Kasuwar cryptocurrency cike take da damarmaki na arziki, amma kuma tana cike da barayi da ’yan damfara masu baki da shuni a dandalin yanar gizo. Idan kana harkar crypto, tabbas ka sha jin labaran mutanen da aka kwashe musu daruruwan daloli cikin kankanen lokaci. Tambayar da kowa ke yi ita ce: Yaya zan kare kadarorina ta yadda babu wani barawo da zai iya taba su?

Gaskiyar magana ita ce, hanya guda daya tilas mafi tsaro don ajiye crypto dinka ita ce amfani da Cold Wallet (Wajen Ajiyar Kudi Mafi Tsaro)

A cikin wannan rahoton, za mu fasa muku kwan gaskiya kan dalilin da ya sa wannan ita ce garkuwarka ta karshe, da kuma yadda zaka kare kanka daga asarar dukiya.


HATSARIN "HOT WALLETS" 

Mafi yawan mutane suna ajiye crypton su ne a manhajoji kamar Trust Wallet, MetaMask, ko kuma a manyan dandamalai na canjin kudi (Exchanges) kamar Binance, Bybit, da KuCoin. Ana kiran wadannan da Hot Wallets.

Wadannan dandamalai suna da dadi da saurin amfani, amma suna da babban hadari:

Kullum Suna Cikin Intanet: Domin suna da alaka da intanet, ’yan kutse (Hackers) na iya lalubo hanyar shiga wayarka ko kwamfutarka ta hanyar kwayoyin cutar gizo (viruses/malware).

Ba Ka Da Cikakken Iko: Idan kana ajiye kudi a Exchange, akwai wata tsohuwar magana a duniyar crypto da ke cewa: β€œNot your keys, not your crypto” (Idan ba kai ke da lambobin sirri ba, kudin ba naka ba ne). Idan dandalin ya durkushe ko aka yi musu kutse, kudinka sun tafi kenan.


Menene Cold Wallet, Kuma Me Ya Sa Shi Ne Mafi Tsaro?

Cold Wallet (wanda aka fi sani da Hardware Wallet) wata na'ura ce tabbatacciyaβ€”kamar USB drive ko hard drive na musammanβ€”wacce aka kera ta musamman don ajiye lambobin sirrinka na crypto (Private Keys) bata tare da intanet.

Shahararrun kamfanonin da ke kera wadannan na'urori sun hada da Ledger da Trezor.


Dalilin Da Ya Sa Shi Ne Mafi Tsaro:

Yanke Alaka da Intanet: Tunda na'urar ba ta jonu da yanar gizo ba, babu wani dan kutse (hacker) a duniya, ko da sun fito daga Rasha ko Amurka, da zai iya shiga cikinta ya sace kudin kalilan.

Kariya Daga Cutar Kwamfuta: Ko da kwamfutarka ko wayarka tana da virus, ba zai iya taba abin da ke cikin Cold Wallet dinka ba.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Kai Ne Bankin Kanka: Kai kadai ke da iko da kudadenka. Babu wani kamfani da zai iya kulle maka asusu ko ya hana ka cire kudi.


Sharuddan Amfani Da Cold Wallet 

Duk da cewa Cold Wallet shi ne kololuwar tsaro, yana bukatar taka-tsantsan daga gare ka. Lokacin da ka sayi na'urar, za a ba ka wasu kalmomin sirri guda 12 zuwa 24 (wato Seed Phrase ko Recovery Phrase).

Wannan shi ne ainihin rayuwar crypton ka. Ga yadda za ka kare shi:

Kada Ka Taba Sanya Shi A Intanet: Kada ka dauki hotonsa da waya, kada ka tura shi a email, kuma kada ka rubuta shi a notes na wayarka.

Rubuta Shi A Takarda: Rubuta shi da alkalami a jikin takarda ko karfe, sannan ka boye shi a wurin da babu wanda ya sani, nisa da ruwa ko wuta.

Idan Suka Bace, Kudinka Sun Bace: Idan ka rasa wadannan kalmomi 24, ko da na'urarka tana hannunka, ka rasa kudinka har abada.


Matakan Kariya 

Idan da gaske kake kana son kare dukiyarka ta crypto don nan gaba, ga abin da yakamata ka yi yanzu:

Raba Kudinka Gida Biyu: Kudin da kake kasuwanci da su na yau da kullum (Trading) zaka iya barinsu a Hot Wallet ko Exchange. Amma babban jarinka na dogon lokaci (Long-term investment), tura shi zuwa Cold Wallet.

Sayi Na'ura Daga Asalin Kamfani: Idan zaka sayi Ledger ko Trezor, kada ka taba saya a wajen taron mutane ko shafin da ba a amince da shi ba (kamar dillalan gida). Sayi kai tsaye daga shafin kamfanin na asali domin guje wa na'ururar da aka riga aka yi wa lalata 


A duniyar crypto, kai ne manajan bankin kanka. Tsaron kudinka yana farawa ne da kare asirinka. Kada ka jira sai ranar da za a wayi gari an kwashe maka dukiya sannan ka dauki mataki. Cold Wallet ba dabi'ar almubazzaranci ba ce; tabbatacciyar kariya ce ga gobe dinka.

Shin kun taba amfani da cold wallet?