A duniyar kasuwancin crypto, farashi baya tafiya kawai saboda fasaha ko canjin tattalin arziki; yana tafiya ne mafi yawancin lokuta saboda motsin rai (emotions). Tsoro, fargaba, da kuma doki sune manyan injunan da ke gudanar da kasuwar nan da muke ciki.

Hakan ya sa aka fito da kalmomin nan guda biyu da kowa ya sani: FUD (Fear, Uncertainty, and Doubt) β€” wato tsoratarwa da jifanta kasuwa da shakku don rage farashi, da kuma Hype (ko FOMO - Fear Of Missing Out) β€” wato hura wutar farin ciki na bogi don cusa wa mutane kwalamar siye a lokacin da farashi ya yi tsada.

A matsayinka na mai zuba jari na zamani, dogaro da idanunka kawai don tace gaskiya a cikin dubunnan labaran Twitter (X), Telegram, da Discord ba zai taba yiwuwa ba. Anan ne fasahar AI Sentiment Analysis Tools (Kayan aikin AI na auna ra'ayoyin jama'a) zai taimaka maka 


Menene AI Sentiment Analysis a Duniyar Crypto?

Wannan wata fasaha ce ta mutum-mutumi (Artificial Intelligence) da ke amfani da tsarin Natural Language Processing (NLP). Aikinta shine ta shiga lungu da sako na intanet, ta kwashe miliyoyin rubuce-rubuce, labarai, da maganganun mutane akan wani babban kudin crypto (kamar Bitcoin ko Ethereum), sannan ta yi nazari akan ko mutanen na magana ne cikin fushi, tsoro, farin ciki, ko kuma kwadayi.

Maimakon ka zauna kana karanta sako dubu biyar, AI zai fassara maka su zuwa ga lissafi ko jadawali mai saukin fahimta a cikin dakika kalilan.


Hanyoyi 3 Da Zaka Gano "FUD" Da "Hype" Cikin Sauki

Idan kana amfani da wadannan kayan aikin na AI, ga abubuwan da ya kamata ka mayar da hankali akai don gano tarkon kasuwa:


1. Bambance Tsakanin Labarin Gaske da "FUD" (Tsoratarwar Bogi)

Lokacin da wata mummunar jita-jita ta barke (misali: "Gwamnati kaza za ta haramta Crypto"), farashi yakan fadi da sauri. AI Sentiment tools na iya auna abin da ake kira "Social Volume" (yawan mutanen da ke maganar) da kuma "Sentiment Score" (maki na yanayin ra'ayin).

Tarkon FUD: Idan AI ya nuna maka cewa ra'ayin mutane ya koma na tsoro (Negative Sentiment) amma babu wani babban canji a cikin tsarin blockchain din kansa (on-chain data), to kwararan alamomi ne na cewa "FUD" ake kitsawa don tsoratar da kananan masu zuba jari su sayar da kudadensu cikin asara, domin manyan kifi (Whales) su saya da arha.


2. Lokacin Tsanantar "Hype" (Murna ta Bogi) 

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Hype ita ce abokiyar gaba ga alusunka. Lokacin da kudin crypto ya fara tashi, kowa fara maganarsa ta alheri. AI zai nuna maka "Extreme Greed" (tsananin kwadayi) ko "Positive Sentiment Spikes".

Tarkon Hype: Idan jadawalin AI ya nuna maka cewa murnar mutane ta wuce kima (ta kai 80% zuwa 90%), to wannan shi ne lokacin da ya kamata ka dakata da siye, ko ma ka fara siyarwa ka fita. Domin yawanci idan hayaniyar ta yi yawa, kasuwa ta kusa dambaraswa (Correction).


3. HaΙ—a Sentiment Data da Volatility (Motsayin Kasuwa)

Manyan kwararru ba sa amfani da ra'ayi kadai. Suna duba alakar da ke tsakanin abin da mutane ke fada da kuma ainihin abin da ke faruwa a kasuwa. Idan AI ya nuna ra'ayin mutane ya yi kyau sosai amma kuma farashin kudin ya ki tafiya sama, to lallai akwai lauje cikin nadi β€” akwai masu juyawa kasuwar ta boye.


AI Platforms da Bayanan da Suke Aunawa?

Santiment: Binciken On-chain da Social Media. Yawan magana a X/Telegram da maki na tsoro/farin ciki.

LunarCrush: Karfin Jama'a (Social Intelligence). Yana auna tasirin da masu fada a ji (influencers) ke da shi akan kowane kudi.

Crypto Fear & Greed Index: Ma'aunin Tsoro da Kwadayi Gamsarwa ga yanayin kasuwa baki daya (daga 0 zuwa 100).

The Tie: Bayanan Sentiment na Lokacin-Gaske. Yana tace labaran jaridu da shafukan sada zumunta don gano motsin farashi na gaba.

Yayin da kake lura da labarai a shafukan sada zumunta, karka bari tsoron FUD ko kwalamar Hype ta rude ka. Yi amfani da kayan aikin AI na zamani don tace hayaniya, ka gano gaskiyar inda kudin kasuwar ke dosa, kuma ka kare jarinka.

Magana mai Tasiri a kasuwar crypto crypto: Do Your Own Research (DYOR), amma a wannan karon, bari AI ya zama mataimakinka wajen binciken!

Me kuke gani game da amfani da AI wajen gano tarkon kasuwa? Kun taba fadawa tarkon FUD ko Hype? Ku rubuta mana ra'ayoyinku a sashen sharhi (comments)!