Ka taɓa ganin wani trader ya ninka kuɗinsa cikin ƴan kwanaki, sai ka ji a ranka:

“Da ace ina bin wannan mutumin tun farko…”

Yau zamu yi magana akan Social Trading.

Social Trading hanya ce da ke baka damar kallon yadda wasu traders suke kasuwanci, nazarin dabarunsu, kuma a wasu platforms har ka iya kwafar trades ɗinsu kai tsaye.

Wai tsaya ma tukuna, ka taba baiwa kanka wannan amsar:

shin strategy nake kwafa ko kawai riba nake bi?


Ta yaya "social trading" yake aiki?

Misali, kaine kana bibiyar wani trader.

Sai ya buɗe trade na TON.

To daman kana bibiyar sa, kaima saika kunna copy trading.

Duk irin position daya buɗe kai tsaye kaima za'a shigar maka trade ɗin bisa tsarin daka saita.

Idan ya samu riba to kaima kana cikin alheri.

Idan kuma yayi asara haka kaima zaka rungumi ƙaddara.

Saboda haka, copy trading ba guarantee ba ne na riba.


Kada ka dinga ruɗuwa da PNLs

Ka ga trader ya samu:

+200%

Sai kayi tunanin cewa:

“wannan kwararre ne, shi zan bi.” Inji hausawa suka ce "daga nin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi?" 😁

A tsarin social trading kafin ka bibiyi wani trader ya kamata ka amsawa kanka waɗannan tambayoyin:

Nawa ne maximum drawdown ɗinsa?

Nawa ne leverage?

Trades nawa ne suka samar masa da wannan ribar?

Shin yana ɗaukar babban risk?

Shin strategy ɗinsa zai yi aiki idan market ya sauya?

Ba koda yaushe riba zata dinga rudar ka ba. 

Trader zai iya samun babbar riba saboda ya ɗauki babban risk—kuma irin wannan strategy ɗin na iya fuskantar babbar asara idan kasuwa ta juya.


Sirrin Social Trading ba copying ba ne

Mafi amfani shi ne koyo.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Ka lura da yadda trader yake aiki lokacin da:

Bitcoin yake tsalle-tsalle da kuma lokacin daya ke wuri ɗaya.

Open Interest ya tashi

Funding Rate ya yi tsanani

Volatility ya ƙaru

Trend ya juya

Kada ka kalli yadda yake cin riba kawai.

Kalli yadda yake managing risk.

Wannan shi ne inda ainihin ilimin trading yake.

Kafin ka bi trader, ka duba waɗannan abubuwa 5:

Return — Nawa ya samu?

Drawdown — Nawa ya taɓa rasawa?

Leverage — Yaya girman risk ɗinsa?

Track record — Tsawon wane lokaci yake samun wannan sakamakon?

Strategy — Shin ka fahimci abin da yake yi?

Indai ba ka fahimci strategy ɗinsa ba, zaifi kawai ka hakura, karka yarda PNLs ya ruɗe ka.

Kada ka manta cewa:

Social Trading ba ATM ba ne.

Ba ya kawar da risk.

Sannan baya baka tabbacin riba.

Kuma tradern da kake gani mai zamani a yau ba lallai ya kasance kasuwa tayi dashi kowane lokaci ba.

Misali yau ka ninka kuɗinka cikin sauri, kada tambayarka ta farko ta zama:

“Ta yaya zan sake ninka shi?”

Tambayi:

“Me ya sa na samu wannan ribar, kuma wane irin risk ne na ɗauka?” hakan zai sa ka koyi darasi tareda kwarewa.

Ta wacce fuska kake kallon social trading, ga ƴan koyo kaɗai ko harda gogaggun ƴan kasuwa.