Yana kama da abu mai maβana har mutane kusan ba sa tambayarsa.
"Zan sayar idan ya kai target dina."
Wannan ita ce Ζaryar. Ba target Ιin ba. Ba strategy Ιin ba. Kalmar "zan." Domin lokacin da lambar dake kan screen tayi daidai da abin da kayi mafarki a kai na tsawon watanni wani abu yana canzawa. Kwakwalwa tana matsar da burin gaba. Kana shawo kan kanka cewa zai iya Ζara hawa. Sai ka riΖe. Daga baya kuma ka kalli komai yana dawowa Ζasa.
Wannan ita ce babbar Ζarya a crypto. Ba scams ba. Ba fake projects ba. Ba market manipulation ba. WaΙannan Ζaryoyi ne da wasu mutane suke faΙa maka. Wannan kuwa kai kake faΙa wa kanka. Kuma tana jawo asara fiye da komai.
Dalilin Da Yake Faruwa
Kowane investor yana shiga crypto da tsari mai kyau. Saya. Kalli ya Ζaru. Sayar a sama.Tsai mai sauΖi. Tsarin yana aiki da kyau har sai farashi ya fara motsawa da gaske.
Lokacin da portfolio Ιinka ya tashi da 200%, sai kafara raina target Ιin da kasa. Kana yin sabon lissafi. Kana neman analysts waΙanda za su tabbatar maka da sabon babban burinka. Kana watsi da muryoyin masu taka-tsantsan saboda kana ganin basu fahimci abin da ka fahimta ba.
Wannan ba wauta bace. Wannan psychology na Ιan adam ne. Lokacin da farashi yake hawa, kwakwalwa tana da wahalar tunanin zai iya sauka. Sayarwa yana nufin ka daina jin daΙin ganin kuΙinka yana Ζaruwa. Saboda haka yawancin mutane basa sayarwa. Suna jira. Sai kasuwa ta juya.
Darasin 2021 Wanda Babu Wanda Ya Koya
A Nuwamba 2021, Bitcoin ya kai kusan $69,000. Ethereum ya wuce $4,800. Mutanen da suke riΖe da ribar da zata iya canza rayuwarsu a takarda ana gaya musu cewa $100,000 yana nan kusa.
Mutane nawa suka sayar? KaΙan ne sosai.
Zuwa Ζarshen 2022, Bitcoin ya rasa sama da 75% na darajarsa. Yawancin altcoins sun rasa 90% ko fiye. Mutanen da suke da kuΙin da zai canza rayuwar su a Nuwamba 2021 sun fuskanci babbar asara bayan watanni 12 ba don crash Ιinba a iya hango shi ba, amma saboda sun yi imanin za su san lokacin sayarwa. Kuma lokacin ya zo, suka shawo kansu cewa har yanzu bai zo ba.
Ζaryar Da Ke Cikin Wannan: "Ni Long-Term Investor Ne"
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Wannan magana ana amfani da ita a yanayi biyu daban daban.
Ga investors masu discipline, long-term holding hanya ce ta gaske wadda take dogara da bincike, imani, da matsayi da zasu iya barinsa ba tare da taΙawa ba na shekaru.
Ga wasu da yawa, "Ni long-term investor ne" shi ne abin da mutane suke faΙa lokacin da suka saya kusa da sama, suka kalli farashi ya faΙi, kuma basa iya fuskantar sayarwa da asara. Holding ya zama ba strategy ba amma hanyar Ιoye ciwo. Yin gaskiya da kanka game da wanne ne kai yana daga cikin abubuwa mafi amfani da za ka iyayi wa kuΙinka.
Tarkon Altcoin: "Zai Dawo"
Bitcoin ya dawo daga duk manyan crashes a tarihinsa. Wannan tarihin ya haifar da tunani mai haΙari cewa duk crypto assets suna aiki iri Ιaya.
Ba haka ba ne. Luna ta kasance top 10 cryptocurrency mai darajar dala biliyan 40. Ta koma sifili cikin awanni 72 a Mayu 2022. BitConnect. SafeMoon. Iron Finance. Jerin projects da suka faΙi kuma ba su dawo ba ya fi yawa sosai fiye da waΙanda suka dawo. "Zai dawo" gaskiya ne kawai ga assets masu zurfin daraja na gaske. Idan akayi amfani da shi ga komai Ζarya ce da ta lalata dukiya mai yawa.
Mafita:- Tsari Kafin KwaΙayi Ya Zo
Babu wanda ya san saman kasuwa yaushe zai zo. Babu kowa. Ba analysts ba. Ba whales ba. Ko mutanen da suka yi saβa suka hango na baya. Ana ganin saman ne kawai bayan komai ya faru.
Amsa mai amfani ita ce mai sauΖi β Ιauki profits yayin da kasuwa ke hawa. Ba gaba Ιaya lokaci guda ba. Ba ΖoΖarin gano peak Ιin daidai ba. Sai dai a hankali kuma da tsari. Sayar da wani Ιangare a target na farko. Wani Ιangare idan ya Ζara hawa. Ka bar wani Ιangare don yiwuwar Ζarin tashi. Amma ka kulle ribar gaske a hanya. Wannan strategy ba zai taΙa ba ka cikakken saman kasuwa ba. Amma yana tabbatar da cewa crash ba zai goge duk abin da ka gina ba.
Babbar Ζarya a crypto ita ce wadda kake faΙa wa kanka lokacin da kwaΙayi ya kai kololuwa. Gina tsarinka kafin wannan lokacin ya zo kuma ka tsaya a kai ko da duk muryoyin dake kusa da kai suna cewa ka riΖe kaΙan kaΙan.
Wannan article domin ilimi ne kawai kuma ba financial advice ba ne.