A kasuwar crypto, mutane da dama suna amfani da candlestick, RSI, MACD, EMA da sauran alamomin fasahar nazarin kasuwa (Technical Indicators). Amma akwai wata dabara da ƙwararrun 'yan kasuwa da manyan cibiyoyin kuɗi suke amfani da ita domin fahimtar abin da ke faruwa a kasuwa tun kafin ya bayyana sosai a kan chart. Ana kiran wannan dabara da Order Flow Analysis.
Ka taɓa yiwa kanka wannan tambayar, "Wa yake sayen Bitcoin yanzu? Su waye ke siyarda da Ethereum? Shin wannan tashin farashin gaske ne ko tarko ne?" to Order Flow Analysis na iya ba ka waɗannan amsoshin.
Menene Order Flow Analysis?
Order Flow Analysis hanya ce ta nazarin ainihin umarnin saye da sayarwa (Buy Orders da Sell Orders) da ke shiga kasuwa a lokaci guda.
Candlestick yana nuna maka abin da ya riga ya faru. Amma Order Flow yana ƙoƙarin nuna maka abin da yake faruwa a wannan lokacin, wato yana ƙoƙarin bayyana maka masu siya ne ke matsa lamba ko kuma masu sayarwa ne suke da rinjaye.
A taƙaice:
Candlestick = Sakamakon abin da ya faru.
Order Flow = Dalilin da ya sa abin ya faru.
Yaya Farashi Ke Motsi?
Farashi ba ya tashi saboda an sami koren candle kawai.
Farashi yana tashi ne idan masu siya suna ci gaba da siye cikin ƙarfi har ya zamto sun danne masu sayarwa da ke kasuwa. Haka kuma, farashi yana sauka idan masu sayarwa suka rinjayi masu siya.
Misali:
Idan mutane dubu suna son siyan Bitcoin a farashin yanzu, amma masu sayarwa sun yi kaɗan, farashin zai fara hawa.
Idan kuma manyan masu riƙe da Bitcoin (Whales) suka fara zubar da kadarorinsu da adadi mai yawa, farashin na iya fara sauka cikin sauri.
Su Waye Aggressive Buyers da Aggressive Sellers?
A Order Flow akwai nau'i biyu na mahalarta kasuwa.
1. Aggressive Buyers
Waɗannan su ne masu son siye nan take.
Ba sa jiran farashi ya sauko. Suna siye kai tsaye da farashin da ake sayarwa a lokacin.
Idan irin waɗannan suka yi yawa, yawanci farashi yana hawa.
2. Aggressive Sellers
Suma ba sa jiran wani ya zo ya saya.
Suna sayarwa nan take ko da hakan zai sa farashi ya sauka.
Idan suka rinjayi kasuwa, farashi zai fara faɗuwa.
Mene Ne Liquidity?
Liquidity na nufin yawan umarnin saye da sayarwa da ke jiran a cika.
Kasuwa mai liquidity mai yawa tana da wahalar motsawa.
Kasuwar da liquidity ɗinta ya yi ƙasa kuwa tana iya yin babban motsi cikin sauƙi saboda babu isassun masu rinjayar wani ɓangaren na yan kasuwar.
Saboda haka, ƙwararru suna lura da inda liquidity yake taruwa kafin su shiga kasuwa.
Menene Order Book?
Order Book wani jerin umarni ne da ke nuna:
Wa ke son saya.
Wa ke son sayarwa.
A wane farashi.
Da kuma adadin kuɗin da suke son amfani da shi.
Ta hanyar Order Book, ana iya hango wuraren da manyan kuɗi suke fakewa.
Sai dai ba duk abin da ke cikin Order Book ne yake tabbata ba. Wasu manyan orders ana saka su ne domin tsoratar da kasuwa, daga baya kuma a cire su kafin a cika su. Wannan ake kira Spoofing.
Menene Cumulative Volume Delta (CVD)?
CVD na auna bambanci tsakanin:
Girman sayen da aka aiwatar.
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
Girman sayarwar da aka aiwatar.
Idan CVD yana hawa:
→ Masu siya suna rinjaye.
Idan yana sauka:
→ Masu sayarwa suna rinjaye.
Amma akwai lokacin da farashi zai ci gaba da hawa yayin da CVD ke sauka. Wannan na iya nuna cewa wani babban ɗan kasuwa yana sayarwa cikin sirri yayin da ƙananan masu zuba jari ke ci gaba da saya. Wannan ana kiransa Divergence, kuma yana iya zama alamar yiwuwar sauyin alkiblar kasuwa.
Menene Absorption?
Wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da ƙwararru suka fi nema.
Misali:
Masu sayarwa suna ta zubar da Bitcoin adadi mai yawa yawa.
Amma duk da haka farashin bai sauka sosai ba.
Me hakan ke nufi?
Akwai wani babban mai siya "whale" da yake saye dukkanin wannan coins ɗin ba tare da ya bari farashi ya faɗi ba.
Wannan shi ake kira Absorption.
Sau da yawa, idan aka ga wannan yanayi, ana iya samun babban tashin farashi daga baya.
Menene Footprint Chart?
Footprint Chart yana buɗe sirrin da ke cikin kowace candle.
Maimakon kawai ka ga Green Candle ko Red Candle, Footprint yana nuna:
Yawan saye.
Yawan sayarwa.
Wane farashi aka fi ciniki.
Wane ɓangare ne ya fi ƙarfi.
Saboda haka ƙwararren trader yana iya fahimtar abin da ya faru a cikin candle ɗin da idon chart na al'ada ba zai nuna ba.
Shin Order Flow Ya Fi Technical Indicators?
A'a.
Babban kuskuren masu koyon trading shi ne tunanin Order Flow shi kaɗai zai sa su zama ƙwararru.
Gaskiyar magana ita ce:
Order Flow kayan aiki ne na ƙara fahimta, ba sihiri ba.
Ana samun sakamako mafi kyau idan aka haɗa shi da:
Market Structure
Support da Resistance
EMA
Volume
Open Interest
Funding Rate
Masana suna amfani da Order Flow domin tabbatar da ra'ayin da suka samu daga sauran nazarin kasuwa, ba domin maye gurbinsu gaba ɗaya ba.
Abun Lura
Kasuwar crypto ba ta motsawa saboda zane-zanen chart kaɗai.
A bayan kowane candle akwai dubban cinikayya da ke gudana tsakanin masu siya da masu sayarwa. Fahimtar wannan mu'amala na iya taimaka wa mai ciniki ya gane ko motsin farashi yana da ƙarfi, ko kuwa tarko ne da zai iya karewa cikin sauri.
Order Flow Analysis ba ya ba da tabbacin abin da zai faru nan gaba. Amma yana ba ka damar ganin abin da ke gudana a kasuwa fiye da abin da candlestick kaɗai zai nuna. Wannan ne ya sa manyan traders da cibiyoyin kuɗi ke amfani da shi wajen inganta lokacin shiga da fita daga trade.
Idan kana son inganta matakin fahimtarka a kasuwar crypto, kada ka tsaya ga kallon launin candlestick kawai. Ka fara fahimtar abin da ke faruwa a bayan fage—inda kuɗi ke shiga, inda ake tara kadarori, inda ake rarrabawa, da kuma wanda ke rinjayar kasuwa a kowane lokaci.
A ƙarshe, trader mai nasara ba wai wanda ya fi yawan indicators ba ne, illa wanda ya fi fahimtar halayen kasuwa da yadda masu siya da masu sayarwa ke mu'amala. Order Flow Analysis na daga cikin muhimman hanyoyin da ke taimakawa wajen ganin hoton kasuwa a sarari.