kasuwar crypto sun sake shiga cikin wani yanayi na rashin tabbas. Bayan watanni na tashin komaΙa da kuma dawowar kwarin gwiwar yan kasuwar, yanzu tambayar da ake yawan yi ita ce: Shin ana tsammanin wani crash ne nan gaba?
Amsar wannan tambaya ba ta da sauΖi. Kasuwar crypto ba ta taΙa bayarda tabbaci. A tarihi, ta saba hawa cikin sauri, sannan kuma a samu correction kafin ta sake farfadowa. Wannan shi ne dalilin da ya sa Ζwararrun masu saka hannun jari ke kallon irin waΙannan lokuta da idon basira, ba da tsoro ba.
Me Ya Sa Ake Zaman Dar-dar?
A cikin 'yan makonnin nan, abubuwa da dama sun fara nuna cewa kasuwar tana cikin wani yanayi mai haΙari.
Na farko akwai matsin lambar tattalin arzikin duniya. Har yanzu babban bankin Amurka yana ci gaba da tsaurara manufofin kuΙi domin rage hauhawar farashi. Idan ruwa ya yi tsada, yawanci masu zuba jari kan rage saka kuΙi a kadarori masu haΙari kamar crypto.
Na biyu kuma, an ga wasu manyan masu zuba jari suna cire kuΙinsu daga Bitcoin ETF da Ethereum ETF. Wannan ya rage Ζarfin saye a kasuwa, lamarin da ke sanyaya gwiwar yan kasuwar.
A lokaci guda kuma, ana ganin wani Ιangare na manyan kuΙaΙen duniya yana komawa zuwa kamfanonin Artificial Intelligence (AI), wanda hakan ya rage yawan kuΙin da ke shiga crypto.
Shin Wannan Yana Nufin Kasuwa Za Ta Rushe?
Ba lallai ba ne.
A kasuwar crypto akwai babban bambanci tsakanin market correction da market crash.
Correction na nufin farashi ya sauka domin kasuwa ta huce bayan dogon hawa. Wannan abu ne da ake yawan gani a kusan kowace bull market.
Crash kuwa yana nufin faduwa mai tsanani wadda ke lalata kwarin gwiwar kasuwa gaba Ιaya.
A halin yanzu, masana sun kasu gida biyu. Wasu na ganin idan Bitcoin ya kasa bijirewa manyan matakan support, to za a iya sake ganin wata babbar faduwa. Amma wasu kuma suna ganin mafi yawan labarai marasa kyau sun riga sun gama tasiri, kuma kasuwar na iya samun zarafin farfadowa cikin sauri.
Abubuwan Da Ya Kamata Yan Kiripto Su Sa Ido A Kai
Maimakon tsoron kowace jita-jita, ya fi dacewa a dinga bibiyar abubuwan da ke motsa kasuwa.
Idan Bitcoin ya kasa jure manyan kinshikan support, hakan na iya Ζara jawo firgici.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Idan ETF sun ci gaba da fuskantar ficewar kuΙi, za'a iya cigaba da fuskantar selling pressure.
Manufofinsa hukumar FED, idan aka cigaba da samu tsauraran matakai hakan na iya rage sha'awar masu saka jari ga kadarori masu haΙari.
Sai dai idan aka ga kuΙi sun fara dawowa ETF, tattalin arziki ya fara sassautawa, sannan Bitcoin ya sake kafa Ζarfi, hakan zai zama alamar cewa kasuwar ta halin farfaΙowa.
Market Crash Sabo Abu Ne?
Tun bayan kafuwar Bitcoin, kasuwar crypto ta sha faduwa sau da dama.
An ga faduwar shekarar 2018.
An ga rugujewar kasuwa bayan rushewar Terra.
An ga rikicin FTX.
Duk waΙannan lokuta sun haifar da babban tsoro. Amma bayan kowace irin faduwa, kasuwar ta sake farfadowa, har ta kafa sabbin tarihi.
Wannan ba yana nufin tarihin zai maimaita kansa ba, amma yana nuna cewa kasuwar crypto tana da yanayin zagaye. Tsoro da kwaΙayi suna ci gaba da sauyawa a koda yaushe.
A yau, babu wanda zai iya tabbatar da cewa wata babbar faduwar kasuwar crypto tana nan tafe. Amma abin da ya tabbata shi ne kasuwar tana cikin wani yanayi mai cike da rashin tabbas.
Masu zuba jari masu hikima ba sa yanke hukunci saboda tsoro ko jita-jita. Suna kallon bayanai, suna lura da yanayin tattalin arziki, suna kuma gudanar da kasadarsu cikin tsari.
Ko kasuwa za ta sake faΙuwa ko kuma za ta fara sabon babin farfadowa, abu Ιaya ya tabbata: waΙanda suka fi samun nasara ba su ne masu saurin firgita ba, su ne masu haΖuri, binc
ike da kuma bin tsarin investment na hikima da ilimi.