Kasuwar crypto na ci gaba da jan hankalin masu zuba jari a duniya. A cikin kwanakin nan, ana ta tattaunawa kan wani hasashe da ke cewa babbar faduwar kasuwa (crashed) na iya fara bayyana daga watan Satumbar 2026.
Sai dai babban abin da ya kamata a fahimta shi ne cewa wannan hasashe ne, ba tabbacin abin da zai faru ba. Kasuwar crypto ta shahara wajen yin abubuwan da ba a zata ba, kuma sau da dama ta kanyi hannun riga da hasashen masana.
Me Ya Sa Wasu Ke Hasashen Satumba?
Masu nazarin kasuwa suna danganta wannan hasashe da wasu muhimman abubuwa:
Duk lokacin da a kace kasuwa tayi tashin gwauron zabi (Bull Market), akan fuskanci (Correction) ko kuma yanayin Bear. Musamman idan kasuwa ta zama bullish wannan Q3 Ιin.
Sauye-sauyen manufofin tattalin arziki kamar Ζarin kuΙin ruwa, hauhawar farashi (Inflation), da matakan manyan bankunan duniya kai tsaye yakan shafi kasuwar crypto.
A irin wannan lokacin investors sukan riΖe kuΙaΙen su don ganin sahihancin alkiblar kasuwa.
Shin Lallai Faduwar Za Ta Fara A Satumba?
Amsar ita ce ba wanda zai iya tabbatar da hakan.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Kasuwar crypto ba ta da tabbataccen jadawalin da take bi. Labarai masu Ζarfi, sababbin dokoki, karΙuwar fasahar blockchain, ko kuma shigar manyan kamfanoni cikin kasuwa na iya sauya alkiblar farashi cikin Ιan lokaci.
Saboda haka, kuskure ne mai zuba jari yace zai yanke hukunci bisa hasashe kaΙai.
Darasi Daga Tarihi
A tarihin crypto, ba bakon abu bane faduwar kasuwa a watan Satumba, abun har yanaso ya zama kamar wata al'ada. Don haka wajibi ne yan kasuwa suyi shirin ko ta kwana.
Idan muka kalli yanayin ta babbar fuska zamu fahimci cewa kasuwar crypto tana tafiya ne cikin zagaye (Market Cycles). Don haka, fahimtar inda kasuwa take a wannan zagaye ya fi muhimmanci fiye da tsoron wata rana ko wani wata.
Hasashen cewa za'a samu market crash a watan Satumbar 2026 na daga cikin ra'ayoyin da ake tattaunawa a tsakanin masu nazarin kasuwa. Amma har zuwa yanzu, babu wata hujja da ke tabbatar da cewa hakan dole ne ya faru.
Dole ne mu yan kiripto mu kasance masu lura da bayanan kasuwa, sannan mu dinga taka tsan-tsan Ζwarai wajen sarrafa labaran kasuwa, kuma kada mu yanke hukunci bisa jita-jita ko hasashe kawai.
A kasuwar crypto, bayanai, bincike da kuma sarrafa kanu sune manyan makaman Ιan kasuwa.