A halin yanzu, idanuwan daukacin masu zuba jari a fadin duniya sun koma kan farashin Bitcoin (BTC). Tambayar da kowa ke yi a yanzu ita ce: Wane mataki kasuwar za ta dosa? Bayan fuskantar fadi tashi da kuma sauyin farashi na ba tsammani, maganar cewa Bitcoin zai iya taba matakin $40,000 (The $40k Scenario) ta zama babban topic na muhawara tsakanin kwararrun masu sharhi kan tattalin arziki.

A cikin wannan rahoton, za mu fuskanci gaskiyar lamarin, mu duba abubuwan da za su iya janyo hakan, da kuma abin da hakan ke nufi ga makomar yan crypto.


Me Yasa $40k?

Maganar saukar Bitcoin zuwa $40,000 ba ta zo haka kawai ba. Akwai manyan dalilai guda uku da ke barazana ga farashin a halin yanzu:

1. Sayarwa Daga Manyan Hukumomi (Institutional Selling): Kamfanoni da gwamnatoci da ke rike da kudaden crypto masu yawa suna yawan cefanarwa domin samun na goro (liquidity), wanda hakan ke janyo faduwar farashi saboda Ζ™aruwar yawan supply.

2. Matakan Tsanantawa Daga Gwamnatoci (Regulatory Pressures): Hukumomin tsara dokoki na Amurka (SEC) da na Turai suna ta fito da tsauraran dokoki kan musayar kudaden crypto. Wannan yana tsoratar da sabbin masu zuba jari.

3. Koma Baya na Yanayin Tattalin Arziki (Macroeconomic Factors): Ƙarin kudin ruwa da bankunan ke yi don dakile hauhawar farashin kaya (inflation) yana sa masu zuba jari 

4. janye kudadensu daga kasuwanni masu hadari kamar crypto, su koma tabbatattun fannoni.


Me Zau Faru Idan BTC Ya Fadi Zuwa $40k?

Idan har Bitcoin ya taba wannan matakin, abubuwa biyu ne manya ake kyautata zagon za su faru a kasuwa:

1. Firgici da Kuma Sayar da Kaya Cikin Gaggawa (Panic Selling)

Ga kananan masu zuba jari (retail investors), ganin farashin ya sauko kasa zai iya haifar da fargaba, wanda zai tilasta musu sayar da abin da ke hannunsu don tsoron kar su yi asarar duka kudadensu. Wannan shi ake kira Capitulation a fannin crypto.

2. Masu Hannu Da Shuni (The Whale Accumulation)

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

A daya bangaren kuma, manyan masu kudi da kamfanoni (Whales) suna kallon matakin $40,000 a matsayin babbar dama ta sayan Bitcoin cikin sauki. Matakin $40k babban shinge ne na goyon baya (Major Support Level) wanda ke da wuyar karyewa, domin akwai masu saye da yawa da ke jiran farashin ya fado nan don su daka babban kamu.


Hasashen Makoma: Ina Aka Dosa?

Masu fashin baki sun kasu kashi biyu kan wannan batu:

Masu Gani Da Kyau (The Bullish View): Suna ganin ko da Bitcoin ya sauko $40k, hakan zai zama tamkar jan baka ne da za a sake shi don ya lula zuwa sama da karfi, wanda zai iya karkata zuwa matakin $70k ko fiye da haka kafin karshen shekara.

Masu Hakon Koma Baya (The Bearish View): Suna gargadin cewa idan har aka karye matakin $40,000 ba tare da an samu masu saye da yawa ba, to fa kasuwar zata iya shiga dogon lokaci na sanyi (Crypto Winter), inda farashin zai iya komawa har $35,000 ko kasa da haka.


Shawara Ga Masu Karatu Da Masu Zuba Jari

Kasuwar crypto ba wuri ba ne na garaje ko bin ra'ayin taron jama'a (FOMO). Idan kai mai zuba jari ne a wannan lokaci, ga abubuwan da ya kamata ka kiyaye:

Rarraba Hannun Jari (Diversification): Kar ka taba sanya dukkan kudadenka a narrative guda ko a coin guda daya.

Yi Binciken Kanka (DYOR): Koyaushe ka dogara da sahihan bayanai da alkaluman kasuwa, ba jita-jita ba.

Zuba Jari Na Dogon Lokaci: Tarihi ya nuna cewa masu rike da coins na tsawon lokaci (HODLers) sune mafi yawan lokuta ke fita da nasara lokacin da kasuwa ta daidaita.