Wayarka ta san abubuwa game da kai fiye da mafi kusancin abokinka. Ta san inda kake kwana, inda kake aiki, hanyar da kake bi kullum da safe, lokacin da kake tashi daga barci, abin da kake searching da misalin karfe 2 na dare, wadanda ka fi kira, abubuwan da kake siya, harma da irin ra’ayin siyasarka. Kuma mafi yawan wannan bayanin ana rabawa ne kullum da companies da baka taba jin sunansu ba.

Kasuwancin Bayanai Da Ke Gudana a Cikin Wayarka

Kowane app dake cikin wayarka yana iya zama hanyar tattara bayanai. Lokacin da kayi installing app sannan ka danna β€œAllow” akan permissions dinsa location, contacts, microphone, camera, storage kana bawa wannan app din damar shiga muhimman bayanai na rayuwarka. Ana tattara wannan data, a hada shi, sannan a sayar da shi ga advertisers, data brokers, kuma wani lokaci har governments.

Advertising industry gaba daya yana aiki ne da behavioral data. Duk lokacin da kaga wani ads wato talla da yayi kama da conversation daka yi yanzu-yanzu, wajen da kaje, ko wani product da kayi tunani akai wannan ba coincidence ba ne. Wannan surveillance capitalism ne yana aiki yadda aka tsara shi.

Wane Irin Bayanai Ake Tattarawa?

Ana tracking location dinka kullum ta apps ko da baka amfani dasu. Tafiyar da kakeyi kullum tana iya bayyana gidanka, workplace dinka, wurin ibadarka, asibitocin da kake zuwa, da relationships dinka. An taba sayar da wannan data ga insurance companies, anyi amfani da shi a legal cases, har ma law enforcement sun taba samu ba tare da warrant ba.

Idan ka bada permission na microphone da camera, apps na iya amfani da su ta hanyoyin da suke da wahalar ganowa ko monitoring. Keyboard apps ma suna iya tattara duk abin da kake typing. Browser history kuma yana nuna abubuwa game da interests dinka, tsoranka, health concerns, da private searches dinka.

Yadda Zaka Rage Wannan Bibiyar

Ba zaka iya fita daga digital world gaba daya ba amma zaka iya rage yawan bayanan da ake samu game da kai sosai. Ka rika duba app permissions akai-akai kacire location, microphone, da contacts access daga dukkan wani app da baya bukatarsu da gaske. Yi amfani da browser kamar Brave wanda yake blocking trackers automatically. Yi amfani da VPN idan kana public networks. Ka sauya default search engine dinka zuwa DuckDuckGo. Kuma ka rika clearing ads tracking ID a settings din wayarka lokaci zuwa lokaci.

Ba za ka taba zama completely invisible ba. Amma zaka iya sa ya zama da wahala sosai ga companies su gina cikakken profile na rayuwarka ba tare da cikakken izininka ba.