A matsayinka na mai harkar trading, akwai wani babban kuskure da kusan kowa yake fadowa cikinsa, musamman idan mutum sabon shiga ne: Neman wani tsinannan Indicator da zai rika bashi signal na Buy da Sell duka a matsayin abun dogaro
Traders da yawa suna cika chart dinsu da su RSI, MACD, da Moving Averages, har chart din ma ya rika musu dishi-dishi. Amma gaskiyar magana ita ce: Babu wani Indicator guda daya da zai yi maka aiki a kowane irin sauyin kasuwa. Saboda me? Saboda akwai abinda ake kira, Market Regimes (Alkiblar Kasuwa).
Idan ba ka gano ainihin yanayin da kasuwar ke ciki ba a yanzu, to kowane irin Indicator kake amfani da shi, fake signal kawai zai rika ba ka yana babbake maka account.
Menene Market Regime?
A takaice, Market Regime shine babban yanayin da kasuwa take ciki a wani takamaiman lokaci. Kuma a duniyar crypto, kasuwa ba ta wuce wannan matakan:
Trending Market: Lokacin da farashi ya kama hanya daya da karfi β ko dai yana ta sama (Bullish) ko kuma yana ta daddalawa kasa (Bearish).
Ranging/Choppy Market: Lokacin da kasuwa ba ta da gaba balle baya. Farashin yana ta tangal-tangal ne kawai a tsakanin Support da Resistance.
Abun lura anan: Shi yasa zaka ga Indicator din da ya tara maka kudi lokacin da kasuwa ke Trending, shi ne kuma zai cinye maka dukiyar idan kasuwar ta koma Ranging.
Tarkon Da Ke Cikin Dogaro Da Indicators Kadai
Mafi yawancin Indicators (musamman Oscillators kamar RSI ko Stochastic) an tsara su ne domin su nuna maka lokacin da kasuwa ta yi tsada da yawa (Overbought) ko kuma lokacin da ta taba kasa (Oversold).
Idan kasuwa tana Ranging: Wadannan abubuwan suna da matukar dadi. Idan RSI ta nuna Oversold, ka san zaka iya shiga Long, farashi kuma zai koma sama abinsa.
Amma idan babban Trend ya tashi (Lokacin Bull Run): Anan ne ake gizo ke sakar. Farashin coin zai iya cigaba da yin sama na tsawon makonni, yayin da RSI dinka ke nuna maka Overbought. Idan ka dogara da shi kaki siya domin tunanin sai kasuwar ta fadi nan za'a barka da rike baki saboda already trend din yanada karfi
Kar ka manta, ba kowane Indicators bane suke baka labarin abunda zai faru nan gaba ba; lissafin abinda ya riga ya faru ne kawai suke baka (Lagging).
Me Yasa Fahimtar Yanayin Kasuwa Yakeda Muhimmanci?
Manyan βyan kasuwa na gaske (Whales da Institutional Traders) ba sa fara duba RSI ko MACD idan sun bude chart. Tambayar farko da suke jefawa kansu ita ce: "Wane irin regime kasuwar nan take ciki yanzu?"
Da zaran ka gano hakan, to ka riga ka san wane irin tsari ko Strategy ya kamata ka fitar:
Idan Kasuwar Na Cikin "Trending"
Tsari mai karfi: Kar ka kuskura ka tsaya neman inda kasuwar zata tsaya ta juya. Bi ta kawai a yadda take tafiya (A trend is your friend).
Mafi kyawun abokin aiki: Wannan shine lokacin amfani da Moving Averages (kamar EMA 20/50) domin gano inda farashi ke samun karfi
2. Idan Kasuwar Na Cikin "Ranging"
Salon Masu Wayo: Kar ka kuskura ka bi farashi idan kaga yana breakout da gudu (za ka iya fadawa a tarko). Sayi kaya a kasa (Support), ka sayar a sama (Resistance).
Mafi kyawun abokin aiki: Anan ne RSI da Bollinger Bands ke zama gwal.
Dabarar da Zaka Dinga Amfani
Idan kana son ka fita daga sahun wadanda ke barin kudi a kasuwa koyaushe, canza tunaninka daga kallon "Wanne Indicator zan saka?" komawa zuwa "Wanne Alkibla kasuwa ke ciki?". Ga matakan da zaka bi:
Bude Babban Hoto (Higher Timeframes): Ka duba chart na Daily (D1) ko Weekly (W1) domin ka san ainihin inda aka dosa, kar ka tsaya makale a cikin hayaniyar chart na minti 5 ko 15.
Kalli Volatility (Motsi Da Kwararar Kudi): Idan babu kudi da ke shigowa a kasuwar, zata rika yin ta-tata ne kawai a wuri daya (Ranging). Idan aka saki wani babban labari ko manyan kudi suka shigo, nan da nan zata koma Trending.
Saita Indicators dinka: Su zama masu taya ka tabbatar da abinda ka riga ka gani da idonka ne kawai, ba wai su ne zasu rika yanke maka hukuncin shiga kasuwa ba.
Indicators tamkar kayan aiki ne kawai a akwatin makanike. Ba zaka dauko guduma ba domin ka cire noti (screw). Haka abun yake a kasuwa: Dole ka fara sanin wace matsala ce a gabanka kafin ka san wanne kayan aiki zaka dauko.
Gano Market Regime shi zai nuna maka ainihin kayan aikin da zaka yi amfani da shi. Da zaran ka gane wannan sirrin, dabarunka zasu sauya, kuma zaka daina tsoron duk wani motsi na ba-zata da kasuwar crypto ke yi.
Me ra'ayin ku? Shin kun taba shiga tarkon indicators?