A cikin 'yan watannin nan, hankalin kasuwar crypto ya koma kan wata doka da masana ke ganin za ta iya sauya makomar masana'antar crypto a duniya β€” CLARITY Act.

Wannan doka na daga cikin manyan kokarin da ake yi domin samar da cikakken tsarin dokoki ga kasuwar crypto, amma har yanzu ba ta kai matakin zama doka ba. Yanzu kuma ana kallon makonni biyun da ke tafe a matsayin lokaci mai matukar muhimmanci domin ganin ko za ta tsallake babban matakin majalisa ko kuma a sake samun tsaiko. 


Menene CLARITY Act Kuma Me Ya Sa Take Da Muhimmanci?

CLARITY Act (Digital Asset Market Clarity Act) wata doka ce da aka tsara domin warware babban rikicin da ya dade yana damun kamfanonin crypto a Amurka: waye zai kula da wane bangare na kasuwar crypto?

A yau akwai rashin cikakken bayani tsakanin hukumomi kamar:

SEC (Securities and Exchange Commission)

CFTC (Commodity Futures Trading Commission)

Tambayar da aka dade ana fama da ita ita ce: Shin wani token ko crypto asset ya kamata a dauke shi a matsayin security ko kuma digital commodity?

Wannan rashin tabbas ya sanya kamfanoni da masu kirkirar blockchain fuskantar matsaloli wajen sanin dokokin da za su bi.

Idan aka amince da CLARITY Act, ana sa ran za ta samar da karin haske kan yadda za a rarraba kadarorin crypto da kuma irin hukumar da za ta kula da su.


Me Ya Janyo Jan Ƙafa Akan Dokar?

Duk da cewa dokar ta samu ci gaba a majalisa, har yanzu akwai manyan batutuwa da suka hana a kammala ta. 


1. Rikicin Stablecoin Da Batun Riba

Daya daga cikin manyan matsalolin shi ne batun stablecoin.

Bangaren bankuna na ganin cewa idan kamfanonin crypto suka samu damar bai wa masu rike da stablecoin damar samun lada ko riba, zai iya sa mutane su karkatar da kudadensu daga bankuna zuwa crypto platforms.

A daya bangaren kuma, kamfanonin crypto suna ganin hana irin wannan damar zai rage gasa da kirkire-kirkire a masana'antar. 


2. Rikici Kan Ikon SEC Da CFTC

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Wani muhimmin batu shi ne yadda za a raba iko tsakanin hukumomin biyu.

Masu goyon bayan dokar suna son a kara wa CFTC iko wajen kula da wasu bangarorin crypto, yayin da wasu ke nuna damuwa cewa hakan zai iya rage ikon SEC wajen kare masu zuba jari. 


3. Lokacin Majalisa Na Kara Matsawa

Dalilin da ya sa ake cewa "mako biyu masu zuwa na da muhimmanci" shi ne saboda majalisar dokokin Amurka tana fuskantar karancin lokaci kafin hutun majalisa.

Idan dokar ba ta samu ci gaba ba a wannan lokacin, akwai yiwuwar a kara jinkiri zuwa wani lokaci mai tsawo. 


Makomar Kasuwar Crypto?

Masana kasuwa suna kallon CLARITY Act a matsayin wata dama da za ta iya bude kofar karin shiga daga manyan cibiyoyin kudi.


Idan aka amince da dokar:

Za a iya samun karin kwarin gwiwa daga manyan masu zuba jari.

Kamfanonin crypto za su samu karin haske kan dokokin aiki.

Amurka na iya kara karfafa matsayinta a fagen blockchain da digital assets.

Amma idan aka sake samun tsaiko, hakan na iya ci gaba da barin kasuwar cikin yanayin rashin tabbas. 


Menene Zai Faru?

A yanzu, CLARITY Act ba kawai wata doka ba ce; ga mutane da yawa a masana'antar crypto, tana wakiltar gwagwarmayar neman cikakken tsarin da zai tabbatar da makomar kasuwar digital assets.

Makonni biyun masu zuwa na iya zama wani muhimmin lokaci da zai nuna ko Amurka za ta dauki matakin samar da cikakkiyar dokar crypto, ko kuma za a sake komawa jiran wani lokaci.

A kasuwa kuwa, irin wadannan labarai na iya zama abin da ke kara tasiri kan yanayin tunanin masu zuba jari, musamman yayin da ake sa ran karin shiga daga manyan cibiyoyi.