Indai kana bibiyar tsarin tattalin arziki da harkokin kuɗi na duniya zaka san yadda wasu tsirarun ƙasashe ke nuna iko da makomar arzikin mafiya yawan al'ummu.

Hakan ya basu ikon jefa kasashe masu rauni cikin fatara.

A yau, taswirar siyasar duniya tana fuskantar wani gagarumin sauyi. Zamanin da tsarin 'Unipolar'—petro dollar system da tsarin Swift ke jan ragamar tattalin arzikin kowa—yana daf da cika.

Muna rayuwa ne a duniyar 'Multipolar', inda manyan kasashe kamar Sin, Rasha, da gungun BRICS ke kokarin katsalandan domin ruguza ikon dalar Amurka. A tsakiyar wannan fagen daga, duniya ta shiga kishirwar neman mafita kwatsam sai sabuwar fasahar cryptocurrency ta bayyana. 

Crypto ba kawai wata hanya ce ta yin kasuwanci ko adana dukiya ga samari masu sha'awar fasaha ba; ta rikide ta koma wani "makamin monetary" na boye wanda ke sake tsara taswirar karfi tsakanin kasashen duniya.


1. Soke Takunkumi: Tawaye Ga Tsarin Swift

Kasashe irin su Rasha, Iran, da Venezuela sun dade suna fuskantar takunkumin tattalin arziki daga Amurka da kawawenta. Amfani da tsarin banki na gargajiya (Swift) yana ba Amurka damar rufe hanyoyin kudi na maƙiyanta da tafin hannu guda.

Bayan jimawa wannan tsarin na Swift ya ciwa sauran ƙasashe tuwo a kwarya, zuwan crypto ya basu mafita tare da yanci (Alternative Mechanism):

Ayyukan da ke bayan fage: Kasuwancin crypto baya ƙarƙashin ikon wata ƙasa ko tsirarun mutane (It's a decentralized system). Wannan dalilin yasa kasashe ke gudanar da kasuwancin mai, kayan aiki, da abinci ba tare da Amurka ta gani ko ta dakatar da shi ba.

Amfani da Stablecoins: Ba lallai ne sai Bitcoin ba, Kasashe da dama suna amfani da kudaden crypto da ke manne da farashin kadarori (Stablecoins) domin gudanar da kasuwancin kasa da kasa ba tare da shiga tsarin dalar Amurka na gargajiya ba.


2. CBDC: Arzikin Crypto na Ƙasashe 

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Baya ga kudaden digital na 'yan kasuwa, kasashen duniya sun fara kirkirar kudaden crypto na manyan bankunan (Central Bank Digital Currencies - CBDCs). Wannan ba komai bane illa martani mai karfi ga mulkin dalar Amurka.

Yuan na Digital (e-CNY): Kasar Sin tana gaban kowa a wannan fage. Ta hanyar e-CNY, Sin tana kokarin gina wani tsarin biyan kudi na kasa da kasa wanda zai gudanar da cinikayya tsakaninta da kasashen Asiya, Afirka, da Latin Amurka.

Rage Dogaro: Babban burin CBDC a duniyar multipolar shi ne rage dogaro da dalar Amurka a cinikayyar kasa da kasa (De-dollarization), ta yadda kowace shiya zata iya gudanar da harkokinta ta hanyar kudin digital na kanta.


3. Amfani da Ma'adanan Ƙasa Domin Cin Gajiyar Crypto

Harkar "Mining" ko hakar kudin crypto ta koma wani makami na siyasa. Kasashen da ke da wadataccen man fetur, iskar gas, ko makamashin ruwa suna amfani da wannan damar domin samar da dukiya ta hanyar Crypto.

Rasha da Yankin Asiya: Wadannan yankuna suna amfani da makamashinsu mai sauki domin aikin haƙar Bitcoin. Wannan yana ba su damar sauya makamashinsu zuwa kudin duniya nan take, ba tare da sun bi ta hanyar cinikayya ta gargajiya da ke cike da shamaki ba.

A duniyar multipolar, karfin kasa ba zai dogara kawai kan yawan sojojinta ko tarin zinaren da ke asusun bankinta ba; zai kuma dogara ne kan illar da za ta iya tafka wa abokan gabarta ta hanyar amfani da fasahar kuɗaɗen crypto. Mun shiga zamanin da kudi ba kawai abun musaya bane—kudi makami ne na yaƙi.

Idan ka fahimci tsohon tsarin gurguzun tattalin arziki da duniya ke kai da kuma salon da crypto yazo da shi, nan zaka san cewa crypto sai ya samu gindin zama a tsarin harkokin kuɗi ko ma ya kwace iko da shi. Wannan abun da muke gani yanzu somin taɓi ne 💪