A duniyar crypto, kalmar "HODL" (riΖ™e hannun jari na tsawon lokaci) ta zama tamkar wani babban sako na addini. Muna ganin hotuna da sakonni a kafafen sada zumunta suna kwadaitar da mu cewa: "Kada ka sayar, ko me zai faru!" Sai dai, akwai wata gaskiya mai daci da kwararrun yan kasuwa suka sani, wacce masu koyo ba sa son ji: HODLing kadai ba dabarar ritaya ba ce; dabarar fatan alheri ce kawai.

Idan burinka shi ne ka gina arziki mai dorewa wanda zai baka damar yin ritaya cikin jin dadi, kana bukatar wani abu da ya wuce kawai kallon lambobi suna tashi a kan manhajarka. Kana bukatar Dabarar Fita (Exit Strategy).


1. Tatsuniyar "Har Abada"

Dayawa daga cikin masu zuba jari suna fada wa kansu cewa za su rike kudin su har sai sun kai "Wata" (Moon). Amma matsalar ita ce, kasuwar crypto tana tafiya ne a mizanin hawa da sauka (cycles). Idan kudin ka ya ninka sau goma (10x), amma ba ka cire ko kwabo ba, sannan kasuwa ta fadi da kashi 90%, to a zahiri ba ka taba samun riba ba.

Gaskiyar Magana: Riba tana zama taka ne kawai idan ka sayar ka mayar da ita zuwa tsayayyen kudi (Stablecoins) ko kudin gida (Fiat). Lambobin dake kan fatar allo (Screen) mafarki ne kawai har sai ka fita.


2. Me Ya Sa Kake Bukatar Exit Strategy?

Ba tare da tsarin fita ba, kai ba mai zuba jari ba ne; kai dan caca ne mai jiran gaske. Ga dalilan da suka sa tsarin fita yake da mahimmanci:

Kiyaye Jari: Kasuwar Crypto tana da saurin canzawa. Abin da ya tashi yau, zai iya faduwa gobe.

Kwanciyar Hankali: Sanin lokacin da zaka fita yana rage maka fargaba (FOMO) da kuma damuwar ganin kasuwa tana ja.

Sake Zuba Jari: Idan ka cire riba lokacin da kasuwa take sama, zaka sami kudin da zaka sake sayen wasu kadarorin idan kasuwa ta fadi (Bear Market).


3. Salon Fita daga Kasuwa Cikin Kwarewa 

Kwararren dan kasuwa ba ya jiran sai lokacin da kasuwa ta rikice yake yanke shawara. Yana tsara komai tun kafin yayi investing. Ga matakan:


I. Cire Jari (Initial Investment)

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Da zaran kudin da ka zuba ya ninka (misali 2x), matakin farko shi ne cire jarinka na asali. Ta haka, ko da kudin ya fadi zuwa sifili, ba ka yi asarar komai ba. Kana wasa ne da "liquidity din kasuwa."


II. Tsarin "Tattalin Riba" (Laddering Out)

Kada ka sayar da dukkan kudin ka a lokaci daya. Raba fitar ka gida hudu ko biyar:

Siyar da 20% idan kudin ya tashi da kashi 50%.

Siyar da wani 20% idan ya kara tashi.

Ta haka, zaka ci gaba da samun riba yayin da kudin ke kara sama, kuma kana rage hadari.


III. Kayyade Burin Ka

Kafin ka shiga kasuwa, rubuta a takarda: "Zan fita idan kudin nan ya kai kaza." Idan ya kai, fita ba tare da waigawa ba. Kada ka bari kwaΙ—ayi ya sa ka ce "bari na kara jira kadan."


4. Shin HODLing Ya Mutu Ne?

A'a, HODLing yana da amfani idan kana maganar manyan kudade kamar Bitcoin ko Ethereum na tsawon shekaru 5 zuwa 10. Amma ko su ma, suna bukatar dabarar sarrafawa. Idan kana zuba jari a kanana kudaden nan na "Altcoins" ko "Meme coins," yin HODLing har abada zai iya zama hanyar da zata kai ka ga fatara.

Babban burin kowane mai zuba jari shi ne ya inganta rayuwarsa. Ba a gina gida da "Bitcoin" dake cikin wallet; ana gina gida ne da ribar da aka cire aka tabbatar da ita.

Idan kana son yin ritaya ta hanyar Crypto, daina kallon kasuwar a matsayin gidan ajiya, ka fara kallonta a matsayin hanyar samar da kudi (Cash flow). Ka tuna: Wanda ya san lokacin fita, shi ne wanda ya yi nasara a wasan crypto.

Shin kai wane irin tsari kake bi? Kana jira ne har sai "Moon," ko kuma kana da tsarin cire riba a hankali? Ka fada mana ra'ayinka a kwament