A halin yanzu, kasuwar crypto ta yi tsit. Mutane da dama da suka shigo da gudu a lokacin da komai ke tashi (Bull Market), yanzu sun fece. Shafukan sada zumunta ba sa ruri kamar da, kuma idan ka duba darajar portfolio ta watse, zakayi tunanin karshen crypto ne yazo.
Sakon da ke yawo a tsakanin gama Gari shi ne: "Crypto ya mutu."
Amma ga kwararrun dillalai, masu hangen nesa, da kuma wadanda suka san sirrin wannan kasuwa, wannan shirun ba alamun mutuwa ba neβalamun dama ce ta musamman. Kamar yadda wani sanannen kararin magana na dandalin Wall Street ke cewa: "Kasuwa mai rauni (Bear Market) ita ce ke mai da talakawa mawadata, yayin da kasuwa mai karfi (Bull Market) ke tabbatar da hakan."
Me Yasa Koda Yaushe YanBaiwa Ke Sayen Top (tsada)?
Babban kuskuren da yawancin Ζ΄an kasuwar crypto ke yi shi ne tafiya da ra'ayin taron jama'a (Herd Mentality). Suna tsoron shiga kasuwa lokacin da komai ya yi araha kuma kowa ke kuka, amma suna yin rububin saye lokacin da farashi ya riga ya tashi sama, inda daga nan kuma kasuwar ke juyawa da su.
A lokacin da kasuwa ke fuskantar jajayen kwanaki (Bear Market):
Tsoro da fargaba (Fear & Panic) ke mulkin zukatan mafi yawan mutane, wanda hakan ke sa su sayar da kadarorinsu cikin asara.
Labaran karaya (FUD) ke mamaye kafafen yada labarai, suna nuna cewa crypto ba zai sake tashi ba.
Farashin manyan kadarori kamar Bitcoin da Ethereum na fadowa kasa da kima, wanda hakan ke samar da rangwame na musamman.
Yayin da sauran masu zuba jari ke guduwa saboda tsoron asara, su kuma manyan giwaye da kamfanonin zuba jari (Whales) a lokacin ne suke shigowa da kudadensu suna kwasar kadarori cikin sauki. Suna saye ne lokacin da "jini ke kwarara a kasuwa," domin sun san cewa nan gaba kadan, wadanda suka gudu za su dawo da gudu su sayi wadannan kadarorin a farashi mai tsada sosai.
Me Yasa Wannan Shi Ne Lokacin Gina Arziki?
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Idan ka dubi tarihin crypto, kowane lokacin (Crash) na biye ne da wani babban tashin gwauron zabi (Rally) wanda ke kafa sabbin tarihin girgizar kasar kuΙaΙe.
Lokacin Faduwar Kasuwa (Bear market): gama garin Ζ΄an kasuwa suna siyarwa ne domin tsoron asara. A lokacin da kwararrun yan kasuwar ke dabarar siya kadan-kadan DCA
Lokacin Yabanya (Bull Market): gama garin yan kasuwa suna rige-rigen sayen kadara domin fargabar kar abarsu a baya. A daidai lokacin da kwararrun ke siyarwa (take profit)
Don haka, idan kana son sauya fasalin rayuwarka ta fannin kudi, yanzu ne lokacin yin bincike mai zurfi (DYOR), gano projects da ke da ingantaccen tushe (Good Fundamentals), da kuma fara dabarar zuba jari ta Dollar-Cost Averaging (DCA)βwato sayen kadan-kadan a tsakanin lokuta mabanbanta.
Shiri Domin Gobe
Kada ka bari yanayin kasuwar yanzu ya yaudare ka. Kasuwar crypto tana tafiya ne a cikin (Cycles). Wannan matakin na yanzu kamar shuka ce a lokacin damina; ba ka ganin amfanin gona nan take, amma idan rani ya kusa, farin ciki zai cikaka saboda ganin yalwa.
Babban kalubalenka a yanzu shi ne juriya da kuma ilmantar da kanka. Yayin da sauran mutane ke barci suna tunanin crypto ya riga ya mutu, ka tabbatar kai kana can kana gyara akwatinanka na ajiya, kana koyon dabarun DeFi, Web3, da kasuwanci na gaba daya.
Zantukan Hikima: "Anayin arziki ne ta hanyar siyan kadara lokacin da mafiya yawan jama'a ke cikin halin shakku da tsoro; sannan a sayar lokacin da kowa ke murna da jin shi wani na musamman ne."
Shin za ka zama cikin wadanda za su yi kuka idan kasuwa ta tashi, ko kuwa za ka zama cikin wadanda za su yi murmushin nasara?