Halin da ake ciki a duniyar cryptocurrency na cike da damarmaki na canza rayuwa, amma a daya bangaren kuma, akwai barayi na zamani da kullum suke kirkirar sabbin hanyoyin da za su kwashe wa mutane kadarorinsu. Mafi hadari da tsoro a cikin wadannan hanyoyi a yanzu ita ce wacce ake kira βPig Butcheringβ Scam (ko Sha Sha Tau).
Wannan rahoton na musamman ne muka tsara shi don masu neman sani da kuma zuba jari a kasuwancin crypto domin ku gane tarkon tun kafin ku fada ciki.
Ka taba karbar sako ta WhatsApp ko Telegram daga lambar da ba ka sani ba, tana cewa: "Sannu, kamar kai ne wanda muka haΙu a Ιakin taron crypto submit?" ko kuwa "Hi John, gobe zamu hadu don tattaunawa akan kasuwancin nan?"
Idan ka amsa musu da cewa "A'a, ka yi kuskuren lamba ne," maimakon su nemi gafararka su wuce, sai su ce: "Haba dai! Amma dai kai mutumin kirki ne, ko za mu iya zama abokai?"
Anan ne wasan yake farawa. Wannan ita ce hanyar shiga tarkon "Pig Butchering" (ko Sha Sha Tau). Sunan ya fito ne daga kalmar Sinanci "Sha Zhu Pan". Ma'anarta ita ce: Kiwata alade yayi Ιul-Ιul kafin ka yanka shi.
Masu aikata wannan salon damfara, basa hanzari ko yunkurin gaggawa. Zasu lallashe kane zuwa wani lokaci cike da aminci da kyautatawa kafin daga bisani suyi awon gaba da duk kwabben dake lalitar ka galibi ta hanyar dandamalin bogi.
Matakai Hudu Na Hikima Da Suke Amfani Dasu
Masu damfarar suna fara tuntubar ka ta kuskure. Suna amfani da hotunan kyawawan mata ko maza masu rishin arziki a shafukansu. Suna nuna matukar kulawa da damuwa da rayuwarka, har sai ka amince musu a matsayin abokai na kusa ko ma masoya na gaske.
Bayan sun tabbatar ka saki jiki dasu, sai su fara turo hotunan rayuwarsu ta alfarmaβmotoci na alfarma, abinci a otal-otal masu tsada. Idan ka tambaye su sirrin arzikinsu, sai su ce maka Crypto Trading ne ta wani dandali na musamman da suke amfani da shi.
Za su tura maka hanyar shiga (link) na wani dandali na bogi (wanda ke kama da Binance ko Coinbase amma na jabu ne). Za su ce ka saka $100 ko $500 gwaji. Cikin kankanin lokaci, za ka ga kudin sun ninka. Har ma za su kyale ka ka cire (withdraw) wadannan kudaden don ka amince 100% cewa tsarin na gaskiya ne.
Ganin ka samu riba, sai ka kwashe duk tanadinka, ko ma ka yi rance don ka zuba kudi masu yawa ($10,000 zuwa sama). Da zaran ka tura wadannan kudaden, sai ka ga dandalin ya daskare. Idan kana son ka cire kudadenka, sai su ce maka sai ka biya haraji (tax) na kashi 20%. Ko ka biya, ba za su taba baka kudin baβdaga nan sai su bace gaba daya.
Halayen da Za Ka Gane Masu Wannan Damfara (Red Flags)
A matsayinka na mai biye da duniyar crypto, dole ne idanunka su kasance bude. Ga alamomin da za ka gane kana fuskantar masu Pig Butchering:
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Sakon da ya zo ta "kuskure": Kusan dukkan tuntuΙar farko tana farawa ne da nuna kamar an yi kuskuren tura sako ne.
Zance ya koma kan Crypto da sauri: Ko da kun fara maganar iyali ne ko abinci, dole sai sun nemo dabarar da zance zai karkata kan yadda suke samun kudi a crypto.
Dandalin zuba jari mara rijista: Suna tura ka zuwa wasu manhajoji (Apps) ko shafukan yanar gizo da ba a san su ba a duniya, kuma ba za ka same su a Google Play Store ko Apple App Store na gaskiya ba.
Neman ka zuba kudi na gado: Suna matsa maka lamba ka sayar da kadarorinka ko ka yi rance domin "wannan damar ba za ta dade ba.
Babban Gargadi: Babu wani kwararren mai harkar crypto da zai binciko ka ta WhatsApp don ya koya maka yadda ake samun kudi kyauta
Yadda Za Ka Kare Kanka da Dukiyarka
Kada ka bari kwadayi ko kadaici ya sanya ka fada cikin wannan mummunan tarkon. Ga hanyoyin tsira:
Kada ka amince da bako a intanet: Kada ka taba yarda da shawarar zuba jari daga mutumin da ba ka taba haduwa da shi ido-da-ido ba.
Yi bincike mai zurfi (DYOR): Koyaushe ka yi amfani da sanannun dandaloli (kamar Binance, OKX, Bybit) don gudanar da hada-hadar crypto dinka.
Kada ka taba tura kudi zuwa dandali da ba ka sani ba: Idan ba ka ga sunan dandalin a jerin manyan dandaloli na duniya ba, kada ka taba saka ko da kobo daya.
A matsayinmu na mambobin da ke son ganin ci gaban crypto a kasashenmu na Hausa, kare dukiyarmu shi ne mataki na farko na samun nasara. Ka kasance mai lura, kuma ka kayi sharing rahoton ga abokanka domin mu gudu tare mu tsira tare.