Mu leƙa kasuwar crypto wannan satin.
Na tabbata kuma shaida ne bisa tirka-tirka tare da rashin tabbacin dake faruwa a cikin space ɗin nan musamman irin wannan lokacin. A satinnan ne dai farashin bitcoin ya nuna wata halayya irin ta masu marisa, abun kamar abun tsoro yayinda daga bisani kuma yayi bazata.
Wani abun burgewa kuma shine yadda fasahar Blockchain da crypto ke samun gindin zama a tsarin harkar kuɗaɗen gargajiya "traditional finance".
Wasu muhimman abubuwan da suka faru:
BITCOIN at $80K+
Bitcoin ya farfaɗo bayan matsin lambar da kasuwa ta fuskanta sakamakon rashin ci gaba kan dokar crypto ta Amurka da kuma shawarar Federal Reserve.
CLARITY ACT
Majalisar Dattawan Amurka ta kasa ciyar da babban kudirin dokar crypto gaba. Wannan ya haifar da sabon yanayin tan-tama da rashin tabbaci akan makomar kasuwar.
FED
A satinnan ne dai Federal Reserve ta ƙara interest rate a karon farko cikin shekaru uku, lamarin da ya ƙara rikita kasuwannin risk assets.
SEC TA BUƊE ƘOFA 🔥
SEC ta ƙaddamar da wani tsarin gwaji da zai bai wa wasu trading platforms damar gwada cinikin hannayen jarin Amurka waɗanda aka fi sani da tokenized assets a kan blockchain.
Wannan na iya zama babban mataki wajen ƙulla ɗorarriyar alaƙa tsakanin Wall Street da kasuwancin crypto.
ƁANGAREN ETHEREUM
Manyan kamfanoni sun cigaba da nuna ra'ayin su akan Ethereum. Acikin satin nan dai BitMine ta sanar da cewa holdings ɗinta sun kai kusan 5.96M ETH, wanda ya nuna yadda Ethereum ke ƙara zama wani muhimmin asset ga wasu kamfanoni.
Zcash yayi recording sabon all time high wanda hakan ya sake jan hankalin masu zuba jari akan kasuwar privacy tokens.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
KASUWAR ETF
A ranar Juma'a ne, Bitcoin ETFs suka fuskanci kwaranyar kuɗaɗe kusan $433M na net inflows, yayin da Ethereum ETFs suka samu kusan $144M
BABBAN CIGABA
Babban bankin Jamus Deutsche bank ya shirya ƙaddamar da digital-asset custody domin institutional da corporate clients a Turai.
SOLANA NETWORK
Kamfanin Solana sun sake matsawa zuwa 250ms slot time, wani mataki da ke nuna ci gaba da mayar da hankali kan sauri da scalability.
RUSSIA
Moscow Exchange ta shirya ƙaddamar da perpetual futures da suka danganci Bitcoin, Ethereum, Solana da XRP.
Wannan mako ya nuna mana cewa kasuwancin crypto bai tsaya iya labarin farashin tokens ba.
A gefe guda muna ganin:
Bitcoin → ETFs → Institutional Money
A ɗaya gefen kuma:
Blockchain → Tokenized Stocks → Traditional Finance
Wannan yana nuna cewa blockchain na ƙara wuce matsayin fasahar cryptocurrencies kawai, yana neman zama wani ɓangare na infrastructure na kasuwar kuɗi ta duniya.