Akwai wani yaki da yake faruwa yanzu amma yawancin mutane basu ma gane suna cikinsa ba.
Ba da bindiga ko makamai ake yin wannan yakin ba. Ana yinsa ne da kalmomi, hotuna, waka, da ideas. A gefe guda akwai artificial intelligence (AI), yana tafiya da gudun da babu wani mutum da zai iya kaiwa. A daya gefen kuma akwai mutane masu dauke da wani abu da AI ba zai taba iya kwaikwayonsa gaba daya ba.
Tambayar ita ce wa zai yi nasara? Kuma menene maβanar nasara a wannan yakin?
Bangaren AI: A Gaskiya Yana Riga Yin Nasara Ta Hanyoyi Da Dama
Mu fada gaskiya game da abin da AI zai iya yi. A cikin seconds kadan, zai iya rubuta cikakken article, kirkirar hoto mai kyau, hada waka, design logo, harma da yin video script. Abin da da zai dauki creatives kwanaki ko makonni yanzu ana iya gama shi kafin coffee dinka ya huce.
Ga businesses, wannan kamar mafarki ne. Karancin kudi. Saurin aiki. Unlimited scale. Tools kamar ChatGPT, Midjourney, da Sora ba wai suna zuwa ne su karbi creative jobs ba sun riga sun iso. Agencies suna rage maβaikata. Freelance markets suna raguwa. Stock photo platforms sun cika da AI-generated images.
Lambobi ba sa karya. AI ya fi sauri, ya fi arha, kuma yanzu ya isa ya yi aikin da mutane da yawa suke bukata.
Bangaren Dan Adam: Akwai Abubuwan Da AI Ba Zai Taba Ji Ba
A nan ne labarin yake kara ban shaβawa.
AI ba ya tashi da karfe 3 na dare da wani idea daya ki barinsa. Ba ya kirkira daga bakin ciki, daga yunwa, daga ganin kasarsa tana wahala, ko daga son wani har zuciya tana ciwo. Yana generating ne kawai amma baya ji.
Mafi girman art a tarihin dan Adam an haife shine daga wahala, farin ciki, tawaye, da rayuwar da aka rayu da gaske. Wakar Fela Kuti ba sauti kawai bane resistance ne. Labaran Chimamanda Ngozi Adichie ba kalmomi kawai ba ne identity ne. Wadannan abubuwa sun fito ne daga rayuwa ta gaskiya.
AI zai iya kwaikwayon hakan. Zai iya yin wani abu da yake kama da emotion. Amma a ciki babu komai. Babu experience. Babu gaskiya. Babu soul. Masu sauraro na gaske mutane na gaske suna iya gane bambancin. Wata kila ba nan take ba. Amma daga baya.
Asalin Yakin: Gaskiya a Duniya Mai Cike da Content
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Ga bangaren da mutane da yawa ba sa magana akai.
Yanzu internet ya cika da AI-generated content fiye da yadda aka taba gani. Millions na articles, hotuna, videos, da wakoki ana yin su cikin sauri ba tare da iyaka ba. Yawancinsu average ne. Da yawa kuma suna kama da aikin mutum a kallo na farko.
Kuma wannan shi ne matsalar.
Lokacin da komai yake kama da na gaskiya, babu abin da yake jin zama gaskiya kuma. Audiences yanzu suna samun wani sabon radar suna neman content da yake genuinely human. Raw. Imperfect. Honest. Creators da suke nasara yanzu ba su ne wadanda suke gogayya da AI wajen yawa ko gudu ba. Su ne wadanda suke kara nuna humanity dinsu muryarsu ta musamman, labarinsu, da perspective dinsu wanda babu algorithm da zai iya kwaikwayonsa.
Accent dinka. Asalinka. Failures dinka. Unguwarka. Wadannan ba weaknesses ba ne a zamanin AI. Su ne manyan creative assets dinka.
To Wa Zai Yi Nasara?
Duka β kuma babu daya.
AI zai mamaye bangaren volume. Zai yi content da ake bukatar ya zama mai sauri, mai sauki, da mai rahusa. Amma human creativity zai mallaki bangaren meaning labaran da suke taba mutane, art da yake defining generations, da muryoyin da suke sa wani ya ji ba shi kadai bane da tsakar dare.
Creators daza suyi nasara basu ne masu yaki da AI ba. Su ne masu amfani da AI a matsayin tool yayin da suke kara karfi a abubuwan da suke sa su zama uniquely human.
Yakin gaskiya ne. Amma mafi yawan mutane ba sa yaki da shi suna wuce shi.
Wannan article yana nuna raβayin marubucin game da yadda dangantaka tsakanin artificial intelligence da kirkirar dan Adam ke canzawa.