Crypto BULL RUN yana zuwa kullum tambayar ita ce zaka kasance a shirye wannan karon, ko za ka tsaya kana kallon wasu suna samun kudin da zai canza rayuwar su yayin da kai har yanzu kana kokarin fahimta? Idan kana Najeriya, Ghana, Kenya, South Africa, ko ko’ina a Afrika, wannan shi ne jagoranka. Mai sauki. A aikace. Babu hayaniya.

Mataki na 1: Gyara Harkokin Kudinka Da Farko

Kafin ka taba crypto, ka gyara al’amuranka. Ka biya basussuka masu yawa wadan da ka karba. Ka ajiye akalla kudin rayuwa na watanni 1–3 a matsayin emergency fund. Bull run yana da dadi amma shiga ba tare da kariya ba yana da hadari. Ka saka kudin da zaka iya rasawa gaba daya kawai.

Mataki na 2: Fara Shiryawa Yanzu Basai Lokacin Trend Ba

Lokacin da kowa a unguwarka yake magana akan Bitcoin, farashin ya riga ya tashi sosai. Masu hankali suna farawa da wuri a hankali. Kafara siya kadan-kadan daga yanzu ana kiran wannan Dollar Cost Average (DCA). Ba sai katara da yawa ba. Ko $10–$20 a wata zai iya gina matsayi mai kyau a hankali.

Mataki na 3: Ka tsaya kan Manyan Assets

Ba lokacin caca ba ne akan altcoins na banza da WhatsApp groups ke turawa. A lokacin bull run, coins da suke tsira kuma su yi nasara sune Bitcoin (BTC) da Ethereum (ETH). Idan ka saba, zaka iya duba wasu altcoins masu kyau amma BTC da ETH sun zama tushe.

Mataki na 4: Yi Amfani da Platforms Masu Aminci

Ka siya kuma ka ajiye crypto a wuraren da zaka iya amincewa dasu kawai kamar Binance, Gate.io, CoinW, ko Coinbase. Ka nisanci duk wani wuri da ke bada tabbacin riba ko mutane ke tafiyar da shi. Idan ba a tsara shi ba, kudinka basa cikin aminci da tsaro.

Mataki na 5: Ka Kare Dukiyarka Kamar Rayuwarka

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Ka cire crypto dinka daga exchange zuwa wallet din daka tanada. Rubuta Seed Phrase dinka a takarda ka ajiye shi a wuri mai tsaro. Kada ka taba ba kowa shi. A lokacin bull run, masu damfara suna kara yawa β€” fake giveaways, phishing links, fake exchanges. Ka kasance cikin shiri.

Mataki na 6: Ka Sanya Target Kuma Ka Siyar Da Gaske

Mutane da yawa a Afrika sun samu riba mai yawa a bull run na 2021 a takarda amma amsu sayar ba. Sai kasuwa ta fadi dasu suka rasa komai. Ka yanke shawara tun da wuri: a wane farashi zaka dauki riba? Ka sa target. Ka tsaya a kai. Daukar riba 50% ya fi rike 100% ka kare ba komai.

Mataki na 7: Ka Cigaba Da Koyo A Kowane Lokaci

Crypto yana canzawa da sauri. Ka bi sahihan mutane, ka karanta labarai daga shafuka kamar CoinDesk ko Cointelegraph, ka shiga communities da ake bada bayanai na gaskiya. ilimi shi ne makamin ka mafi karfi musamman a Afrika inda bayanai marasa kyau ke yaduwa da sauri.

Karshe

Bull run yana saka lada ga wanda ya shirya, ba wanda yayi murna kawai ba. Shirya yanzu. Ka kasance mai daidaito. Ka kare dukiyarka. Kuma idan kudin ya zo β€” ka dauka.


Wannan rubutu don ilimi ne kawai, ba shawarar saka jari ba.