Yana kama da abu mai ma’ana har mutane kusan ba sa tambayarsa.

"Zan sayar idan ya kai target dina."

Wannan ita ce ƙaryar. Ba target ɗin ba. Ba strategy ɗin ba. Kalmar "zan." Domin lokacin da lambar dake kan screen tayi daidai da abin da kayi mafarki a kai na tsawon watanni wani abu yana canzawa. Kwakwalwa tana matsar da burin gaba. Kana shawo kan kanka cewa zai iya ƙara hawa. Sai ka riƙe. Daga baya kuma ka kalli komai yana dawowa ƙasa.

Wannan ita ce babbar ƙarya a crypto. Ba scams ba. Ba fake projects ba. Ba market manipulation ba. Waɗannan ƙaryoyi ne da wasu mutane suke faɗa maka. Wannan kuwa kai kake faɗa wa kanka. Kuma tana jawo asara fiye da komai.

Dalilin Da Yake Faruwa

Kowane investor yana shiga crypto da tsari mai kyau. Saya. Kalli ya ƙaru. Sayar a sama.Tsai mai sauƙi. Tsarin yana aiki da kyau har sai farashi ya fara motsawa da gaske.

Lokacin da portfolio ɗinka ya tashi da 200%, sai kafara raina target ɗin da kasa. Kana yin sabon lissafi. Kana neman analysts waɗanda za su tabbatar maka da sabon babban burinka. Kana watsi da muryoyin masu taka-tsantsan saboda kana ganin basu fahimci abin da ka fahimta ba.

Wannan ba wauta bace. Wannan psychology na ɗan adam ne. Lokacin da farashi yake hawa, kwakwalwa tana da wahalar tunanin zai iya sauka. Sayarwa yana nufin ka daina jin daɗin ganin kuɗinka yana ƙaruwa. Saboda haka yawancin mutane basa sayarwa. Suna jira. Sai kasuwa ta juya.

Darasin 2021 Wanda Babu Wanda Ya Koya

A Nuwamba 2021, Bitcoin ya kai kusan $69,000. Ethereum ya wuce $4,800. Mutanen da suke riƙe da ribar da zata iya canza rayuwarsu a takarda ana gaya musu cewa $100,000 yana nan kusa.

Mutane nawa suka sayar? Kaɗan ne sosai.

Zuwa ƙarshen 2022, Bitcoin ya rasa sama da 75% na darajarsa. Yawancin altcoins sun rasa 90% ko fiye. Mutanen da suke da kuɗin da zai canza rayuwar su a Nuwamba 2021 sun fuskanci babbar asara bayan watanni 12 ba don crash ɗinba a iya hango shi ba, amma saboda sun yi imanin za su san lokacin sayarwa. Kuma lokacin ya zo, suka shawo kansu cewa har yanzu bai zo ba.

Ƙaryar Da Ke Cikin Wannan: "Ni Long-Term Investor Ne"

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Wannan magana ana amfani da ita a yanayi biyu daban daban.

Ga investors masu discipline, long-term holding hanya ce ta gaske wadda take dogara da bincike, imani, da matsayi da zasu iya barinsa ba tare da taɓawa ba na shekaru.

Ga wasu da yawa, "Ni long-term investor ne" shi ne abin da mutane suke faɗa lokacin da suka saya kusa da sama, suka kalli farashi ya faɗi, kuma basa iya fuskantar sayarwa da asara. Holding ya zama ba strategy ba amma hanyar ɓoye ciwo. Yin gaskiya da kanka game da wanne ne kai yana daga cikin abubuwa mafi amfani da za ka iyayi wa kuɗinka.

Tarkon Altcoin: "Zai Dawo"

Bitcoin ya dawo daga duk manyan crashes a tarihinsa. Wannan tarihin ya haifar da tunani mai haɗari cewa duk crypto assets suna aiki iri ɗaya.

Ba haka ba ne. Luna ta kasance top 10 cryptocurrency mai darajar dala biliyan 40. Ta koma sifili cikin awanni 72 a Mayu 2022. BitConnect. SafeMoon. Iron Finance. Jerin projects da suka faɗi kuma ba su dawo ba ya fi yawa sosai fiye da waɗanda suka dawo. "Zai dawo" gaskiya ne kawai ga assets masu zurfin daraja na gaske. Idan akayi amfani da shi ga komai ƙarya ce da ta lalata dukiya mai yawa.

Mafita:- Tsari Kafin Kwaɗayi Ya Zo

Babu wanda ya san saman kasuwa yaushe zai zo. Babu kowa. Ba analysts ba. Ba whales ba. Ko mutanen da suka yi sa’a suka hango na baya. Ana ganin saman ne kawai bayan komai ya faru.

Amsa mai amfani ita ce mai sauƙi — ɗauki profits yayin da kasuwa ke hawa. Ba gaba ɗaya lokaci guda ba. Ba ƙoƙarin gano peak ɗin daidai ba. Sai dai a hankali kuma da tsari. Sayar da wani ɓangare a target na farko. Wani ɓangare idan ya ƙara hawa. Ka bar wani ɓangare don yiwuwar ƙarin tashi. Amma ka kulle ribar gaske a hanya. Wannan strategy ba zai taɓa ba ka cikakken saman kasuwa ba. Amma yana tabbatar da cewa crash ba zai goge duk abin da ka gina ba.

Babbar ƙarya a crypto ita ce wadda kake faɗa wa kanka lokacin da kwaɗayi ya kai kololuwa. Gina tsarinka kafin wannan lokacin ya zo kuma ka tsaya a kai ko da duk muryoyin dake kusa da kai suna cewa ka riƙe kaɗan kaɗan.

Wannan article domin ilimi ne kawai kuma ba financial advice ba ne.