Kowa mahaluki yana son yaga yayi hasashe kuma hasashen ya tabbata, musamman idan aka zo batun harkar crypto. Idan ka dade a cikin harkar nan, tabbas ka saba ganin charts cike da layuka daban-daban, da mafiya yawan wadanda ake girmamawa a matsayin "kwararru" da kuma yan kanzagi suke cewa: βBitcoin zai taba $100k nan da wata mai zuwa!β ko βWannan coin din zai ba da kudi sosai!β
Amma ka taba zama ka tambayi kanka: Me yasa kusan kashi 90% na wadannan hasashen baya zama gaskiya?
Bayan na dade ina bincike, ina tafka asara, kuma ina kallon yadda kasuwar nan ke wasan kura da YanBaiwa, a karshe na gano inda gizon yake saΖa. Wannan abin da na gano shi ya daidaita min dabarun kasuwancina yanzu. Ina so kai ma ka nutsu ka karanta wannan, domin zai iya zama silar tsirar capital Ιinka.
1. Makircin Whales
Babban kuskuren da yawancinmu muke yi shi ne zaton cewa kasuwar crypto tana tafiya ne kawai da tsarin lissafi ko abin da layukan chart suka nuna. Sam abin ba haka yake ba. Wannan kasuwar tana karkashin ikon mutane kalilan ne (Whales). Sau da dama manyan dillalan kasuwar nan suna aikata opposite na abunda zahiri ya nuna ne. A daidai lokacin da kake murnar cewa chart dinka ya nuna kasuwa za ta yi sama, sai kaga kuma wani abun ya faru daban, anan zaka fara tan-tamar ilimin ka, to ka sani da yawan lokuta ba laifinka bane. Anan ne whales suke Ζulla makircin su, suke hada baki wajen zubar da nasu kudin da gangan domin su tsoratar da masu karamin jari. Idan kowa ya firgita ya sayar da asara, sai su kuma su kwashe shi da arha. Irin wannan dabi'a yana daga cikin abunda na'ura ba zata iya detecting ba
2. Rudun "Technical Analysis" (Confirmation Bias)
Mafi akasarin masu yin bincike a crypto suna fada wa cikin tarkon ra'ayin son zuciya. Suna bude chart ne domin ganin son ransu:
Idan mutum yana son coin ya yi sama, sai ya ta laluben duk wata alama da za ta goyi bayan hakan.
Idan kuwa baya son coin din, sai ya ta nemo alamun faduwarsa.
Gaskiyar magana ita ce, chart ba madubin da zai haska maka tabbaci akan abunda zai faru bane; kawai dai yana nuna maka abin da ya riga ya faru ne a baya. Kasuwar crypto tana da saurin sauyawa fiye da yadda kake tunani.
3. Guje-Gujen Tsoro da Zumudi (FUD & FOMO)
Kasuwar crypto ba ta tafiya abisa reality; emotion yafi yawa a cikin ta. Hasashe mafi kyau zai iya rugujewa cikin kankanin lokaci idan labari guda daya ya fito daga gwamnati ko wani babban attajiri.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Zumudin Ballewa (FOMO): Yana sa mutane su ta sayen abu da tsada saboda tsoron kar a bar su a baya.
Tsoron Asara (FUD): Yana sa kyakkyawan hasashe ya tarwatse saboda kowa ya firgita yana tsoron kar kudinsa su kone, sai a shiga sayarwa a tare.
Ta Yaya Wannan Ya Sauya Min Salon Trading?
Tun lokacin da na gane cewa yawancin wadannan hasashe-hasashen surutu ne kawai na neman mabiya, sai na daina biye wa ra'ayin mutanen Tuwita (X) ko YouTube. Maimakon haka, na koma amfani da wadannan dabarun:
Bin Diddigin Coin (Fundamental Analysis): Maimakon kallon layukan chart kawai, yanzu ina bincikar me coin din zai yi, su wane ne jagororin project Ιin, da kuma yadda aka shirya tokenomics Ιinsa.
Tattalin Jari (Risk Management): Tunda na san babu hasashen da ke da tabbacin 100%, yanzu ba na taba zuba kudin da idan sun bace zan shiga damuwa. Sannan na tilastawa kaina amfani da Stop Loss.
Saye Kadan-Kadan (DCA): Maimakon na zauna jiran sai coin ya gama sauka kasa baki daya kafin na saya, yanzu ina sayen abina kadan-kadan duk bayan wani lokaci. Wannan yana takaita min fargaba da asara.
Idan kana son ka dore a duniyar crypto, ka daina sakan-kan cewa da hasashen yan kanzagi ko influencers. Duk wanda ya fito ya ba ka tabbacin inda kasuwa za ta dosa, to ko dai yana yaudarar kansa ne, ko kuma kai yake son ya nakasa.
Kasuwar crypto ba gidan caca ba ne; kasuwanci ne na ilimi, juriya, da natsuwa. Ka daina bin hasashen mutane barkatai, ka fara gina naka ilimin. Wannan ita ce kadai hanyar da zaka sauya akalar harkar ka daga asara zuwa riba mai dorewa.
Shin ka taba rashi saboda dogaro da hasashen wani? Fada mana experience dinka!