A halin yanzu, kasuwar (Crypto) tana fuskantar guguwar canji mafi girma da ta taba gani a tarihi. Yayin da tsofaffin masu zuba jari da kananan 'yan kasuwa ke murnar ganin yadda manyan hukumomin kudi na duniya (Institutions) ke shigowa cikin harkar, kalilan ne ke hango babban hadarin da ke tafe.

Bincike da hujjoji na nuna cewa, mafi yawan coins din da ke kasuwa a yanzu suna dab da zama tarihi. Kuma lokacin wannan guguwar da muke ciki ya kusa karewa fiye da yadda kowa ke zato.


1. Kaka Gidan Hukumomi (The Institutional Takeover)

A da, kasuwar crypto tana tafiya ne a kan ra'ayin talakawa da kananan 'yan kasuwa (retail investors). Amma a yau, manyan bankuna, kamfanonin sarrafa kudade (Hedge Funds), da masu tace dokoki sun karbe ragamar tafiyar.

Lokacin da wadannan manyan hukumomi suka dauki fagen fama, ba za su zuba kudadensu a kan kowane irin coin ba. Suna neman abubuwa uku kacal:

Tsaro na Shari'a (Regulatory Compliance): Coins din da ke da cikakken goyon bayan doka.

Amfani na Gaske (Real-world Utility): Ayyukan da ke magance matsalolin rayuwa na gaske, ba wai kawai na jita-jita (hype) ba.

Kyakkyawan Tsari (Institutional-grade Infrastructure): Tsarin da bai zama holoko ba sannan bashi da barazanar kutse.

Gaskiya guda Daya: Duk wani coin da bai cika wadannan sharuddan ba, za a bar shi a baya. Wannan shi ne dalilin da ya sa kashi 95% na coins din da ke kasuwa a yanzu za su rasa darajarsu, saboda ba su da abin da wadannan manyan masu kudi ke nema.



2. Mutuwar Zamanin 'Hype' da Memecoins

A shekarun baya, zaka iya siyan coin din da ba shi da wani amfani na gaske (kamar Memecoins ko coins din bogi) ka yi arziki na dare daya saboda kawai ana yayinsa a dandalin X (wanda aka sani da Twitter a da). Wannan zamanin ya kusa karewa.

Lokacin da manyan kudade suka mamaye kasuwa, "hype" yana mutuwa, "kima" (value) kuma tana wanzuwa. Yawancin coins din da ke sharafi a yanzu ba su da tsari mai dorewa (sustainable tokenomics). Idan guguwar ta kada, wadannan coins din za su narke kamar kankara a tsakiyar rana


Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

3. Har Zuwa Yaushe Kake da Damar Hanklta?

Da yawan yan crypto suna tunanin cewa suna da isasshen lokacin don su gyara wasu kusa-kurensu fahimtar su da kasuwa. Wannan babban kuskure ne. Lokacin da za ka gyara dabarunka (positioning) yana gudu da sauri fiye da yadda kowa ke fada a fili.

Idan ba ka raba (portfolio) Ι—inka daga coins masu hadari zuwa ga projects masu inganci (high-utility projects) ba tun yanzu, za ka tsinci kanka a tsaka mai wuya tareda kadarorin da babu wanda zai sake sayensu a nan gaba.


Me Ya Kamata Ka Yi Tun Kafin Lokaci Ya Kure?

Don kada ka kasance a cikin kashi 95% na wadanda ambaliyar za ta tafi da su, ga matakan da kwararru ke ba da shawara ka dauka:


Tace Portfolio Dinka: Zauna ka duba coins dinka daya bayan daya. Shin suna da amfani na gaske ko kuwa tallansu kawai ake yi

Rungumi Coins Masu Kyau (Utility): Mayar da hankali kan projects da ke da alaka da sabbin fasahohi kamar AI, RWA (Real World Assets), da Layer-2 scaling solutions masu karfi.

Kiyaye Dokoki: Zuba jari a Projects da ba su da rigima da hukumomin da ke sa ido kan kudi.


Kasuwar crypto ba mutuwa take yi ba; canzawa take yi na dindindin. Tsohon salon ya wuce, sabon salon kwararru kuma ya dab da karbe iko 

Tambayar da kake bukatar amsa wa kanka yau ita ce: Shin portfolio dinka tana cikin kashi 5% da za su dore, ko tana cikin kashi 95% da za su shiga tsilla-tsilla?

Gyara zama, lokaci ba jiran kowa yake yi ba!