Idan ka tambayi kusan kowane Ιan kasuwar crypto ko mai zuba jari game da halin da walat dinsa ke ciki a yau, amsar da zai ba ka tsakanin murmushin takaici da numfashi mai nauyi ita ce: "Wai ashe haka kasuwar nan take?"
A shafukan sada zumunta kamar X da Telegram, kowa na maganar zama miloyniya cikin sauri. Amma a zahiri, mutane da dama suna gani ne kawai yadda jarin da suka wahalta wajen nemansa yake narkewa kowace rana.
Shin ka taba tambayar kanka: Ainihin me yasa kake fatara duk da cewa kana cikin kasuwar da ke ΖyanΖyashe miloyniyas kowace rana?
Wannan ba labarin rashin nasara bane kadai; rahoto ne da zai fito ma da ainihin "tushen matsalar" a kasuwar crypto, da kuma hanyar da zaka gyara ta.
1. Ζaukin Gaggawa FOMO (Fear of Missing Out)
Babban kuskuren da ke jefa Ζ³anBaiwa a halin ΖaΖa na kayi shine siyan (token) a lokacin da ya riga ya tashi kololuwa.
Yadda abin yake faruwa: Za ka ji ana maganar wani Meme coin ko wani sabon project watakil ana kaurarashi da yin "100x" a shafukan labarai da cakwalkwalin Ζ΄an crypto. Lokacin da ka yanke shawarar siya, ainihin wadanda suka fara siya sun gama da romon, suna jiran sababbin shiga (irin ka) domin su sayar muku (dump).
Gaskiyar Lamari: Idan har ka ji labarin wani token ya karaΙe kowace irin tsangaya, to ka sani already ka riga ka makara don samun babbar riba, a takaice wannan ba lokacin siya bane. Shi yasa 'yan kasuwa kan ce: "Buy the rumor, sell the news." (Siyi labari tun yana jita-jita, ka sayar lokacin da ya zama labari).
2. Wofantar Da Tsarin Tattalin Jari (Risk Management)
Mafi yawan mutane ba sa shiga crypto a matsayin Masa'uba na Kasuwanci (Investor); suna shiga ne a matsayin Masa'uba na Caca (Gambler).
"Zuba dukiyarka duka a wani token guda daya tamkar sa kwai ne duka a kwando gudaβidan kwandon ya fadi, komai ya lalace."
Mafi yawan wadanda crypto ke yiwa dukan sakwara:
Suna amfani da Futures Trading da tareda (Leverage) mai yawa (misali 50x ko 100x).
Ba sa amfani da Stop Loss (tsarin takaita asara).
Suna zuba kudin da ba za su iya jure rashinsu baβhar da kudin rance ko na makaranta!
3. "Kada Ka Yarda Da Kowa, Yi Bincikenka" (DYOR - Do Your Own Research)
Enjoying this analysis?
Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.
A duniyar crypto, akwai abin da ake kira Influencer Culture. Mutane da yawa suna bin shawarar wadansu 'masana' a kafar X ko YouTube ido rufe ba tareda nasu binciken ba.
Gaskiyar ita ce, da yawa daga cikin wadannan masu mabiya da dama ana biyan su kudi ne domin su zakula ko tallata wani project galibi na bogi (Pump and Dump Scheme). Su suna karbar kudadensu na tallace-tallace, yayin da mabiyan ke shiga tsaka mai wuya da asara idan project din ya rushe (Rug Pull).
4. YaΖi da Mafi Girman Makiyinka: Hankalinka (Trading Psychology)
Kasuwar crypto ba ta motsawa kawai saboda girman fasahar Blockchain; tana motsawa ne ta hanyar shauki TSORO (Fear) da KWADAYI (Greed).
Tashi Kasuwa - KwaΙayin Saya
Faduwar Kasuwa - KwaΙayin Sayarwa
Konewar Jari - "Hanyar Shiga Fatara Cikin Sauki"
Irin wannan yanayi na siyan abu a tsada saboda kwadayi, sannan a sayar dashi a araha saboda tsoron kada ya kara faduwa, shine hanya mafi sauri ta mayar da Dangote Kamaye a crypto.
Me Ya Kamata Kayi?
Idan kana tsakiyar wannan yanayi na fatara a matsayinka na Ιan kasuwar crypto, har yanzu akwai kofa. Gasu wasu 'yan shawarwari domin canza takun tafiyarka:
1. Raba Zuba Jarinka (Diversification): Ka tabbata kaso mai yawa na jarinka yana cikin manyan kudaden da ke da tsari mai karfi kamar Bitcoin (BTC), Ethereum (ETH) da ire-iren su kafin ka kafara tunanin saka dukiyar ka cikin (Altcoins ko Memecoins).
2. Yi Amfani da Tsarin DCA (Dollar-Cost Averaging): Maimakon ka zuba kudaden ka duka a lokaci guda, rika siyan kadan-kadan a kai-a kai ba tare da damuwa da me kasuwa ke yi a ranar ba.
3. Koyi Ilimin Taswira (Technical & Fundamental Analysis): Karku zama masu gaggawa. Binciki ingancin team dake bayan project da kakeson saka kuΙi, tsarin usecase dinsa da utility, da kuma yadda jadawalin faduwa da tashinsa yake (tokenomics).
4. Sarrafa Kwadayi: Koda yaushe ka zama mai fitar da ribarka (Take Profit). Riba a cikin kasuwa (Unrealized Profit) ba takamaimiyar ribarka ce ba har sai ka maida ita Stablecoin (kamar USDT) ko kudinka na gida.
Kasuwar Crypto ba waje bane na samun kudi na dare daya ba tare da wahala ba. Waje ne mai cike da damarmaki masu yawa, amma damammakin na bukatar Haquri, Ilimi, da Juriya.
Idan a yau ka tsinci kanka a matsayin "Broke Crypto Investor", kar ka sare a nan. Ware wani kaso na jarinka domin neman ingantaccen ilimin kasuwa.