Duniya tayi imani cewa (Cryptocurrency) masalaha ce ga "makomar kudi," amma abin mamaki shi ne, duk da wannan hasashen, kusan kashi 80% na masu shiga harkar suna tashi a matsayin masu asara. Tambayar dake bukatar amsa a nan ita ce: Me ya sa hakan ke faruwa?
Gaskiyar ita ce, yawancin mutane suna shiga Crypto ne da tunanin samun kudi dare daya (Get-rich-quick), ba tare da fahimtar ainihin amfanin wannan fasahar ba. Domin ka zama cikin kashi 20% da ke samun nasara, dole ne ka daina kallon Crypto a matsayin sha yanzu magani yanzu, ka fara kallonsa a matsayin juyin-juya hali na tattalin arziki.
1. Utility Maimakon Hype
Mafi akasarin mutane suna siyan Coin ne saboda sun ji ana yayinsa. Amma kwararru suna duba me Coin din yake yi? Shin yana magance matsalar tura kudi ne? Ko kuma yana samar da tsaro ne ga bayanan sirri?
Fahimta: Idan Coin ba shi da ainihin aikin da yake yi (Real-world use case), to darajarsa tamkar gadar zare ce
2. Illar "FOMO"
Tsoron kar a bar ka a baya (Fear of Missing Out) shi ne babban makamin da yake cinye kudaden kananan masu zuba jari. Lokacin da kake ganin kowa yana maganar wani Coin ya tashi, a lokacin ne ya kamata ka kiyaye, domin yawanci a lokacin ne manyan yan kasuwa (Whales) suke shirin sayarwa don su fita da riba.
3. Rashin Hakuri Da Tsare-tsare
Crypto ba tseren gudu ba ne na mita dari; tafiya ce ta dogon zango. Kwararren mai zuba jari shi ne wanda:
Yake da tsarin Risk Management (Sanin adadin abin da zai iya rasawa).
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Yake bin diddigin labaran duniya da tasirinsu ga kasuwa.
Yake bambanta tsakanin "Trading" (cinikayya na yau da kullum) da kuma "Investing" (zuba jari na dogon lokaci).
βA cikin duniyar Crypto, ilimi shi ne babban jarinka, sannan hakuri shi ne ribarka.β
Ina Aka Sa Gaba?
Don masu karatu su amfana, dole ne mu fahimci cewa Crypto ya wuce kawai siye da sayarwa. Muna maganar:
DeFi (Decentralized Finance): Samun rancen kudi ko ajiyar banki ba tare da bukatar bankin kansa ba.
Smart Contracts: Yarjejeniya ta fasaha wacce babu bukatar lauya ko wani shaida tsakanin mutum biyu.
Cross-Border Payments: Tura kudi zuwa kowace uwa duniya a cikin dakiku kalilan ba tare da tsadar harajin bankuna ba.
Idan kana son dorewa a wannan harkar, karka dan abi Yarima asha kida. Ka tsaya ka koyi yadda Blockchain yake aiki. Ka daina kallon jadawalin farashi (Charts) kawai, ka fara karanta abin da ake kira Whitepaper na duk wani project da kake son sanya kudi.
Nasara a Crypto ba ta saβa ba ce; nasara ce ta bincike, lura, da kuma juriya.
Wane mataki kake ganin shi ne mafi kalubale ga sabbin masu zuba jari a yau? Shin rashin ilimi ne ko kuwa kwadayi? Ku fada mana ra'ayinku