A cikin βyan kwanakin nan, kasuwar crypto na kara shiga wani sabon yanayi bayan bullar wani muhimmin alβamari da zai iya sauya yadda βyan kasuwa ke hulΙa da kasuwar. Wannan sabon alβamari shi ne US Perpetual Futures (US Perps) β wani sabon tsarin cinikin derivatives da ake ganin zai iya bude wata babbar kofa ga masu zuba jari daga Amurka.
Tsawon lokaci, an samu takunkumi da matsaloli wajen bai wa masu amfani daga Amurka damar shiga wasu nauβikan kasuwannin crypto derivatives, musamman perpetual contracts, wadanda suka zama daya daga cikin manyan bangarorin kasuwar crypto a duniya.
Amma yanzu, dawowar US Perps na iya zama wani muhimmin mataki da zai kara kawo sauyi a kasuwar.
Menene US Perps?
Perpetual Futures wani nauβin kwangilar ciniki ne da bai da ranar karewa. Wannan yana bawa βyan kasuwa damar yin hasashen hawa ko saukar farashin wani asset kamar Bitcoin, Ethereum ko wasu tokens ba tare da sun mallake su kai tsaye ba.
A cikin wannan tsarin, masu ciniki na iya amfani da leverage domin kara girman matsayinsu a kasuwa, wanda ke nufin damar samun riba mai yawa β amma kuma yana zuwa da karin hadari.
Me Yasa Dawowar US Perps Yake Da Muhimmanci?
Amurka tana daya daga cikin manyan kasuwannin hada-hadar kudi a duniya. Idan aka samu damar shiga wannan bangare na crypto cikin tsari mai kyau, hakan na iya kawo:
Karin yawan masu shiga kasuwa
Karin liquidity (kudin zagayawa a kasuwa)
Sabbin manyan βyan kasuwa daga bangaren kudi na gargajiya
Kara gasa tsakanin manyan kamfanonin crypto
A saukake, idan manyan masu kudi suka samu saukin shiga kasuwar perpetual futures, hakan na iya kara yawan muβamala a kasuwar crypto.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Shin Wannan Na Nufin Kasuwa Za Ta Tashi?
Ba lallai ba ne. Kasuwar crypto tana da abubuwa da dama da ke tafiyar da ita kamar:
Yanayin tattalin arzikin duniya
Shaβawar masu zuba jari
Interest rates
Liquidity
Halin masu ciniki
Amma tarihi ya nuna cewa idan aka samu sabbin hanyoyin shigar manyan βyan wasa kasuwa, hakan kan haifar da karin motsi (volatility) da sabbin damammaki.
Abin Da Ya Kamata Masu Crypto Su Kula Da Shi
Duk da cewa US Perps na iya zama babban labari ga kasuwa, perpetual trading ba wasa ba ne. Amfani da leverage ba tare da tsari ba na iya jawo asarar kudi cikin sauri.
Shigowar US Perps na iya zama daya daga cikin manyan abubuwan da za su kara sauya fasalin kasuwar crypto a wannan zamani.
Yayin da ake kara hade duniyar kudi ta gargajiya da blockchain, kasuwar crypto na ci gaba da bude sabbin hanyoyi masu amfani ga masu zuba jari.
Tambayar da ta rage ita ce: Shin US Perps zasu zama sanadin sauya akalar kasuwa zuwa Bullrun?