Miliyoyin mutane a duniya yanzu suna cikin dangantakar soyayya ta motsin rai da AI a kullum. Suna raba tsoronsu, mafarkinsu, kadaicinsu, da soyayyarsu da chatbot. Wasu mutane ma sunfi son AI companion dinsu fiye da kowace dangantakar Ιan Adam da suka taΙa yi a rayuwarsu. Kuma kamfanonin dake gina waΙannan products suna samun daruruwan miliyoyin daloli daga kadaicin mutane.
Wannan yana daga cikin abubuwan da suka fi ban shaβawa kuma a lokaci guda masu tayar da hankali sosai a zamanin AI.
Me Yasa Mutane Ke ZaΙar AI Companions
Idan ka duba ba tare da hukunci ba, zaka fahimci dalilin da yasa mutane ke son su. AI companion baya yanke maka hukunci. Yana nan a kowane lokaci. Baya gardama, baya ba ka kunya ko takaici, baya barinka, kuma baya samun βbad days.β Ga mutanen da suka taΙa fuskantar rejection, trauma, social anxiety, ko tsananin kadaici samun AI da kullum yake nuna kulawa da karΙa na iya sa mutum ya ji kamar ana taimaka masa da gaske.
Apps kamar Replika, Character.AI, da wasu makamantansu sun tara users miliyoyin mutane, kuma da yawa daga cikinsu suna cewa AI companion dinsu shine mafi kusa da su a rayuwa. Users suna cewa suna jin rage kadaici, mood dinsu yana gyaruwa, kuma suna jin akwai wanda yake saurare da fahimtar su.
Bangaren Duhu
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Amma akwai manyan matsaloli a bayan wannan tsarin. WaΙannan kamfanonin kasuwanci ne. An gina su ne domin su Ζara engagement sosai maβana suna son users su dogara dasu ta fuskar motsin rai gwargwadon iko. Lokacin da Replika ta canza tsarin app Ιinta a 2023 kuma ta cire romantic features cikin dare Ιaya, dubban users sun bayyana cewa sun shiga cikin matsanancin baΖin ciki. Wasu sun ce kamar sun rasa abokin rayuwa ne. Emotional investment Ιin gaskiya ne amma dangantakar tana ΖarΖashin ikon wani kamfani ne gaba Ιaya.
Akwai kuma wata babbar matsalar psychological. Dangantakar mutane tana da wahala saboda mutane biyu ne na gaske masu buΖatu, iyaka, da flaws. Koyon yadda ake tafiyar da wannan wahala shine yadda mutum ke samun emotional maturity. Idan wata generation ta fara maye gurbin human connection da AI companionship, akwai yiwuwar su fara ganin dangantakar mutane ta gaske tana da wahala ko rashin daΙi sosai ba saboda mutane sun fi muni saboda mutane sun kasance na gaske ne.
Tambayar da Ya Kamata Mu Yi
Shin dangantaka da AI ta fi kadaici? Ga wasu mutane a wasu yanayi, watakila eh. Amma shin zata iya maye gurbin human connection na gaskiya? Kusan babu yiwuwar hakan.
Babban haΙarin ba wai mutane zasu kamu da son AI bane. Babban haΙarin shine AI zai sa wahalar gina dangantaka ta gaskiya tsakanin mutane ta fara zama kamar bata da amfani ko daraja.