Wannan ita ce tambayar da economists, technologists, gwamnatoci, da ma’aikata na yau da kullum suke ta kokarin fahimta a lokaci guda  kuma gaskiyar magana ita ce babu wanda yake da cikakkiyar amsa mai gamsarwa. Abin da muke da shi yanzu shi ne data, historical precedent, da kuma cikakken hoto na yanda abubuwa suke tafiya.

Girman Abin Da Ke Zuwa

Wani rahoto na Goldman Sachs a 2023 ya kiyasta cewa AI zai iya automate tasks da har yanzu ma'aikata miliyan 300 na full-time suke yi a duniya. World Economic Forum kuma yayi hasashen cewa duk da AI zai ƙirƙiri sabbin ayyuka miliyoyi, zai kuma kawar da wasu ayyuka masu yawa a short zuwa medium term  wanda hakan zai haifar da wani lokaci mai wahala sosai ga ma’aikatan dake cikin industries da abin zai shafa.

Ayyukan da suke cikin haɗari ba low-skill roles kawai ba ne. Radiologists, lawyers, accountants, financial analysts, journalists, da junior software engineers duk suna fuskantar automation na muhimman tasks dinsu. AI ba muscle kawai yake maye gurbi ba yana maye gurbin cognitive labor ma.

Tarihi Ya Nuna: Sabbin Ayyuka Za Su Bayyana

Ra’ayin masu optimism wanda historical precedent ke goyon baya shine technological revolutions kullum suna lalata tsoffin ayyuka sannan su ƙirƙiri sababbi. Industrial revolution ya rage agricultural labor sosai amma ya ƙirƙiri factory work. Computer revolution ya kawar da typing pools amma ya ƙirƙiri gaba ɗayan software industry. Ana ganin AI ma zai bi irin wannan hanya.

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Sabbin roles ma sun riga sun fara bayyana: AI trainers, prompt engineers, AI ethics officers, machine learning operations specialists, da human-AI collaboration managers duk waɗannan positions ne da kusan babu su shekaru biyar da suka wuce.

Matsalar Tana Cikin Transition

Wannan optimism ɗin na tarihi yana da wani muhimmin caveat. Transition tsakanin old economy da new economy yana da matuƙar wahala ga mutanen da suka makale a tsakiya. Wani data entry clerk mai shekaru 45 ba zai iya sauya kansa kawai ya zama AI engineer cikin sauƙi ba. Ma’aikatan da suka fi wahala sune waɗanda suke da narrow skills a highly automatable roles kuma basu da resources na retraining.

Gwamnatoci, educators, da businesses duk suna da rawar da zasu taka wajen kula da wannan transition. Amma individuals baza su jira systemic solutions ba. Abu mafi muhimmanci da duk wani mai aiki zai iya investing a kai yanzu shi ne skills masu wahalar automate creativity, leadership, emotional intelligence, complex judgment, da technical expertise a emerging fields.