A fagen gine-gine, mutane kan yaba wa kyawun fenti, tsayin bene, ko kyan gilasan waje. Amma gine-gine ba sa tsayuwa saboda fenti; suna tsayuwa ne saboda ginshikin da ke binne a karkashin kasa wanda idanu ba sa gani.

A dandalin hada-hadar kudi da Crypto, wannan boyayyen ginshikin shi ne Liquidity (Wato yalwar kudi masu yawo ko saukin musanya kadarori). Idan babu shi, komai kyawun fasahar blockchain ko tsarin wani token, komai zai iya rushewa cikin kankanin lokaci.


1. Menene "Liquidity"?

A saukake, liquidity yana nufin ikon siyar da wata kadara (kamar Bitcoin, Ethereum, ko Real World Assets - RWA) cikin sauri ba tare da farashinta ya fadi da gagarumin gibi ba.

Misali kaine kanada gida na Naira miliyan shida, kuma kana bukatar kudi yanzu-yanzu. Sayar da gidan zai iya daukar satuka ko watanni musamman idan a wajen gari yake; wannan yana nufin gida kadara ce mai karancin liquidity (illiquid). Amma idan kana da Bitcoin na miliyan shida, zaka iya mayar da shi tsabar kudi (USDT/NAIRA) cikin yan mintuna; wannan shi ne koli na yalwar liquidity.

Saboda haka, liquidity shi ne iskar da kasuwa ke shaka. Idan aka samu yalwarsa, farashin kaya yana tashi cikin kwanciyar hankali. Idan yayi Ζ™aranci kuma, kasuwa na fuskantar abun da ake kira Flash Crash (faduwar farashi farat daya).


2. "Global Liquidity" da Kasuwar Crypto 

Idan kana bin diddigin kasuwar crypto, watakila kana tunanin cewa labaran ci gaban fasaha ko tweets na manyan mutane ne ke sa Bitcoin tashi. Eh, akwai wannan ma. Amma babban abunda yafi muhimmanci shine: Kudaden da babban bankin Amurka (Federal Reserve) da sauran manyan bankunan duniya ke saki shi ne ke da tasiri Ζ™warai wajen sarrafa kasuwar crypto 

Lokacin da bankuna suka rage kudin ruwa (interest rates), mutane da manyan hukumomi (Institutional Investors) suna yin rige-rigen karΙ“ar lamuni (bashi). Wadannan kudaden da suke karba bawai suna barin su a banki bane; sukan nemi inda za su hayayyafa cikin sauri. Wuri na farko da suke fadawa shi ne kasuwanni masu hadari amma masu riba mai tsokaβ€”wato Crypto da Tech Stocks.

Abunda Aka Saba Gani: Idan ruwan kudi na duniya (Global Liquidity) ya karu, farashin crypto yana hau-hawa da girma. Idan aka samu matsi bakin lalita daga bankuna, kasuwa na shiga yanayi na rashin tabbas (Bear Market).


3. Order Books Da Kuma Hatsarin "Slippage"

A Ι“angaren Ζ™ananun masu zuba hannun jari kuma da (Retail Traders), liquidity shi ne gatan su. A cikin tsarin ciniki (Order Books), idan akwai masu siye da siyarwa da yawa a kowane matakin farashi, kasuwar zata zama tana da "yalwa" (Deep Liquidity).

Enjoying this analysis?

Subscribe to get more deep dives directly in your inbox.

Sponsored Alpha

Idan kuma kasuwa ba ta da liquidity, akwai shiga barazana guda biyu:

Slippage (Gibin Farashi): Lokacin da kake Ζ™oΖ™arin "Buy" ko "Sell" da kuΙ—i mai tsoka, maimakon ka siya a farashin da kake gani, sai tsarin ya siyar maka a farashi fiye da kima saboda babu matches na kusa.

Manipulations (Juya Kasuwa): Tsirarun Ζ΄an kasuwa masu kudi (Whales) suna iya shigowa su kitsa makirci akan farashin coin da suke so saboda babu wata hada-hada ta azo-a-gani da zata rinjaye su.


4. Tokenization Na RWA Da Dark Pools

A halin yanzu da muke ciki, ana samun sauyi na musamman inda ake kawo tsofaffin kadarorin duniya kamar zinari, gidaje, da hannun jarin kamfanoni zuwa kan blockchain (Real World Assets - RWA). Me yasa ake yin haka? Domin a sanya musu Liquidity! Blockchain yana bawa kowa damar siyan ko da kaso daya ne cikin dubu na wata babbar kadara a ko ina a fadin duniya kuma ya siyar dashi tak.

Haka zalika, babban tsarin nan na Dark Pools da cibiyoyin hada-hadar kudade na zamani (decentralized dark pools) suna kara yaΙ—uwa. Wadannan wasu boyayyun wuraren kasuwanci ne inda manyan hukumomi zasu iya siyan daruruwan miliyoyin daloli na crypto ba tare da fuskarsu ko order din su ta bayyana a bainar jama'a ba, wanda hakan ke hana farashin tashi ko faduwa da gaggawa kafin su gama cinikinsu. Suna samar da sirri da kuma kariya ga yadda ake gudanar da hada-hada a kasuwar.

A matsayinka na mai zuba jari, kada ka kalli farashin coin kawai; koyaushe ka duba Trading Volume da Liquidity dinsa.

A fagen gine-gine, idan gini ba shi da kyawun asali na tubali, ko ba dade ko ba jima zai rushe. Haka ma a crypto: kowane coin ko token (Project) da ba shi da sahihin tsari na samar da liquidity, to tamkar gidan rami ne da aka gina shi a kan yashi. Liquidity shi ne boyayyen ginshikin da ke rike da dukkan daular crypto.

Zuba ido a kan yadda hada-hadar kudaden duniya ke tafiya shine sirrin za

ma kwararren mai hango makomar kasuwa!