A kasuwannin duniya, akwai wasu abubuwa da suke faruwa a bayan fage waɗanda ba sa bayyana kai tsaye a jadawalin crypto, amma suna iya yin tasiri sosai a kan kasuwar.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan abubuwan shi ne Japanese Yen (JPY).

A farkon watan Agusta 2026, Amurka da Japan sun ɗauki wani mataki da ba kasafai ake ganin irinsa ba: ƙasashen biyu sun shiga tsakani a kasuwar kuɗaɗen waje domin ƙarfafa yen, bayan kuɗin Japan yayi irin karyewar da ba'a taba ganiba tun kimanin shekaru 40 da suka gabata. Wannan shirin haɗin gwiwa ya zama banbara kwai, domin kuwa da jimawa irin hakan bai faruba.

Abunda ƴan kiripto suka fi tambaya shine: ta yaya hakan zai shafi kasuwar tasu?

Amsar tana cikin kalma guda: liquidity — global liquidity, kuɗin da ke yawo a tsarin hada-hada na kasuwancin duniya.


Karyewar Kuɗin Yen 

A ranar da matsin lamba ya kai kololuwa, yen ya kusan kai ¥164 kan dala ɗaya, matakin da ya kasance mafi rauni cikin kusan shekaru arba'in.

Japan ta shiga cikin matsala mai wahala.

A lokaci guda, tana son kuɗinta ya kasance mai ƙarfi domin rage tsadar kayayyakin da take shigowa da su daga waje.

A ɗaya gefen kuma, ƙara yawan kuɗin ruwa cikin sauri na iya ƙara wa gwamnati, kamfanoni da masu karɓar bashi nauyi.

Idan bamu manta ba tun shekarar data gabata Bankin Japan (BOJ) ya riga ya fara barin zamanin kuɗin ruwa mai matuƙar sauƙi. A watan Yunin 2026, BOJ ya sa babban ƙimar ruwa zuwa 1%, kuma wannan shi ne matakin da yake aiki a yanzu.

Duk da hakan kuma, Yen ɗin dai ya ci gaba da fuskantar matsin lamba.

A ranar 3 ga Agusta, Amurka da Japan suka tabbatar da cewa sun gudanar da haɗin gwiwar sayen yen, abin da ya taimaka wajen ɗaga darajar yen daga matakin kusa da ¥164 zuwa kusan ¥155 a kan dala.

Amma daga baya yen ɗin ya sake karyewa, inda ya koma kusan ¥159 kan dala.

Hallau dai kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba.


Me Yasa Amurka Take Ruwa Da Tsaki Akan Faduwar Yen?

A kallon farko, mutum zai iya cewa:

"Japan ce ke da matsalar yen. Me ya sa Amurka za ta damu?"

Yadda tsarin tattalin arzikin duniya ke aiki:

Japan ba ƙaramar ƙasa ba ce a kasuwannin kuɗi na duniya. Tana daga cikin manyan masu riƙe da U.S. Treasuries, wato bashin gwamnatin Amurka.

Saboda haka, idan Japan tana buƙatar kuɗi domin tallafa wa yen, akwai yiwuwar ta sayar da wasu kadarorin da take riƙe da su a waje — ciki har da kadarorin Amurka.

Wannan na iya ƙara matsin lamba a kasuwar Treasury, ya tura bond yields sama, sannan ya ƙara tsadar rancen kuɗi a Amurka.

Wasu manazarta sun bayyana wannan a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka sa Washington ta fi son a samu daidaito a yen maimakon barin matsalar ta ƙara muni. Japan tana riƙe da sama da dala tiriliyan ɗaya a cikin U.S. Treasuries, don haka babban motsi daga Tokyo zai iya shafar kasuwar bashi ta Amurka.

A takaice:

Amurka ba ta shiga tsakani saboda tana son "ceton yen" kawai ba. Tana kuma son kare daidaiton tsarin kuɗin duniya da kuma kasuwar bashin Amurka.

Inda Gizo Ke Saƙa: Yen Carry Trade

Ga masu crypto, wannan shi ne ɓangaren da ya fi dacewa a kula da shi.

Shekaru da dama, Japan ta kasance ƙasa mai ƙarancin interest rate.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Saboda haka, manyan masu zuba jari na iya:

Karɓar bashi da yen saboda ƙarancin kuɗin ruwa.

Sai su sauya yen zuwa dala ko wasu kuɗaɗe.

Daga nan kuma sai su saka kuɗin cikin kadarorin da ke samar da riba mai yawa "irin su crypto".

Hakan yana basu damar samun riba mai yawa daga bambancin kuɗin ruwa " interest rate gap".

Wannan shi ake kira Yen Carry Trade.

Misali mai sauƙi:

Kaine ka karbi rance Yen watakil a zero interest rate, sannan ka saka kuɗin cikin wata kadara da ke samar da riba mai yawa.

Muddin ƙimar Yen bai ƙaru sosai ba, Kanada yiwuwar samun gwagwgwabar riba.

Amma idan akayi rashin sa'a ƙimar Yen ta karu, Hakan zai kawo tsaiko:

Waɗannan investors zasu hanzarta sayar da kadarorinsu domin su dawo da Yen da suka ci bashi. Idan ba haka ba kuwa to ciko ne zai biyo gyartai.

Yunkurin waɗannan investors yana iya haifar da abunda ake kira "Carry-Trade Unwind".

Kuma lokacin da leverage ya yi yawa, wannan na iya zama babban matsin lamba ga kasuwannin duniya.


Shin Yunkurin Amurka Zai Taimaki Crypto Ne?

Ba lallai ba.

A gaskiya, tasirin yana iya zuwa ta hanyoyi biyu.

Na farko: Short-term volatility

Idan intervention ɗin ya sa Yen ya ƙarfafa sosai cikin gajeren lokaci, wasu carry trades na iya fara rufewa.

Wannan na iya haifar da deleveraging a kasuwannin duniya.

Idan hakan ya faru, Bitcoin da altcoins na iya fuskantar matsin lamba.

Na biyu: Long-term liquidity

Amma idan haɗin gwiwar Amurka da Japan ya rage rikicin Forex, ya daidaita bond markets, sannan ya hana tashin hankali mai yawa a kasuwannin duniya, hakan na iya haifar da ɗa mai ido ga risk assets daga baya.

Saboda haka tsoma bakin Amurka ba manuniya ce cewa farashin bitcoin zai karye ba, sai dai yana iya tas

iri akan liquidity da interest-rate expectations, kuma wannan na iya sauya alkiblar kasuwar crypto.